CHAPTER 19

3K 209 80
                                    


LUBA'S POV

Wayar caja ta janyo ta fara tsulani aiko take na soma kuka ina burbuwa itako fadi take da izinin wa kukaje gidan aliyu harda kwana? Ke Dan iskanci da rashin sanin ya kamata kika fada musu daki kai tsaye kaman gidan ubanki, su nana ta cafko ta hada dasu tayi mana tas tas sannan sannan ta kora mu daki..... tana zaune ta ganni da jaka niki niki dama yanzu nafi dadewa a gidanta amma tunda nasha assauda nace babu dawowa.

Ganin ina saukowa da jaka niki niki yasa tace ina zuwa? Cikin bacin rai na abinda aliyu da aunty maryam suka min nace gidan ubana  inda zan fada ko ina ba tare da anga laifina ba. Baki ta saka Dan ban taba Mata rashin kunya ba saide taurin kai..... take taji wani iri a zuciyar ta Dan tunda na fada mata magana kuma na tafi toh naji haushi... kila ina da gaskiya da ta tambayeni....

Kiran sunana ta soma nikam kara sauri nayi Dan banaso na dawo gidan. Direct gidan mu na nufa ko napep din banhau ba jakata na daura aka... ummi na gani na da kaya da hawaye ta taso tana salati... luba yar umminta ya akayi? Rungume ta nayi ina kuka wiwi ta zaunar dani a kujera dama tasan abinda ke sani farin ciki... ABINCI amm da ta bani ko kalla banyi ba har juice ta bani na dauke kai toh tasan maganar ta girmama.

Gaba daya ta rikice tace luba hankalina yana tashi me akayi miki ? Fada Mata komai nayi amma na tsallake fada ta da ladidi tayi ajiyar zuciya tace kema de luba harda laifinki ya zaki fada musu daki ? Nace toh ummi sanda nayi knocking sosai fa amma ba'ayi magana ba sai na dauka ko basanan ne....  race toh nikam bance miki akwai abinda Mata da miji keyi Wanda ba'ason kowa yaji ko ya gani ba? Nace kin fada kince za'a mutu tace yauwa toh nan gaba indai suna daki a tare karki sake shiga kinji daga kai nayi badan na hakura ba.

Kwakulo tasono nayi zankai baki ta make hannu na tace kede kin shiga uku katuwa dake na dauka an dena halin ta canja zani ashe da saura ? Kai aliyu yanada aiki... turo baki nayi nace ni kar ki kara min maganar sa. Tace au yanzu zancen aliyun ma bakya so?

Tashi nayi na tafi dakina tace aiko yarinya kina ruwa tunda shi zaki aura kaji min shirmen banza. Dauko wayata nayi na fara kiransa har sau uku bai dauka ba aiko na cika na batse Dan dama so Nike na dan masa rashin kunya na basa haushi.

ALIYU'S POV

Bayan na Kira aunty maryam na sanar da ita abinda luba tayi min... da ina Dan tunanin in yarda in aureta amma yanzu ta sa na soma sanja tunani. Yarinya ahaka in ka ganta kamar sallah ashe ko alwala babu? son kowa kin Wanda ya rasa yar budurwa amma da ka kwankwashi hankalinta sai kaji shiru kamar mushriki yaci shirwa yasha ruwa?

Yar amarya ta ladidi ne ta fito an karya dankwalin nan gwanin ban sha'awa flask din abinci ta dauko mana ta kawo tana budewa mukaga an  sande mu yan iskan yaran nan sun cinye. Murmushi tayi tace laa  kilan su luba najin yunwa yasa suka ci bara na daura mana wani.

Kawai binta nayi da kallo ina fadin Allah na gode ma ka bani Mata kyakkyawa ga hankali kuma yar karama abinta.

Abincin ta kawo mukaci muka shiga hira anan ne

LADIDI'S POV

Lokacin da ya Kira aunty maryam zai bata rahoto dadi naji a raina Dan dama nice na rigashi da dabara nace masa ya fada Mata abinda luba tayi kar abar yarinya ta tashi ba gwaba kuma AI in ta Sami tarbiyya mu keda riba tunda mu zamu zauna da ita aiko ya dauka shine fa ya fada Mata.

Wanka nayi na sheka ado kamin na dauko mana abinci tun a kitchen din nasan sun taba danko naji nauyin ya canja hakan yasa na bude na gani murmushi nayi Dan ko gyara kaina zanyi.
Budewa nayi kamr bansan me ya faru ba nace laa kila su luba ne kemin yunwa sukaci bari na daura mana wani abin. Irin kallon da yake bina dashi nasan na burgeshi ne. Wata kwarkwasa nasa har kitchen inajin haushi danko abincin ya biya raina guntun na sude  dan yunwa nakeji saboda kwakulata da mai gidana yayi.

Bread da kwai nayi mana sannan nakai masa na basa abaki daga nan muka shiga hira cikin so da kauna.

LUBA'S POV

Kuka nasha abina na huce haushi sannan na kwanta bacci ya daukeni ina cikin bacci naji waya na ringing...nana ce dauka nayi tana kuka tana rokon sister Dan Allah kar kice bazaki dawo ba kar abinda akayi miki yasa kiyi zuciya na rikeni da Allah ki dawo kinji sis Dina? Nace naji zanyi tunani na kashe wayan batare da na saurare me zata sake cewa ba.
Message na gani daga uncle aliyu wai

"yan Mata me yasa ake  rangaba min Kira ko bata show din bai isa bane sai kuma an hada da kira?😉 " tsaki naja na rafka masa Kira aiko yana dauka na fashe da kuka nace abinda kayi ka kyauta dukda cewa ina da laifi Wanda ba da gangan nayi ba... bai dace ka fadawa aunty maryam har kasa tayi min birtsi birtsi da bulala ba, na dauka inada darajar da nafi karfin wulakanci a Wawrinka ashe abin ba haka bane... ok wani abin nayi ma kamata yayi ka kirani ka zaunar dani bawai kayi min cin mutunci ba toh bari kaji indan nace kai nakeso yasa kake min haka toh kaje gaka ga ladidi.... ni dama akwai wani mai gadi kuma yanaso kawai nice naki yarda amma bari kaji ni luba daya daya ka rubuta ka ajiye NA FASA AURENKA!... in ga uban da zai tursasa ni.

AFWAN AFWAN NAYI LATTI YAU AYI MANAGE DA WANNAN GOBE DA WURI ZAKU JINI INSHA ALLAH.

KAI TSAYA ASHE FA AN BALLO WANI JAGWAL KO? TOH LUBA DE TACE TA FASA KO SHIN ABIN ZAI YIWA ALIYU DADI? KOKO SABANIN HAKA NE?

TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO

Miss untichlobanty 💕

23rd June,2020.

YARINYAR CE TAYI MIN FYADEWhere stories live. Discover now