Alkali yace ra'ayinki bai karbu ba tunda lauyan bai gama nuna hotunan ba. Samir ya tafi hoto na gaba ina suna zaune ga damin goro da kudi damin naira dari dari. Yace wannan hotan mahaifiyar yarinyar ce ta dauka ga can maryam yayar mahaifiyar a gefe su kuma maza lokacin ana shirin karbar auren kenan.

Wani hoto na uku ya sake nuna wa yace ga kuma hotansu su dukansu harda cousins dinta nana da mama bayan an daura auren. Hindatu tace karfa ku manta ance ranan haihuwar ta ne Dan haka akwai yuwuwar ayi family picture Samir yace menene hadin ranan haihuwa da goro da kalin cingam tare da sisin gwal?
Shiru tayi Samir yace ya mai girma mai Shari'a batun FYADE kuma bai aikata FYADE ba domin kuwa shi kansa ba a haiyacin sa yake ba ansa masa kwaya a bin sha Wanda bamusan waye yayi masa hakan ba Ga result nan na jininsa a ranan da abin ya faru ta nuna tabbas akwai kwaya a jininsa kuma a iya sanin duniya,police station har ma da asubiti ba'a taba kamashi da shaye shaye ba.

Da wannan nake rokan kotun nan mai albarka da ta wanke mr aliyu daga zargin da ake masa ta kuma sa bangaren da suka bata masa suna su biyashi tara sannan abar masa matar sa. Alkali ne yace lauyan me kara ko kinada abin cewa ? Tace zanso gabatar da shaida na mai gadin gidan tare da mai chemist da kuma mahaifin yarinyar.

Alkali yace kotu ta baki dama fitowa sukayi tace bawan Allah zanso sanin ko kai waye yace nine mai gadin gidan malam Ali tace ko zaka iya fada mana abinda ka sani game da shi da kuma matana dake zaune tare da shi? Abinda ya fada ma yan sanda haka ya maimata musu babu ragi babu Kari domin shine iya gaskiyar abinda ya sani kuma ya fahimta. Tace mun gode sannan ta kalli mai chemist tace ko zamu iya sanin ko kai waye? Yace nine malam ubaliyo mai chemist.  Tace shin zaka iya fada mana abinda malam Ali yazo siya a yammacin 3 ga wadannan ?

Kallon aliyu tayi ya tuna da labarin da yake ji a unguwar cewa matar aliyu ta biyu tana da cikin yan uku dukda baisan sanda aliyu yayi wani aure ba. Aliyu ko yanajin news dadi yasa yi dinga kiran makotansu yana fada musu anata sanya alkairi. A ransa yace yanzu idan ba karesa ba haka yaransa zasu tashi a wahale kuma malam Ali mutumin kirki ne yamin halacci    ya bani shago kyauta tare da bani jari sannan baya siyan magani wajen kowa saini Dan ya taimaka min.

Nide akwai kamshin gaskiya a maganarta bazan juya masa baya ba. Yace tabbas yazo wajena ya siya magani kuma maganin da ya siya kamar wacce ta Saba siya ce ta rage masa sha'awa ga receipt nan na ko wani wata kamar bill haka yake biya. Saide ranan yace na basa mai karfi domin ji yake sha'awarsa ya tsananta a ranan Wanda baisan dalilin hakan ba.

Hindatu a ranta tace amma anyi Dan iskan mutumi duk wahalar da nasha lokacin da na ga result din cewa akwai kwaya a jininsa ne na Nemo shagon da yake siyan magani. Kuma ya tabbatar min ya siyenta shine yanzu zai canja zance?

Tace malam ubaliyo kwantar da hankalinka ka fadi gaskiya babu abinda za'ayi maka yace gaskiya ta kenan. Cewa tayi mun gode a kufule ta wuce kan daddy tace shin da gaske ne ka aurar da harka ma malam Ali? Yace Sam bansan da wannan zancen ba.

Haka daddy ya zauna ya karyata Samir ya rushe musu komai hindatu ko murmushi take tace toh hotunan da ya nuna fa? Yace wannan hotuna munyi amma Gordon da nake gani bansan inda ya samesu ba Dan haka technology yayi aiki dashi ya hada hotan.

Tace mun gode malam adamu da wannan nake rokan kotu mai albarka ta gaggauta hukunta malam Ali aka zina da cin amanar matar sa da yayi. Alkali yace lauyan wadda ake kara kanada abin cewa? Tace no my lord babu.
Alkali yace bayan sauraran hujjoji da shaida daga bangare guda biyu kotu ta yanke hukunci ko da Aires ko ba aure tsakanin aliyu da lubabatu toh dole su rabu duba da jawabin mahaifinta wannan case mun rufeshi amma kotu har zuwa yanzu bazata daure malam Ali da laifin FYADE ba domin har yanzu ba wata hujja da aka bayar cewa da gangan yayi Dan haka malam Ali na Rabaka da lubabatu saide idan iyayenta ne suka baka aurenta a baiyane, sannan zaka bada taran 250k ma ladidi na hakwara 5 da ka zubar Mata. Na daga case na biyu zuwa 15 ga wata na gaba kamin ya buga guduma luba ta Mike ta ruga da gudu ta rike guduman yan sanda ne sukayi caraf zasu rikota ta zille ta sauko kasa nace kaji taron sakarkaru.

Cilli tayi da gudumar ta tsuguna Alan guiwowinta tace mai Shari'a karka rabamu Dan Allah wallahi bazan iya rayuwa babu shi ba ya kakeso nayi da jarirai alokacin har ana shirin zuba Mata ankwa saboda tayi disrespecting din doka... alkali yace ku dakata me kike fada? Tace ciki ne dani alkali wallahi har cikin yan uku ma kaga hotan yanzu tun kamin a haifesa nakeson ka raba iyayensu.

Ban aikata abinda na aikata Dan na Rena doka ba na aikata ne saboda yarana kuma na tabbata kana da yara kuma zaka iya yin komai akansu. Ka duba mana ya mai Shari'a. Yace babu abinda zan iya yi domin kun kasa bada sheda kwakkwara saide ki roki iyayenki da su bashi auren ki abinda kika aikata a yanzu kuma an yafe miki amma ki kiyaye na gaba. Zai buga gudumarsa a karo na ba ladidi tace KU DAKATA MAI SHARI'A INADA MAGANA.

GENG! GENG!! GENG !!! ANZO WAJEN GA LADIDI NAN DAI KO ME ZATA CE OHO?

SHIN KUNGA LAIFIN LUBA AKAN ABINDA TAYI?

ANYA ALIYU ZAI TSIRA KUWA?

TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO

Miss untichlobanty 💕

13th July,2020.

YARINYAR CE TAYI MIN FYADEWhere stories live. Discover now