CHAPTER 34

2.2K 249 26
                                    

inspector yayi yace munzo ne muyi arresting dinka ne amma idan nayi haka ban ma hallacci ba zan haka zan cika maka takardan beli amma fa saide kayi hakuri an Riga an shigar dakai kotu Dan haka dole ne kaje saide zanyi kokari na nema maka lawyer.... murmushi aliyu yayi yace karka damu hakan ma na gode.

Fita sukayi aliyu ya mara musu baya yana sake yi ma inspector godiya dafa kafadarsa yayi yace AI kayi min hallacci dukda cewa abinda nayi yanzu bai dace ba na hada aiki da personal life Dina toh amma kuma ka ceci citizens of Nigeria dan haka da wannan zan daga maka kafa amma yanzu dole muje dakai ka bamu statement dinka.

Luba kuwa lungu ta samu ta takura ta rike hotan yayanta Sato ma babu Wanda zai tayata farin ciki Allah ya azurtata da samun da.... tunowa da cewa zasu iya kawo Mata wargi yasa ta sidade jiki ta shige dakinta ta ranbatsa mukulli tayi kwanciyarta anan bacci ya dauketa bayan ta shanye ice cream.

.......

Bokan ladidi ne zaune ya rantaba uban tagumi yana karanta wasikar jaki bayan ya saurari bayanin da aljanin da zai gyara uhm uhm din aliyu saboda ya samu sun shirya. Yace yanzu aljani matuidi babu yadda za'ayi ka gyara aikin? Matuidi yace na fada maka tunda ya shiga matsala ya kama addu'a gam ya rike ni ko unguwar da yake naje sai gabana ya fadi.

Boka yace toh jeka zan tattauna da aljani zatsiwit...boka yace zatsiwit nina mini halin da ake ciki da batun yaron nan Ali dan ban taba yin aikin da nake nadama sai tasa. Nuna masa yayi boka yace zatsiwit........

Ni ban gane sauran me yace masa ba saboda wani yaren su da ya soma amma de kamin mu wuce gaba ina da magana.

Akwai wasu mutane, normally kawai zasuyi su sallah da sauransu amma da sun shiga matsala toh lokacin za'a tuna Allah sune azumi, zikirin nan kamar bakinsu zai fita. Sallar nafilan nan ma ayi ta yi har sai kai yayi ciwo daga sauki yazo kwana daya, biyu sai a watsar toh de ku sani manzon Allah yace:

"Ku tuna da Allah a yayinda kuke cikin jin dadi shi kuma zai tuna daku a yayin da kuka shiga tsanani" tirmidhi be ya rawaito.

Allah ya sake cewa:

“ Therefore remember Me (by praying, glorifying), I will remember you, and be grateful to Me (for My countless Favors on you) and never be ungrateful to Me.” Quran (2:152)
"Ku tuna, ni zan tuna ku. Sannan ku kasance masu godiya a gareni kuma kar ku kasance masu butulci " Quran (2:152)

Toh a gaskiyan lamari ba sai na tsawaita ba nasan dayawa daga cikin ku sai duniya ta dau zafi ta muku atishawar tsiya in akayi rashin sa'a ma ta muku bugun shinkafar year shafi'u tukun ake koma ga Allah toh gaskiya mu gyara yan uwa wannan Sam bai dace ba.

Wasu haka bazaka taba sanin sun iya sa hijab ba sai da RAMADAN a dauki sallama za'a tafi masallati bararam ana tafe ana surutu wai zuwa masallatin ma kuma sai a mayar dashi gasa. Har ana duba hijab din wace yafi kyau da tsada... can you imagine wata fa bama sallah da jin wa'azi taje ba taje ne de kawai ta bawa idonta abinci ko ta hadu da samari toh kuwa asara ta sameki kinji kunya.

Abin haushin matan auren ma ba'a tsira ba wata ana sallah tana duba kasar ganinki wai taga ko holland ko wax? Me tauraro ok babu idan ma akwai na wace wata ce kaji min kayan takaici.

Haka kuma mazannan zakuyi ta bin yan Mata da mujiya ana duba yar lukuta da siririya toh gaskiya ya kamata mu Mike musan me muke yi musan ya kamata.. you didn't come to this world to waste your time and return to you lord with nothing to show.

NAJI ANA JITA JITA WAI ANA SAYAR MA MUTANE DA LITTAFI WHATSOEVER NIDE NAWA BA NA KUDI BANE IN WANI YAR KARBI KUDINKI TOH KI KARBI ABINKI YAR UWA SHIYASA NA BADA HANYOYIN DA ZAKI SAMENI A SAMA DOMIN MU GAISA DA DAI SAURANSU.

Ban garen ladidi kuwa sai washe gari ta farka inda ta koma yar tatata luku kawai take ita batasan me tayi ba yanzu duk wannan wulakancin Dan ta zubar da cikin shege ne ake yi Mata shi? A dake ka a hanaka kuka.

Aliyu kama direct wajen Samir ya tafi bayan ya tashi a police station da sallamar sa ya shiga ya samu shida mamansa suns parlour gaisawa sukayi kamin aliyu yaja shi suka fice.

Samir yace aliyu ya akayi ne? Ajiyar zuciya ya sauke yace mutumi na batun nan ce de ta aure na da luba nikam dama na sanar dakai na tabbata bazaka manta ba. Samir yace dude na yarda dakai yanzu ya ake ciki? Aliyu yace banda wannan batun kasan na fada ma shirmen da nayi akan matar nan ladidi toh shine fa yanzu zamu shiga kotu tunda kaga kai lafiya ne me zai hana ka kare ni.

Samir yace aiko baka fada ba indai naji batun case din dole na nemeka yanzu de menene charges din ? Aliyos yace toh da fari de wai domestic violence and rape ne yanzu kuma an kara min da adultery.

Samir yace innalillah wa inna ilaihi raji'un gaskiya aboki na bazan maka karya ba kana cikin matsala dukda cewa kotun naga ba Shari'a court bane amma ko a haka fa dauri shekara 2 ne fa laifin zina kawai. Toh kuma ga rape.

Wanda in section 358 of the criminal code, it states that “any person who commits the offence of rape is liable to imprisonment for life, with or without canning”
Wato duk wani mutumi Wanda ya aikata FYADE toh hukuncinsa daurin rai da rai ne ko da tara ko babu.

Aliyu yace AI inada gaskiya ta kuma cire Mata da hakori da nayi ni jinina ta kashe min nasan Allah yana tare dani... innallaha ma'ana.

Zuwa yanzu kowa ya fice daga sabar su aliyu Dan gani suke bata lokaci suke kuma babu me basu haushi kamar luba saide har yau sunki bari aliyu ya tafi da ita. Sati na kewayo wa aja nufi kotu.

Ana zaune har alkali ya shigo suka Mike bayan ya zauna suka zauna nana tana shafa bayan luba alamun rarrashi. Dan sanda ne ya rako aliyos har inda zai tsaya bayan anyi introducing case.

Alkali yace ina lauyan me kara? Lauyan ladidi ne ta mike Wanda yan human right ne suka tsaya Mata tace sunana hindatu Bashir nice mai wakiltar wadda take kara. Alkali yace ina lauyan Wanda ake kara? Samir ya Mike cikin harshen turanci yace ya mai girma mai Shari'a sunana Samir Abduljalal nine Wanda nake kare Wanda ake kara.

Alkali yace zamu fara da fyaden da kayiwa matarka, fyade na cin mutunci.
Hindatu tace ya mai Shari'a zanso nayi wa malam aliyu tambaya.

Mai Shari'a yace go on. Tace malam aliyu ko zan iya sanin inda kake sati biyu kamin faduwar abun? yace ina asubiti ne lokacin. Tace shin ko mene dalilin da yasa aka kamaka a asibiti? Yace heart attack ne ya kamani tace ko me yasa heart attack ya kamaka? Samir ne yace objection my lord lauyen me kara tana kokarin tunowa client Dina abinda ya janyo ciwon zuciya ta kama Wanda zai iya tashi masa.

Alkali yace korafi bai karbi ba gaban luba ne ya tsinke har a cikin cikinta taji ace an fara case da gwalesu innalillah. Lauya tace malam Ali kai Mike sauraro yace saboda a ranan ne aka rabani da matata uwar yaya na. Tace toh AI duniya bata sanka da wata Mata ba face ladidi kuma a iya sanin duniya babu Wanda ya rabaku. Aliyu yace MATATA LUBABATU ADAM NAKE NUFI!

TOH A SUBURBUDO COMMENT IDAN BA HAKA BA BAZAKU JINI BA SAI JIBI.

TOH GASHINAN DAI AN SHIGA KOTU KO YA ZATA KAYA?

BOKA DE YA SAMU TALABIJIN YANA HANGO YADDA RAYUWAR SU ALIYU KE TAFIYA... SHIN KUNA TUNANIN ME NAKE TUNANI?

BARI NAGA DA YAN WATTPAD DA FACEBOOK DA WHATSAPP KO SU WAYE SUKA FI SO NA? BARI MU GANI

A BIYO NI DAN JIN YADDA ZA'A KAYA. TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO

Miss untichlobanty 💕

12th July,2020.

Yauwa kuma a mance da VOTE nayi fushi abi na.

YARINYAR CE TAYI MIN FYADEWhere stories live. Discover now