Fita sukayi nikam naci gaba da ciye ciye da hannu bibbiyu ina jinjina kai kamar wata kadangaruwa.

ALIYU'S POV

Tunda na fadi plan din kowa ya yarda amma toh yadda zan zaunar da luba bayan an kaita shine matsalar. Sanda su aunty maryam suka fito daga side dinta kuma side Dina na da.

Sukace toh aliyu mu mun gama namu ga luba de an kawo ma ka rike amana kaji ko? Sannan ka bita a hankali don Allah. Aunty maryam tace kai hajjo kiji da wani zance yarinyar ko tsarki ma batada shi. Hajjo tace AI zata samu... ratan dai kaji ni ko?

Sosa kai nayi a raina nace ni dama babu abinda zanyi Mata kawai so nake na nuna Mata batafi karfinmu ba yayinda a zahiri nace insha Allah.

Suna fita na kafta Mata sakata na wuce dakin ladidi abina Dan nasan yanzu haka luban tayi bacci Dan kayan ciye ciyen nan ba haka kawai nabar su kazar ba. Kuma kan ta tashi sai an jima.

A gida kuwa duk an watse su ABBA ana fatan zaman ya dore Dan sun tsorata da luba zuwa yanzu saide addu'a.
Washe gari da safe ba duba ta aiko ta bingire hannunta dama dama da abinci. Karba nayi na ajiye na cire alewar dake bakinta na gyara Mata kwanciya ina ja Mata kumatu kamin na fita abina.

LUBA'S POV

Ina tashi naji kaina na ciwo sosai nayi mika har zan sauko ba tuna banyi addu'a ba nayi kamin na sauka sai lokacin na fara tunanin ina kyauta ta kuma me yasa na kwana anan ? Fita nayi nagan ni a parlour komai fari kalle kalle nayi kamin na bude wata kofa kitchen ne turo baki nayi Dan kofar fita nake nema.

Sunan aunty maryam na fara Kira ina bude wata kofa ban daki ne sai wani daki daya.... kofar da nake tunanin na fita ne toh shi a kulle Kira nayi amma kowa wayar sa a kashe. Na uncle aliyu na Kira Dan zuwa yanzu na fara tunanin ko saida ni akayi.

Dagawa yayi yana fadin wow I am honored yau her royal highness luba da kanta ke kirana. Toh sarauniya me zan miki? Cikin Muryan kuka nace uncle aliyu an sace ni kazo ka taimake ni yace yimin bayanin me ya faru...

Nace kawai ni da su aunty maryam munzo wani gida na fara ciye ciye su kuma suka tafi dauko min kyauta ta daga nan basu dawo ba kuma nima ban sake sanin komai ba sai yanzu na tashi.

Kode bigesu akayi aka dauresu? Yace karki damu your savior is here kawai sai aka bude kofar.

ALIYU'S POV

Ina zaune muna cin abinci ni da ladidi wacce itama batasan luba tana gidannan ba nace yau abinci Dan kadan zata sakamin sauran zanci anjima tace toh. Wayata ne tayi haske dama tana silent Dan haka nace kawo sauran ki gani bari in adana a dakina. Ba karba sannan na nufi bangare na Wanda ladidi bata shiga in ba Dan tayi shara ba saboda a bangaren ta nake zama.

Bata zargi komai ba ta bani na wuce ina fadin yanzu zan dawo yayinda ta soma cin abincin ta. Dauka nayi cikin tsokana nace wow ! I am honored yau her royal highness luba da kanta ke kirana. Toh sarauniya me zan miki? Cikin Muryan kuka tace uncle aliyu an sace ni kazo ka taimake ni nace yimin bayanin me ya faru...

Cikin muryar tsoro da alamu kuka take yanzu kam tace kawai ni da su aunty maryam munzo wani gida na fara ciye ciye su kuma suka tafi dauko min kyauta ta daga nan basu dawo ba kuma nima ban sake sanin komai ba sai yanzu na tashi.

Kode bigesu aka yi aka daure su? Dariya ke cina da alamu yarinyar nan ta kalli cartoon dayawa shiyasa bata da wayo cikin murmushi nace karki damu your savior is here ina mai bude kofar side din juyowa tayi da sauri ta saki wayar ta rungume ni kamar rayuwata na jiki na sai karkarwa take ta hada gumi dukda ko akwai AC a kunne.

Abinda na soma ji tattare da ita a karo na farko tun rana yarinya naji saboda ban sake raba ta da jikina ba tun yarintar ta iyaka mu gaisa da hannu ko na shafa kanta ko kuma naja Mata kumatu. Tsimi tsimi nayi ina zare ido kamar mara gaskiya amma sai na shafa kanta nima muryata na rawa nace luba karki damu babu Wanda ya saceki a cikin gida na kike kuma ko ladidi bata sani ba....

So ake a aura miki wannan me gadin shine ni da aunty maryam da hajjo muka hada baki cewa a Sato ki a boyeki a gidana kinga sai a dauka kin bata sai an fasa sai ki koma gida Dan haka banda aunty maryam ko ummi kar Kira sai kin fada min sannan ki dinga saka wayar ki a plane mood sai zakiyi chatting ne kawai zaki cire sannan ki rufe su last seen dinki.

Banda posting status banda fita waje idan ba haka ba kuwa a gano inda kike karki bari ladidi ma ta ganki. Tace kutma. Sai kace Kurkuku gaskiya bazai sabu ba! Tureni zatayi ta wuce nace kin shirya auren me gadi kenan? Matansa uku fa kuma kinsan masu gadin nan suna shaye shaye kuma duk Dan shaye shaye yana amalala.

Da sauri ta dawo tace zan zauna kuma zanbi doka nace yauwa kinga ni banason daukan risk ma zan sayo miki sabon waya nasa miki sim sai ki dinga social media dinki amma banda WhatsApp wancan wayar sai ki kashe ta in zakiyi waya da aunty maryam kiyi ta wayata Gyada kai tayi tana zazzare ido Dan taji batun fitsarin kwance.

Abincin na mika Mata nace zan dinga kawo miki abinci na sati daya kamin na gyara kitchen din ki samu ki fara girka naki na karashe ina janyota jikina. Toh tace kamin ta kara da na gode sannan zame har ta juya zata koma daki ta juyo ta Dana bakin nan kamar kosai za'ayi rashin mutunci kenan tace toh amma nima sharadi na daya kar kana tabani. Dariya kawai nayi na fita kar ladidi taji shiru.

Abinda yasa kuwa na rufe Mata waya saboda in tana chatting bazata ji ta gaji ba amma idan taji ta gaji toh ni kadai ne abokin hirarta toh zamu shaku yadda ko taji gaskiyan bazata gudu ba.... fatana daya Allah yasa wannan plan yaci.

TOH MUN DAI GA PLAN DIN ALIYU AMMA TAMBAYAR ANAN SHINE SHIN WANNAN ABU ZAI BILLE KUWA? YA SHARADIN LUBA , ALIYU ZAI KIYAYE KO ZAI SABA?

TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO

Miss untichlobanty 💕

24th June,2020.

YARINYAR CE TAYI MIN FYADEWhere stories live. Discover now