Uncle Aliyu aka kira shima yace bai ganni ba nan cikinsu ya duri ruwa aka fara cigiya ta a unguwa amma babu alamata.

Abinda ya faru kuwa shine tun da magrib ina waya da nana nake fada Mata nifa idan aka ki yarda guduwa zanyi tace yayi mutuniyata toh amma in kin gudu ina zakije? Nace nima ban sani ba. Maama tace toh me zai hana tazo nan ba tare da sanin kowa ba sai musa ta a BQ ko ya kukace mu dinga bata su abinci daga nan.

Nace toh amma masu gadi zasu fada ai nana tace karki damu zan rufe musu baki aiko tunda daddyna bai yadda ba karfe uku nayi sneaking dama already nana ta sanar da masu gadi zuwa na Dan haka suka budemin kofa.
Inaji da safe anata cigiya na dan video call muke da  su nana ina ganin komai.

Zama aka Kira da azahar na yadda za'a soma nemana Allah sarki har sun bani tausayi amma nasha alwashin idan ba auren aka fasa ba bazan fito ba. Gidajen radio da talabijin duk an watsa amma shiru babu labarina. Ladidi ko abin ya Mata dadi amma sai ta nuna tafi kowa damuwa. Harkuka tayi anata bata hakuri ummi ma tasha kuka tace ma daddy na asanar cewa an fasa auren kila na dawo.

Yace Sam ba'ayi haka ba idan naji ba haza San dawo gida shirme nake yunwa ma kadai ya isheni ummi tace toh AI garin neman kudin abinci in na fada wani hali fa gashi dama ba hankali gareni ba? Yace a bari nan da sati sai ayi sanarwan.

Su nana kullum tsakar dare suke kawomin ziyara musha hira kuma Allah cikin ikonsa babu wadda ya taba tsammanin ina gidan kamar wasa har sati daya yayi Dan haka yau abbana suka shirya suka tafi gidan yasa labarai... basusha wahala ba aka basu Dama domin yin magana.

Daddy na yace assalamu alaikum! Nine mahaifin yarinyar nan lubabatu da akayi sanarwa satin daya gaba ta cewa ta bata... luba diyar albarka idan kina jin mu yanzu haka ki dawo gida mun janye batunnan mun fasa. Aliyu ma ya bada nasa jawabin cewa ya fasa Niko tabe baki nayi nace sai bayan kwana biyu zan fito.

Haka sukayi ta zuba ido suna neman ranta inda zan billo amm shiru. Washe gari ma haka abin ya fara daga musu hankali sosai toh kode na mutu ne? Da daddare ne su nana suka hadani da Allah cewa na fito kullum sai ummi tayi kuka kawai sai na yanke shawarar zan fito gobe.

Washe gari ummi na rashi da safe ta leka daki na yadda ta Saba dukda bata tsammaci gani na ba ta ganni nayi wannan wawar kwanciyan nawa a da kullum make ni take amma yau cikin jin dadi ta rungume ni tana sumbatar goshina. Allah sarki diyata ta dawo lubabatu na uwata in kika shiga umminki tayi kewarki.

Kureta nayi da ido Dan ta bani tausayi har ta rame nace ummi na kiyi hakuri na saki damuwa amma babu yadda na iya ne sanda nace muku banason auren kuka dage sai anyi. Tace karki damu an fasa kiyi karatun ki kinji? Toh nace mika sha kuka.

Aka fada wa su aunty maryam an sameni aiko shikenan ban karajin anyi batun auren ba har lokacin WAEC dinmu yayi. A dakin jarabawa ne naji wasu dalibai na hira ta fari tace nifa wallahi ko da aunty kaltume ta rasu naso ni aka aura wa mijin ta gaskiya aliyun nan ya hadu. Ta biyu ne tace nikam kullum sai kin mana zancen aliyunnan amma ko saninshi bamuyi ba ta fari tace aliyu mukhtar fa!  Ta uku tace wanne shi kenan? Ta biyu tace me me Ablimuk plaza ? Ta farin tace shidai.

Ta biyun tace wow gaskiya nima naji ance gayen ya hadu ta ukun tace nikam ban sanshi ba. Ta biyun tace dama ance miki shugaban kasa ne da kowa sai ya sanshi? Mtsww ta ukun tace kanku akeji toh dukda ban sanshi ba toh yamin kuma zan Nemo bayani akansa. Ta farkon tace sannu Sara me bakar tak*shi  Sato dan ubanki ya fi namu kudi shine zaki wani ce ya miki zaki kwata? Ta biyun tace ku da kuke hauka bakusan matansa 2 ba ? AI daddy naji yana cewa matansa biyu amma dayan na sirri ne. Kinsan daddy na aminin yayansa ne.

Ta farkon tace ince wancan lubar ance ta sansa? Yayar mamanta ke auren yayansa? Ta biyun tace kwarai nima naji hakan toh mu tambayeta mana. Ta uku tace yarinyar dake da shegen fi'ili ga reni cab a dawo lafiya. Wajena suka zo suka ce sannunki luba.... take na musu nace sannunku. Sukace wai da gaske kinsan Aliyu mukhtar? Nace na sanshi amma munyi fada ban kulashi Dan haka inma sako me daku bazan iya kaiwa ba.

Sukace haba yar uwa toh ko numbarshi kya bamu AI ko hannu na mika alamun abani littafi suka miko min hannunsu Niko na rubuta na cire numbar karshe nace su nemi wannan da kansu. Daidai lokacin aka kawo papers Dan haka babu halin magana.

ALIYU'S POV

Ya ABBA ne ya tisa ni a gaba yace toh aliyu ga luba fa kaga yadda ta kafe yanzu ya kake tunanin za'ayi?  Kaga de har gida ta bari akan kar ta aureka an tambayeta inda ta zauna ma tace bazata fada ba kar a kuma cewa za'ayi auren ta rasa wajen buya wadda ke nuna in aka sake takura Mata zata gudu kuma dai kasan matsayinta.

Ajiyan zuciya na sauke nace AI ya ABBA kuma kunyi gaggawa bai dace sanda takai shekara goma tace ta yarda ayi auren kuka daura a lokacin ba da kun bari ko zuwa yanzu kunga ko ta fasa ba matsala. Uncle ABBA yace toh ka saketa mana tunda bata ma San da auren ba! Nace kai gaskiya bazan iya ba ni bansan yadda zanyi da ita in tazo gidan sai in sanar da ita.  Ya ABBA yace toh kadai yi a hankali kasan kamar me aljanu kar mu sake nemanta mu rasa!

😳TOH FA NAJI WANI LABARI KO KUNNE NA NE?💃🏻💃🏻 TOH BARI NA TAKA RAWA ASHE LUBAR MU MATAR ALIYUN CE MA TOH YANZU DE YA ZA AYI TA YARDA TAJE GIDAN?

KU BIYONI A NEXT CHAPTER DANJIN YADDA ZA'A KAI LUBA A DABARA, SHI IN ANKAITA ZATA ZAUNA KO ZATA ARCE?

IN KUNYI COMMENTS DAYAWA IN BAKU UPDATE IN NAJI SHIRU KUWA TOH SHIKENAN NIMA ZAKUJI SHIRU😉

TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO

Miss untichlobanty 💕

23rd June,2020.

YARINYAR CE TAYI MIN FYADEWhere stories live. Discover now