Part 5

156 9 1
                                    

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

MUTUWAR AURE

LAURATU ABUBAKAR

HELLO
THIS IS A NOVEL BY ME (Lauratu Abubakar)to entertain and educate you during this quarantine period.It's a fiction,yes it's a fictional story written in HAUSA.
In this novel I'll be teaching you romantic tricks which you should try and also cooking,who doesn't love a delicious meal?nobody,again gyaran jiki you should look takeaway and amm also love tricks in general.kun sanni babu wasa so you should follow up,comment and vote don't forget to follow me on Wattpad @lauratuabubakar
Please don't pirate me,my book and I.
It's a criminal offense!
Create your own work
Also,there will be a RABBANA (Prayer)at the end of every page (Please memorize each everyday)even if you do please read them as I'm posting.
May Allah reward us all.Ameen

Page 5
A daddafe suka shiga cikin gida a wannan ranar Zainabu ta faranta wa Ibro rai haka zalika shima.
Tun da Abu taga farin cikin da Ibrahim ya shiga sai ta dage wajen ganin ta na burge shi ta kowane hanya.
Bayan watanni biyar
A wannan watan ne Allah ya sauk'i Zainabu lafiya,ta haifi d'an ta namiji santalele.Ranar suna yaci sunan Yusuf.
Wata tsohuwa Ibrahim ya nemo wadda zata yi wa Abu wankan jego.
Kasancewar yasan bata son Gyallesu shiyasa ya za'bi ta zubar wanka a nan.
Haka rayuwa take tafiya cikin kwanciyar hankali.
Yusuf ya tashi da gata da kowane yaro yake tashi da shi dai-dai gwargwado.
Exclusive breast feeding Abu tayi for six months sannan aka fara bawa Yusuf ruwa da sauran baby foods,yaro ya cicciko Masha Allah.
A watanni shidan farkon nan Baba tayi wa Abu wankan jego na watanni biyu daga nan taci gaba da kanta,bata zubar da wanka ba har sai bayan watanni shidan farko.
A watanni shidan nan ta gyara kan ta sosai duk wata alak'a tsakanin ta da mijin ta tana saukewa hakan bai hanata darjewa da gyara ba.

Bayan shekaru uku
A wannan shekarun Abu ta haifi d'an ta na biyu Muhammad.
Shekarar Muhammad d'aya da watanni shi kuma a lokacin  Yusuf shekarun sa hud'u babu 'yan watanni ya girma Masha Allah kuma yayi baki sosai.
Da dad'i da rashin sa haka Abu da Ibrahim suka juri zama tsawon shekarun nan.
A wannan shekaran ne suka saka Yusuf a wata School tsallaken su.
Tun bakwai da rabi basu tashi sai k'arfebiyar na yamma ,had'e yake da islamiyya.

Abu ce a kitchen tana feraye dankali bayan ta idar da sallar asubahi .
Ibrahim ya shigo,a hankali ya rungume ta ta baya suka saki murmushi.
Zagayowa yayi ya kar'bi wuk'ar a hannunta "huta gimbiya sarautar mata wannan aiki na ne duk lokacin da nake gida".
Murmushi Abu tayi tana k'are wa farin cikin zuciyar ta kallo.
Kallon ta yayi "kin tsare ni da ido me kike so ayi miki?".
Murmushi tayi "potato omelette zanyi sai kunun gyad'a da black tea".
"Okay so yanzu ga kujera zauna (ya fada yana janyo mata kitchen stool) dafata yayi ya zaunar da ita ,gimbiya ta kiyi ta bani order ina bi".
Murmushi Abu tayi nan ta fara bawa Ibrahim order yana bi.
Kallon sa tayi
"Ka d'ebo dankali cup biyu ka feraye"
'Debowa yayi ya fara da wasa da dariya Abu ke koya masa.
"Yanzu da ka gama feraye dankalin ka yanka shi 'kanana sai kasa a ruwa ka ajiye".
Yadda ta fada hakan yayi
"To yanzu ka d'ebi gyada ludayi uku(nik'ak'k'iyar gyad'a) ka dama da ruwa sai ka dora kan wuta saboda a gama girkin tare da kunun sai na rik'a juya maka".
Hakan kuwa akayi ya d'ora mata gyadar ta rage zafin wutar.
Shinkafa fara data jik'a tun jiya da daddare ta dauko ta wanke ta fara blending,sai data yi juice sosai sannan ka kashe ta juye a cup.
"Yanzu ka kunna wuta ka d'ora frying pan da mai sai ka raba dankalin into 4 sai ka dauki kashi d'aya ka soya"
Yana d'orawa Abu ta d'auko k'wai da attaruhu,albasa da spices ta kad'a ta ajiye masa a gefe.
A nutse taci gaba da juya kunun gyad'ar yana tafarfasowa.
Wannan juice din nik'ak'k'iyar shinkafar ta tace ta juye cikin gyad'ar taci gaba da juya wa.
"Darling dan Allah yi sauri ka jik'a min tsamiya na manta".
Nan ta masa kwatance ya d'auko ya jik'a
"Darling ka duba can drawer da wata yellow rubber ka bude kayan k'amshi ne kazo ka k'ara min anan".
Zuwa yayi ya zuba da bakin rubber "Haba D idan yayi d'aci fa?" Ta fad'a tana tura baki.
Murmushi yayi "sai mu shanye".
Da sauri ta juya taga dankalin ya soyu.
Ka rik'a juya min kunun nan sai inyi guda d'aya ka gani.
Colander na k'arfe ta d'auko ta tsane man a ciki ya rage dankalin nan ta shirya sukayi kyau.
Had'in k'wan nan ta kad'a tazo ta zuba har sai da dankalin suka shige.
Minti biyu ya fara k'amshi nan tayi amfani da flat kitchen spoons biyu ta juya.
Kallon sa tayi
"Nayi na farko yadda nayi haka zaka ci gaba"
Switching suka yi ya dawo ya d'ora mai ita kuma ta koma kan kunu.
Tsamiya ta zuba ta juya sannan ta sauk'e.
A flask biyu ta juye babba da k'arami sannan ta kalli Ibro "Idan mun gama ka kira Musa a waya please Fatima nason kunun nan da tasan dashi da tuni ta aiko".
Murmushi Ibro yayi "Ita dai Fatima bansan had'in ta da kunun gyad'ar ki ba,kwanaki fa Musa yake cemin wallahi idan ta kwana biyu bakiyi ba har zazza'bi take".
Murmushi Abu tayi "Kamar yadda kaima kake jin zazza'bin ba".
Dariya suka yi Ibro naci gaba da aikin sa Abu na tattare kwanukan da suka 'bata.
Bayan minti goma abinci ya kammala.
Yanka omelette din tayi irin yankan da ake ma pizza ta nad'e cikin paper sannan ta sa a flask.
Suna dariya suka fito
'Dakin su Muhammad ta je ta tashe su ta fara yi wa Yusuf wanka da brush sannan ta tashi Muhammad ma ta masa.
Shafe jikin su tayi da mai sannan ta sa musu kaya marar nauyi kasancewar yau Saturday babu makaranta.Kai su parlor tayi ta zuba musu abinci sannan ta tafi d'akin Ibrahim.
"Oya saura kai"
Tashi yayi yana mik'a yau dai tun kafin ki zo na shirya.
Wuce wa toilet tayi shima ta wanke shi tas dama sunyi brush tare da asuba suka fito.
Wannan shine tsarin Zainabu tun lokacin da ta waye sai ya zamana Ibro ya daina wanka da kansa kullum zata yi masa morning and night ('kalubale gare ku mata sai kuce mijin ku k'azami ne shin kun koya masa tsaftar?ko kuwa kuna tsaftace shi?da kin gane halin mijin ki zauna kiyi nazari ko kuma kullum zaku kwanta ke ki k'irk'iri wankan da dole za ku yi idan ma yana da tsafta kiyi training din sa yadda Zainabu tayi).
Suna fitowa su Yusuf suka ruga wurin Abban su.
'Daukan su yayi da kansa yaje kitchen ya wanke musu hannu ya kai su d'aki,littafin a koyon karatu ya basu da sweet da biscuit da juice yace suyi karatu na 2 hours ya rufe musu k'ofa.
Yana fita ya tarar Abu ta canza wata kwalliyar tana zuba abinci idan da sabo kam ya saba da wannan nishad'in.
Murmushi ta saki ta d'auko plate ta zuba suka zauna a k'asa.
A kullum idan yana gida Abu ke bashi abinci kuma kullum akwai salo da take me jan hankali.
Kamar kullum zaunawa tayi ta bud'e k'afafuwan ta ta zaunar dashi a tsakani cinyoyin ta a saman nashi ta fara bashi abinci.
Murmushi yake a zuciyar sa yana gode wa Allah daya bashi mata irin Abu.

Follow me on Wattpad,comment and vote please.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Jul 09, 2020 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

MUTUWAR AUREWhere stories live. Discover now