Part 3

253 14 1
                                    

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

MUTUWAR AURE

LAURATU ABUBAKAR

HELLO
THIS IS A NOVEL BY ME (Lauratu Abubakar)to entertain and educate you during this quarantine period.It's a fiction,yes it's a fictional story written in HAUSA.
In this novel I'll be teaching you romantic tricks which you should try and also cooking,who doesn't love a delicious meal?nobody,again gyaran jiki you should look takeaway and amm also love tricks in general.kun sanni babu wasa so you should follow up,comment and vote don't forget to follow me on Wattpad @lauratuabubakar
Please don't pirate me,my book and I.
It's a criminal offense!
Create your own work
Also,there will be a RABBANA (Prayer)at the end of every page (Please memorize each everyday)even if you do please read them as I'm posting.
May Allah reward us all.Ameen

Page 3

Ya labarin Ibrahim?
Ibrahim kwanan sa uku a garin Abuja ya fara fafutukar neman gida me sauk'i,a kwanaki ukun nan an hada shi da agents da yawa na arean saboda ya samu gida me sauk'i da kyau.
A lokacin da Ibrahim ya cika sati d'aya sun dai-daita da agent akan zai biya na shekara nan da satikai zai tare.
Babban al-amarin da ya faru maigidan su ne bashi da lafiya,rashin lafiya me tsanani kuma shine babba a wurin.
Gashi Gyallesu babu isasshen network da zai yi waya.
Haka yayi hak'uri dan aiki sun masa yawa.
Rik'on amanar sa yasa iyalan Alhaji d'ora shi kan komai.
Ibrahim kasuwanci suke yi.Alhaji Muhammad shi ne wanda tun Ibrahim ya na k'olo ya d'auke shi aiki,ganin k'wazon sa yasa ya 'yanta shi har ya d'ora shi a business d'in sa.
Jinyar Alhaji ita ta d'auki tsawon lokaci duk da Ibrahim na son tafiya haka ya hak'ura.
Kullum da tunanin Zainabu a zuciyar sa.

Yau ta kama Laraba yau garin Gyallesu yayi babban bak'o wato Ibrahim.
Bai sha wahalar gamsar da iyayen sa ba don kowa ya shaide shi da halin kirki.
Zainabu kam kamar an tsunduma ta a aljanna don murna.
Nan aka yanke satin gaba za'ayi biki a tare.

Inna Sahura sanin yarinyar ta ba budurwa tayi aure ba ya dame ta amma haka ta danne ta shiga shirin gyara yarinyar ta.
A sati d'ayan nan gaban Zainabu baya rabuwa da had'in man ayu da man damo da kuma kitsen zakara (BABBAN SIRRI).
Inna Sahura bata da wata wayewa amma tasan matsi me inganci.
Idan zatayi wanka takan dafa mata ruwan wanka da lalle da ganyen magarya (SIRRI).
Wad'annan sune gatan da Sahura ta yi wa d'iyar ta.
Ba wani gyara bane amma a sati Zainabu ta washe tayi kyau dai-dai nata.
Kayan daki ma an mata dai-dai gwargwado dan gado ne na katako me kyau aka mata da kujeru sofa set daya.
Su inna gona suka sayar dan kyautatawa d'iyar su.
Ranar biki anyi an gama duk da bawani taro akayi ba,masu habaici sunyi masu zund'e sunyi.
Nasiha kam Zainabu ta sha sosai da kuka.
A ranar Zainabu tayi sallama da Gyallesu
MAHAIFARTA FARIN CIKIN TA KUMA BAK'IN CIKINTA.

Abuja
A kori kura aka yi shata da kayan d'akin da sauran kayan su su kuma suka hau motar haya.
Tun a mota Zainabu ke kuka a hankali Ibrahim ke rarrashin ta.
Tun k'arfe goma na safe suka fito basu sauk'a ba sai wajen k'arfe shida abinka da k'arfen nasara ga tsayawa da suka yi tayi.
A Mararaba suka sauka can farkon gari.
Gidaje basu yawaita a arean ba sannan ba wasu masu kyau bane.
Gidan da Ibrahim ya kama suka sauk'a nan ya nuna mata ko'ina a gidan.
Fita yayi ya sayo musu abinci ya kai wa Zainabu nata ya dawo d'aki da nasa.
Zainabu ce ta janyo ledar abincin taci dan kuwa yunwa take ji.
Tana gamawa Ibrahim ya shigo
"Kinga Zainaba bawa baya wuce k'addarar sa,kiyi hak'uri ki saki zuciyar ki insha Allahu baza kiyi kuka dani ba".
Nan yayi mata nasiha me ratsa zuciya sannan ya d'ora "motar kayan mu bata sauk'a ba d'akin ki babu katifa idan babu damuwa ki koma can zuwa gobe kafin muyi gyara".
A daren Zainabu ta kwana d'akin Ibrahim shi kuma yana kujera.
Washegari da asubahi motar kayan su ta iso.
Gari na wayewa Ibrahim ya kira aka zo aka yi musu gyaran gida.
Zuwa k'arfe takwas an gama komai.
Zainabu da ke kwance a d'aki tayi shiru tana tunanin sabuwar rayuwarta.
A ranar basu yi barci ba sai da suka gyara gidan tas.

Bayan sati d'aya
Rayuwa na tafiya da dad'i da babu dad'i a cikin satin nan sau d'aya Ibrahim yayi attempting maida Zainabu cikakkiyar mace,ita kuwa a daren ne ta tuno abinda ya faru da ita take ta sume komai daya faru ya dawo mata.
Ya tsorata matuk'a dan haka babu abinda ya k'ara faruwa.
Ibrahim ne ya samu Zainabu bayan ta gaida shi ya kalle ta
"Zainabu akwai islamiyya ta matan aure a bayan layin nan ina so in saki idan kinaso"
Murmushi tayi kanta a k'asa "duk abinda ka yanke yayi mini".
Numfashi Ibrahim ya ja ya kalli Zainabu shi a rayuwar sa yana son mace wayayyiya wanda ta goge sosai duk da kasancewar sa d'an k'auye amma gashi ya auri 'yar k'auyen kuma babu wayewa.
"Dole in canza ta"
Ya fada a fili.
Wata islamiyya ya shigar da ita wanda sai da yayi bincike ya tabbatar ana koyar da hak'k'ok'in aure da zamantakewa sannan ya sata.

Kwanci tashi babu wuya wurin me rai yau ne Zainabu ta cika shekara d'aya gidan Ibrahim.
Yadda suke rayuwar su haka suka saba.
Yanzu akwai fahimtar juna a tsakanin su
A lokacin ne Zainabu tayi k'awa Fatima.
By now kowa ya ganta bazai ce daga k'auyen Gyallesu ta fito ba.
Fatima mak'ociyar su ce kuma 'yar ajinsu.
Fatima ta girmi Zainabu amma suna girmama juna sosai.
Yadda Zainabu ke lura da Fatima da mijin ta sai abin yake wa Zainabu dad'i,wani lokacin tayi ta tunani ita kadai.
A k'arshen shekarar nan ne halittun Zainaba suka cika kuma a k'arshen shekarar ne ta zama cikakkiyar mace.
Duk da samun Ibrahim bashi da yawa amma yana kamanta wadatuwar iyalin sa.
A wannan lokacin ne Zainabu ta samu ciki.
Hutu Ibrahim ya d'auka suka tafi Gyallesu da Zainaba.
Zainaba har ta manta k'uncin rayuwa amma tana shiga Gyallesu ta tuna.
A haka suka yi d'an hutun su suka koma.

Na gaji
Please don't forget to follow me on Wattpad @lauratuabubakar

RABBANA 3
Rabbana atina fiddunya hasanatan wa fir akhirati hasanatan wa qina adhabannar.

MUTUWAR AUREDove le storie prendono vita. Scoprilo ora