Part 1

555 36 9
                                    

MUTUWAR AURE

LAURATU ABUBAKAR

HELLO
THIS IS A NOVEL BY ME (Lauratu  Abu
bakar)to entertain and educate you during this quarantine period.It's a fiction,yes it's a fictional story written in HAUSA.
In this novel I'll be teaching you romantic tricks which you should try and also cooking,who doesn't love a delicious meal?nobody,again gyaran jiki you should look takeaway and amm also love tricks in general.kun sanni babu wasa so you should follow up,comment and vote don't forget to follow me on Wattpad @lauratuabubakar
Please don't pirate me,my book and I.
It's a criminal offense!
Create your own work
Also,there will be a RABBANA (Prayer)at the end of every page (Please memorize each everyday)even if you do please read them as I'm posting.
May Allah reward us all.Ameen

PAGE 1

AURE
Zainabu ce zaune fuskar ta duk ta kumbura saboda kuka.
Gefen ta A'i ce tana rarrashin ta.
A hankali ta fara bayani......
Aure kalma ce mai rai,ma'anar ta na da yawa.
Aure rayayyiyar halitta ce wanda ba'a buk'atar mutuwar ta sai k'addara.
Idan da mishkila akan rabu amma ko babu mishkila k'addara kan afkawa.
Wasu sunyi dace wad'an su kuwa basu dace ba.
Zan iya saka kaina cikin masu sa'a dan kuwa na dace da masoyi na gaskiya.
Shekarar mu goma da Ibrahim amma babu fad'a bare yaji,duk da gwaggwarmayar rayuwa hakan bai hana mu rabuwa ba.
Kafin auren mu mun wahala kasancewar k'auyen nan da al'adu masu tsauri.
Ibrahim ya ji ya gani sannan ya tsamo ni daga k'unci da tsangwama,ni kuwa me zan ce banda addu'a ga mijina sannan nayi addu'ar kar MUTUWAR AURE ta riske mu.
Sai dai kana naka Allah ma na nasa ban taba tunanin  rabuwa da mijina ba.
Ibrahim shine hasken rayuwata .
Inna ce ta shigo ta kalli Zainabu ta girgiza kan ta "Haba Abu sau nawa zan hanaki wannan kukan da surutai?kin zo kin saka k'anwar ki a gaba da surutai kuna kuka anya Abu kina tare da hankalin ki?".
Zainabu ce ta share hawayen ta ta kalli Inna "Inna ban san halin da Ibrahim yake ciki ba,Inna zasu wahalar dashi,Inna wallahi Ibrahim bai aikata abin da ake tuhumar shi da shi ba ".
Kuka ne ya kufce mata
A hankali Inna ta fuskance ta "Abu Allah yana tare da mai gaskiya,Ibrahim addu'ar ki yake buk'ata ba kuka ba,insha Allahu Ibrahim zai fito dan Allah ki kwantar da hankalin ki".
Zainabu ce ta tashi ta fice.
Cikin jimami Inna tace "Allah ya fidda ku Zainaba".

Ibrahim ne zaune a cell babu tunanin da yake sai na matar sa Abu.
Kasancewar ta 'yar k'auye bai hanata gogewa wajen soyayya ba.
Baya iya kwana sai tare da ita,baya iya cin abinci sai da ita.
Komai sai da Abu yake iya wa.
Yau gashi ya kwana babu ita ya yini babu ita,ji yake yi kamar an zare masa laka.
Tun yana daure wa har ya kasa ya fara kuka kamar yaro.
Lallai sabo turken wawa bai san haka Abu ta baibaye rayuwar sa ba sai yau.
Shin yanzu wane hali take?
Ya yaran su?
Ta iya barci?
Da wannan tunanin yaji ana k'wank'wasa teburin da ke gefensa.
Firgigit ya dawo hayyacin sa.
Wata yaloluwar taliya aka ajiye a gaban sa a cikin wani mataccen kwanon roba duk ya 'bule,fara sol da wani ruwa-ruwa ko mai babu bare miya.
Ko ba'ayi magana ba yasan abincin sa ne kuma a hakan jollof ne.
Haka aka kawo masa jiya yak'i ci saboda shi ko a gida idan ba abincin Abu ba baya iya cin na waje.
Ko ruwa ya kasa sha a wurin saboda ko ruwa ba a ko'ina Abu ke barin sa ya sha ba.
Shiru yayi yana tunanin rayuwar sa ga k'ishi ga yunwa.
Shi abin da yafi damun sa ko kad'an ba'a fara azabtar dashi ba,babu tuhuma babu komai tun jiya.
Jira yake yaga inda rayuwar sa zata k'are.

Abu ce ta fito daga kewaye ta ajiye buta ta nufo tabarmar dasu A'i da Inna suke.
A nutse ta zauna tana gyara d'an kwalin ta.
Inna ce ta kalle ta "ki kwantar da hankalin ki Ibrahim kamar ya dawo ne".
Murmushin da yafi kuka ciwo Abu tayi sannan ta ja pillow ta kwanta ta fara tunanin rayuwa.

WAIWAYE
Zainabu da Aishatu sune diyan Inna da Baba Isubu.
Haifaffun Gyallesu ne gaba da baya.Suna zama a Dalalle.A  Gyallesu a k'ark'ashin k'aramar hukumar Zaria dake nan kaduna.
Baba Isuhu na iya k'ok'arin sa a kansu,manomi ne sannan yana kiwo.
Inna Sahura ita ce matar sa d'aya tilo da yaran su biyu.
Zainabu ce babba sai data tasa har takai shekarun aure (11)sannan Allah ya albarkace su da Aishatu.
Duk da Sahura tasha gorin rashin haihuwa haka ta jure har Allah ya ida nufin sa.
Shi ko Isubu duk da Zugar k'arin auren da ake masa baiji ba.
A shekarun Zainabu (Zainaba ko Abu wasu kan ce Me tagwayen suna)na 11 bata da masinsini saboda bata da garin jiki hakan ne yasa ba'a mata zancen aure ba.
Yau ta kama laraba ranar cin kasuwa a Gyallesu
Dan haka Abu ta caba kwalliya ta tafi gari.
Bayan maghriba abokanan tafiyar ta sunyi gaba ta taho tana 'yan wak'en ta a hanya taji an shak'e ta.
Innalillahi wa inna ilaihir raji'un,a wannan ranar aka yi wa Abu fyad'e.
Abu da k'aramin gari gashi lokacin ilimi bai wadatu ba nan aka shiga rad'e-rad'en Abu.
Iyayen ta basu ji dadi ba sam.
Bayan watanni biyu Abu ta fara bud'ewa alamun ciki ya tabbata a tattare da ita,tsangwama babu wanda bata gani ba,har fita ta daina yi,zund'e ta ko ina.
Da taimakon Inna Sahura Abu ta rabu da cikin nan dan kayan bauri da d'aci tayi ta hada mata har tsawon kwanaki uku.

Na gaji
Comment,vote and please follow

RABBANA 1
Rabbana tak'abbal minna innaka antas sami'ul alim.

Ameen

MUTUWAR AUREWhere stories live. Discover now