Part 2

247 18 0
                                    

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

MUTUWAR AURE

LAURATU ABUBAKAR

HELLO
THIS IS A NOVEL BY ME (Lauratu  Abubakar)to entertain and educate you during this quarantine period.It's a fiction,yes it's a fictional story written in HAUSA.
In this novel I'll be teaching you romantic tricks which you should try and also cooking,who doesn't love a delicious meal?nobody,again gyaran jiki you should look takeaway and amm also love tricks in general.kun sanni babu wasa so you should follow up,comment and vote don't forget to follow me on Wattpad @lauratuabubakar
Please don't pirate me,my book and I.
It's a criminal offense!
Create your own work
Also,there will be a RABBANA (Prayer)at the end of every page (Please memorize each everyday)even if you do please read them as I'm posting.
May Allah reward us all.Ameen

Vote of thanks 🙏❤️
Thanks for the love
Even though it has been long before i started this novel (after MATAR AURENA)May be you could have even forgotten me but you're still with me the love you are showing me is beyond comment .Thank you very much i love you ❤️ .

Page 2
Bayan zubar da cikin Zainabu maimakon komai ya canza sai ma hantara da 'kyamata.
Duk inda taje ana yi mata kallon me yawon ta zubar.
Rayuwa tayi wa Abu 'kunci fiye da 'kima.
Ya zamana Abu bata da wurin zuwa sai bayan gonar babanta ta zauna.
Yau Lahadi yau ce ranar da Ibrahim ya dawo daga Abuja.

Wanene Ibrahim?
Ibrahim d'a ne ga Malam Mudi me faskare.
Haifaffen Gyallesu ne shima gaba da baya.
Tun tasowar sa ya tafi garin Abuja  almajiranta.
A halin yanzu yayi sauk'ar al-k'ur'ani mai girma daga nan ya shiga fantamawa neman kudi saboda idon sa ya bude da gari sosai ga girma
Yakan je yayi dako da wasu ayyukan k'arfin domin rik'e kan sa.
Shekaru na tafiya kasuwancin Ibrahim ya bud'ad'a sosai,sai ya zamana shi da garin Gyallesu sai aike don kuwa sai ya shafe shekaru uku bai zo ba.

Tafiya yake da k'afa yana ganin chanjin da garin ya samu kasancewar Gyallesu na samun cigaba sosai.
Wani abu ne ya d'auki hankalin sa ya tsaya kalla,ba wani abu bane illa wata kyakkyawar gona me furanni kamar ba jeji ba yana matuk'ar k'aunar fure dan haka ya k'arasa a hankali.
Wata yarinya ya gani dake zaune tana kallon wuri d'aya.
Da alama tunani take.
A hankali ya k'araso wurin da Abu ke zaune.
A razane ta juyo nan ta ga Ibrahim.
Murmushi tayi ta kalle shi duk da yayi shekaru uku baya gari idan ta ganshi dole ta gane saboda yadda 'yan mata ke zancen Ibrahim kullum.
"Yaya Iro yaushe a gari,bansan ka dawo ba"
Murmushi yayi "Hanne ko?"
Ita ma murmushin tayi tace
"Zainabu dai".
Nan ya shiga canka har dai ta masa bayani.
A hankali ya fara tambayar ta kan garin.
Nan dai Ibrahim bai barta ba sai da ya jata da hira sosai.
Shi dai Ibrahim mutum ne me son jama'a kowa yana haba-haba dashi don haka kusan kowa ya san shi ga kyauta da girmama na gaba.
Nan yake shaida mata yanzu shigowar sa gari .
Tashi yayi yace "ke kadai anan da alama babu abinda kike yi ki tashi mu shiga tare mana".
"Ka barshi idan na gama zan shiga".
Nan ya matsa mata suka taho suna tad'i.
Karo na farko bayan afkuwar annobar nan da Abu tayi farin ciki.
A hanya kowa ya kalle su sai harara ake wa Abu shi kuwa sai gaisuwa da ban gajiya.
Haka sukayi sallama.

Ibrahim kamar yadda aka saba iyayen sa sun tarbe shi da dangi.
Nan 'yan mata suka fara kwalliya suna zuwa sannu da zuwa.
Kowa da kalar kwarkwasar ta.
Kafin yamma tayi 'yan mata sunfi goma suka yo girki na kece raini aka kawo wa Ibrahim.

Yau take kwana uku da dawowar Ibrahim,zaune yake a daki yana duba wani littafi abokin sa ya shigo.
"A'a malam Iro ana karatun ne?"
Ibrahim ya kalli Musa
"Malam Musa ana fama"
Nan suka hau hirar yaushe gamo
Nan yake jin labarin fyad'en da akayi wa Zainabu da rashin auren ta.
Take tausayin ta ya kama shi ya tuna had'uwar su.
Shi kam tausayin ta ya ratsa shi nan dai a wayon ce yayi masa tambayoyi a kanta.

A b'angaren 'yan mata kowa k'aunar Iro d'an Habuja yake,burin kowa ya aure su su tafi Habuja.

Suna gama hira Ibrahim ya dauki hanya sai gidan su Abu.
Nan yayi sallama da ita.
Tayi mamaki matuk'a har tasa a ranta ko dai masu wulak'antata ne suka zo har gida?.
Da k'yar Inna ta sa ta fita.
Ganin Ibrahim ya sanya tayi murmushi.
A hankali ya ke janta da hira har ta saki jiki.
Ba su rabu ba sai da ya jaddada mata zai zo gobe.
Ko da ta shigo ta bawa Inna labari sai zuciyar ta ta sosu
"Kinga Zainaba ki kare mutuncin ki,bayan da k'addarar nan ta auku samarin garinnan duka babu me zuwa wurin ki sai don biyan buk'atar su ba aure ba,kink'i aminta suna bibiyar ki da sharri,kiyi hak'uri kici gaba da hak'uri kar ki canza.'Yan birni wayo garesu watak'il yaji labari ya lalla'bo".
Shiru Abu tayi sai wasu siraran hawaye da suka sau'ko mata.

Bayan tafiyar Ibrahim ya shiga gari a sirrance yayi bincike kan Abu a take hankalin sa ya kwanta da ita.Tausayin ta ya mamaye shi.

Washegari ya sami Malam Mudi da maganar,kasancewar sa me ilimi a take ya amince.
Mahaifiyar sa kam bada son ranta ba amma babu yadda ta iya.
Kishiyoyin Dija (Mahaifiyar Ibrahim)sai zund'en su ake.
Abin da bai wuce sati d'aya ba Malam Mudi yaje neman auren Abu kuma an bashi.
Su kuwa 'yan matan k'auyen babu wadda bata k'ara tsanar Abu ba a cewar su ta asirce Iro.

Har gida an biyo Abu anyi mata d'iban albarka.
Mahak'urci mawadaci yau jama'ar Gyallesu suka shaida auren Ibrahim da Zainabu akan sadaki dubu goma lakadan ba ajalan ba.Allahu akhbar bayan gwaggwarmaya yau jama'a sun ji sun shaida.

Sadakin Abu ya tsole idon mak'iya dan kuwa babu wanda sadakin ta ya haura darajar dubu na dukan dubu har biyar.
Lallai Iro ya cika gwarzo kuma namijin gaske.
Abu da ake zund'en ta ta rasa miji yau gata da Iro gwarzon namiji son kowa.

Bayan d'aurin aure Iro ya tafi Abuja da zummar zai nemi inda zai ajiye matar sa kafin ya dawo.
A cewar sa sati biyu sai gashi yau watanni biyu bai dawo ba.
Tsangwamar Abu ta k'aru dama bata fita sai ya zamana har gida ake zuwa ko ta katanga.
Hatta mahaifan Abu basu jin dadin rayuwa a Gyallesu.

Yau ya cika watanni uku bai dawo ba.
Shin ya Ibrahim yake?
Ku biyo ni a next page
Please don't forget to follow me please.

Our RABBANA
2.Rabbana waja'alna muslimaini laka wamin dhurriyatani ummatan muslimatan laka wa arina manasinaka watub'alaina innaka antattawwabu raheem

MUTUWAR AUREWhere stories live. Discover now