82

5.2K 294 0
                                    

82

  Idon Aysha k'yam akan ya khaleel, yayinda shikuma ya lumshe nasa, bayansa ya maida ya jingina da kujerar, tamkar mai karanta labarin novel ko maibada labarin wani film dayake shauk'i.
       Hannunsa d'aya nakan cikin Aysha, d'ayan kuma yana shafa sumar kanta ahankali.😉👍🏻

       "Hummm karon farko da Ibraheem khaleel yaji fad'uwar gaba yayin kallon mace, wadda bama takai macenba. aranar dana dawo daga k'asar Tanzania bayan aikin kwanaki 70 danayi a can, kaitsaye nabama su Adams damar wucewa dani gida, saboda matuk'ar gajiya da kasalar jiki dake tartare dani. Ina cikin shauk'in son ganin mo... Momy aranar, saboda sayo mata wata sark'a data dad'e tana so, amma bata samu sayaba, nikuma cikin ikon ALLAH saina samu wannan sark'ar zinari acan, wannan ne dalilina Na d'okin ganinta."
        "Sabon labari a shafukan tarihina, koda Na sakko amota sainaci karo da tauraruwa mai wutsiyar alkairi........
    Da sauri Aysha tabud'e idonta, shima yabud'e, suka kalli juna, cikin turo baki Aysha tace, " nice tauraruwa mai wutsiyar?."
     Guntun dariya yayi, yaduk'o ahankali ya sumbaci goshinta, "a'a fa, bakiji minaceba? Tauraruwa mai wutsiyar alkairi".
      Baki Aysha tamurgud'a tana kauda idonta daga kansa, shima kauda kan yayi yana murmushi.
      Yacigaba da fad'in, ''akanki idona ya sauka kaff yawan jama'ar dake harabar gidan, bak'aramin fad'uwa gabana yayiba lokacin dakika d'ago manyan idanunnan naki kema kina kallona kuna magana keda d'iyar iya hama, bansan yazan misalta miki halin dana shigaba alokacin saboda rud'ani, (small girl like you kina Neman sakani Na rasa tunanina) bak'aramar jarumta nayiba wajen tattare dukkan hankalina namaida kansu Ammah, gaisawa nakeyi dasu ammafa dukkan hankalina nakanki, burina kawai nasake kallonki, amma hakan batafaruba.
    Bamma sake ganinkiba saida Mamie takawoku domin yimin gyaran d'akina.
     Hummm bazaki ganeba A'eesha, wlhy lokacin dana bud'e k'ofa wa Anty mamaie naganki zuciyata bugawa tayi tamkar zata fito, saida Na had'a da addu'a gudun kar Anty Mamie ta fahimceni.
      Inakan Sani nasakaki wankin toilet alokacin, sannan kina shiga natura bishirah kar6omin tea badan inason shaba, saidan kawai nagankine atsanake.
       Zaman jiranki nazaunayi har kika gama kika fito, lokacin dakika fito kintadda ina latsa waya ko? Bakomai nakeyiba face video d'inki, duk abinda kikeyi inata kallonki ta wayane, harnabaki umarnin cigaba da aikin, da lokacin da kika d'auki bedsheet zaki shimfid'a Na hanaki........
    ......."kadai dakamin tsawa".
    Aysha tayi maganar tana cije la66anta.
    Murmushi yayi, kawai yana cigaba da zagaya hannunsa akan cikinta.

      Daban Daka miki tsawarnanba da tabbas babu makawa saikin harbor jirgina alokacin.      natsuwarki itace Abu nabiyu daya kuma zuzuta wutar sonki araina, inason mace mai yawan nutsuwa, gakidai k'arama alokacin amma komai naki mai ajine.
     Bank'i nakasance dakeba tun alokacin, saidai k'ank'antarki tamin katanga dahakan, kuma kodama kinkai girman dazan iya aurenki alokacin to tabbas, tarbarki nace inasonki shine babbar matsalata, Dan maganar gaskiya bazan iyabama.

      Aysha tace, "sabodami?".
    
    " saboda banason raini".  'Yay maganar yana jan hancinta".

    K'aramar dariya Aysha tayi tareda salute nashi, cikin salon kissa tace, "agaida boss".
           Dungure kanta yayi yana mata hararar wasa, shima yace, " agaida 6arauniyar zuciya".
     Atare suka tuntsure da dariya, saida sukayi mai isarsu sannan khaleel yacigaba da fad'in.
      "Kinsan wani Abu?".
     " a'a saika fad'a".

   Bak'aramin kamu kikaiminba A'eesha, abubuwa dayawan gaske sunfaru alokacin, Wanda tariyosu ayanzu 6ata lokacine, amma nasan kema kin sansu, bantsinci kaina adamuwaba sai lokacin dana daina ganinki gaba d'aya. narasa wanda zan tambaya agidannan yabani amsata, kwatsam ranar inacin abinci dainaji musleem Na tambayar Maman yara ina kike?.
    Sosai maganar tasu taja hankalina, ni saima ranar nasan Maman yara takawoki gidan.
      Yanda Maman yara take amsama musleem maganganunsa sainaji ban yarda da itaba, domin ni mutumne da inhar zakayi maganar dabata dace da tuharkaba saina ganeka, tawannan hanyar nakanyi saurin cafke mutum mai laifi.
    Daga wannan ranar nafara bibiyar Maman yara batareda tasaniba.
        Abinda nafara cin karo dashi akan Maman yara shine mu'amulla da momy a6oye, dakuma mu'amullah da Ummi amarya a6oye, bankawo komaiba sai munafunci irinna 'yan aiki akan masu gida, wannan ne yasakani rashin maida hankalina akan wannan matsalar, burina kawai nasan inda kike, dukda dai Maman yara tace kinje karatu.
        Acikin bibiyartane nagane cewa zaku bar Nigeria, kuma tabbas ta Abuja zaku tashi.
       Nayi amfani da wani abokina dake aiki a nan airport, kullum yana cikin sakamin ido akanki, har yagano ranar dazaku bar k'asar, alokacin bana nan, nima nayi tafiya.
   Yaturamin dukkan bayanai akan tafiyar taku, harda biye-biye wasu k'asashe Wanda bansan miye dalilin hakanba, inda ace aranar dazaku tafi INA nan, nagakuma Kubrah, to tabbas dolene nazargi wani Abu, kuma dolene nafara binciken kubrah, amma sai'aka samu akasin hakan, bana k'asar, kuma bayanai akanki kawai Na nema banda Wanda zakuyi tafiyar tare.
     Tunda nasan k'asar da aka kaiki nasaka Naufal fara bibiyarki, yana kawomin bayanai sosai akanki, amma baita6a sanarmin akwai wani sirri a tafiyar takiba.
       Naje Na dubaki a islands batareda kin saniba, sannan bayan kin kammala karatu alokacin narasa mizan baki amatsayin taya murna, koshi Naufal baisan komai gameda keba, kawaidai ina fad'a masa k'anwatace ke.
        Naje Spain alokacin nida Adams da Joseph, saimuka shiga wani shago domin munabin wani alokacin, babu abinda ake siyarwa a shagon sai irin furanni da kayan masoya d'innan, jinai kawai shauk'i yakamani, da tunanin nesa tazo kusa agareni, awannan shagon nasayi wannan ruwan mai d'aukeda k'ananun kifaye aciki, tareda flower, itakam wak'an dana rubuta ajikin takardarnan awajen Adams najita yanaji,  kawai sainaji baitin yayi daidai da shauk'ina, shine narubuta nasaka a sak'on, nabada aka kaima Naufal domin yabaki.

CIKI DA GASKIYA......!!Tahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon