43

4K 315 0
                                    

43

         Ɓangaren baffah yaje suka gaisa, saidai baiji dad'in yanda baffan yamasaba, Dan baisakar masa fuskaba kamar yanda yasaba masa.
     Kasa tashi yayi daga gaban baffah, yay shiru kansa ak'asa ya tsurama carpet ido.
        Baffah dake kallonsa a sace yace bawajen aiki zakaje baneba?.
    Eh can zanje baffah.
    To katashi karka makara.
    Shiru ya khaleel yayi, yakasa tashi, wannan yakuma tabbatar masa baffah fushi yakeyi, inba hakanba daya hanashi fitar, zaice hannunsa bai gama warkewaba aii.
         Muryarsa cikeda d'aci yace kayi hak'uri baffah, inhar abinda yafaru jiyane ya6ata maka rai, ni bazan bijirema umarninkaba.
    Sanyi baffah yaji azuciyarsa, ya sauke ajiyar zuciya tareda guntun murmushi, shikenan mu'azzam, ALLAH yayi maka albarka, naji dad'in kasancewarka d'a nagari, amma wacece Aleeya?.
      K'asa yakumayi dakansa, muryarsa a sark'e yace baffah ban santaba.
     Bangane Baka santaba? Ba itace momynka tace kanasoba?.
     Humm baffah maganar gaskiya itace dama tace Na aureta, to nafad'a mata zanyi bincike akan yarinyar tukkunna, to bammayiba wannan al'amarin yafaru.
     Kai laurah kenan, to shikenan, kabincika d'in, inhar kaga itama tamaka saika fad'a mana, insha ALLAH zan had'a makasu Dan farincikinka.
      Zuciyarsa kamar zata faso k'irjimsa ta fito, yace to baffah, bara naje akwai aikin dazanyi.
     Shikenan, ammafa Kasan hannun nan naka da sauransa, saika kula, idankuma kadawo inaso ganinka.
    To, Insha ALLAH baffah.
      Yafita baffah nabinsa da k'yak'yk'yawar addu'a, tareda tausayinsa, yaron yanada halayya mai k'yau, ko kad'an bai biyo halin laurah ba, wannan yasaka yake matak'ar tausaya masa, saboda shikad'aine a samarin y'ay'an nasa bai more uwaba, damma Bilkeesu Na jansa ajikintane, shiyyasa yak'e k'ara k'aunar matar sosai.
 
        Koda yashiga wajen Ammah saiya taras bata tashiba.
    Fitowa yayi indasu Adams ke jiransa.
      Da sauri sukayi salute nasa atare, tareda tambayarsa hannunsa.
        Ya amsa musu murya a cinkushe, hakan ya tabbatar musu yau ogansu yana tareda damuwa.
      Da sauri Adams yabud'e masa motar tsakkiya yashiga.
     Yazauna yanamai lumshe idanunsa daduk suka canja kala zuwa jaa tun jiya.
      Motar tayi tsit, bakajin komai sai k'arar AC.
      Idanunsa a lumshe yace, "Adams wad'anda sukabi bayan Barau sun dawone?".
       Eh sir!, sundawo jiya da daddare, ammafa basu sameshiba, saidai sunkuma kamo yaronsa 1.
       Shiru yayi baice komaiba, har Adams yad'an kalleshi ta madubi, ganin idonsa a lumshe saiya d'auka ko barci ya d'aukeshine.
       Saida suka shigo katafaren Setesion d'in Nasu, Wanda yagama had'uwa, Dan yanada banbanci Dana ainahin police, Ahankali ya bud'e baki yace Adams muje d'akin bincike.
          Kakiramin juned da Faruk, Solomon, sai Taheer.
    OK sir!, Adams yafad'a yana fita amotar da sauri.
    Emmanuel yafito yabud'e masa motar, suma sauran securities d'in dake sauran motocin suka fito.
      Tafiya yakeyi cikin kasaitarsa da jarumta, saidai yanayinsa ya nuna baida k'arfin zuciya a yau.
       Sai gaisuwa k'ananun Securitys keyi tareda salutes nasa, hannu kawai yake d'aga musu, amma ko kallonsu bayayi.
        d'akin dasuka shiga ya tabbatarmin lallai d'akin bincikenne, ko ina Na d'akin zagaye yake da computers, d'akin kansa da zallar glass akayishi,  akwai mutane aciki sunata danne-dannen computers, wasu kuma rubuce-rubuce, kowa dai da uzirinsa, duk sanye suke cikin Uniform d'in police masu tambarin interpol abaya.
      Shigowar ya khaleel tasakasu mik'ewa gaba d'aya, suka k'ame tareda salutea nasa atare.
      Wasu kujeru dake gefe a shirye yaje ya zauna, duk wani ma'aikaci dake awajen yadawo gabansa ya tsaya, sunyi tsit suna sauraren abinda zai fad'a.
     Saida yagama k'are musu kallo tareda nazarinsu su duka, bai yarda yayi aiki da kowanne acikinsuba, Dan yanada tabbacin akwai munafukai acikinsu, ya sauke numfashi alokaci d'aya da furzar da huci.
         Sannan yagyara zamansa, yakuma kafesu da idanu, suma kowannensu idonsa Na Kansu, wani Na hango acikinsu sai ta6e baki yakeyi da hararar ya khaleel a fakaice, (araina nace gaskiyar ya khaleel fa, akwai muna fukai acikinsu).....
     Maganar ya khaleel ce takatsemin tunanina namaida hankalina akansa, jinayi yana fad'in, kuje duk d'inku nabaku hutun kwanaki 5, yau tsawon watanni 4 kenan dabaku aikin bincike akan Godwin amma babu wani kwakwkwarar magana, idan naso yin aikin da kaina zanyi nagano acikin kwana 1 kacal, amma ku sai yawo da hankali kukemin ko? Saboda anbaku aikin dayafi nawa muhimmanci, OK banida matsala daku, kuje Ku huta, amma Ku tabbatar idan har nagano saka hannun waninku wajen 6atamin aiki da akayi 3weeks daya wuce wlhy saiya raina kansa, kunsan halina basai wani yabaku labariba, zaku iya tafiya.
           Jikinsu duk asanyaye suka fara had'a kayansu suna ficewa, wasunsu basuda laifi, sakasu akayi akan dole, Wanda yake Harar ya khaleel kuwa sai jinjina kai yakeyi da cije le6e.
      Adams nakula dashi, yay dariya azuciyarsa, yana fad'in zakayi mai daliline alokacin da boss yakamaka dumu-dumu a hannunsa.
     Bayan duk sun fice ya khaleel yamaida kallonsa kan su Adams.
    Solomon & Juned kuyimin bincike akan dawa-dawaye a contact d'in barau modibbo, sannan da mutum nawa yake hud'a arana.
         Kai kuma Taheer kaida Faruk kumin binciken asusun bankin barau modibbo, da adadin kud'ad'en dake cikinsu, Kausar da Mahmud kuma inaso duk wani airport dake Nigeria ahana barau modibbo jirgi yatashi dashi, dadukkan wani abinsa mai muhimmanci kada yayi aiki, irinsu I'd cart dadai sauransu.
    Banason kuskure, Ku kula sosai akan abinda zakuyi, danshi tsuntsune mai wayo, *Tsuntsu mai wayo kuma, tabaki ake kamashi*.
     OK Sir!.
  Suka fad'a atare gaba d'aya.
  
Wani 6angare daban Na d'akin suka shiga, Adams ya kunna dukkan computers d'ikin, dandanan komai yakawo wuta, kowa yazauna gaban computer d'aya, shiru kakeji babu wani mai motsi, saina k'arar danne-danne, ya khaleel natsaye akansu saikace malami da d'alibai a d'akin exam.
            Faruk yad'ago yana fad'in lallai wannan mutumin d'an cakwakiyane, asusun bankinsafa kusan 16 ne, aciki da wajen k'asarnan, kai d'an bala'ine wannan wlhy sir.
     d'aure fuska ya khaleel yayi, yace Faruk ka kula, bawasane yataramu ananba, banason shashanci.
    Da sauri Faruk yace sorry sir.
    
    Kausar tace, "sir! Gashifa yana shirin barin k'asar ta Kano state, jirginsa zai d'aga zuwa k'asar Germany da k'arfe 5pm.
        K'arasowa ya khaleel yayi inda suke, yaja kujera ya zauna kusadasu, computer tamatso masa da ita, yasaka siririn farin glass a idonsa yafara dubawa anutse.
      Le6ensa ya cije sannan yafara danne-danne, zuwacan yace  Adams?.
    Da sauri Adams ya amsa da yes sir!.
    Kiramin number d'in Captain Salis muzambil.
   OK Sir!.
Da sauri yafara laluben number a contact d'in ya khaleel, babu dad'ewa yasameshi, saidai bai d'agaba, yakuma kira a alokaci nabiyu, saida takusa tsinkewa yad'aga, da sauri Adams ya karama ya khaleel a kunne, muryar Captain salis yajiyo yana fad'in sorry j! Wlhy ina wani aikine kana lfy?.
      Lfy lau Captain, ya aikinka?.
   Alhmdllh, kaima yanaka?.
   Munata fama fa.

CIKI DA GASKIYA......!!Where stories live. Discover now