76

4.3K 299 1
                                    

76

Tunda ya khaleel yafara bayani kowa yay tsirmai-tsirmai da idanu, dankuwa duk Wanda yake a 6angaren Ammah yaci meatpia d'in, Dan Tasleem ma sarkin tsoro hawaye takeyi, tasandai sungama aiki sukam, yau sai mutuwa🤣.
          Mama ce tadakama Aysha tsawa, tayo kanta zata daka, Ammah ta dakatar da ita.
    "Fad'ima kema bakida hankalin kamar iro, waishin kun mantane yarinyarnan k'aramin cikine da ita?, sokuke cikin yazube saboda rashin hankalinku..........?
     Maganar Ammah takatse yayinda sukaga Aysha nalayi, tamkar wadda tasha giya, dak'yar numfashinta ke fita, duk kanta sukayi suna kiran sunanta.
    Yarab Aysha tazube ak'asa asume, sallalami kowa yafara, Muhseen yafita da Sauri d'akko key d'in mota.
   Jikin ya khaleel ne yayi sanyi, dukda bai k'arasa inda Aysha takeba, amma idonsa Na kanta, gashi gaba d'aya mutan gidan sun rud'e, mamace kawai take tsaye agefe kamar ya khaleel, saidai itama hankalin nata amatuk'ar tashe yake.
         Baffah ya dakama ya khaleel tsawa akan yazo yad'auki Aysha yakaita mota.
        K'arasawa yayi ya d'auketa, koda yasakata mota bai shigaba, sai Anty Mamie ce tashiga tarik'e  Aysha, babu Wanda yadamu dashi motocin biyu suka fice aguje.

           🤔wai inama momyne?.
     
      Tunda hajia babba tabama khaleel meatpia tabar gidan, sai gidan Aminiyarta, cikin farinciki take sanar mata komai ya kammala, yau damuwarsu tak'are.
     Atare suka shak'e da dariya, suka tafa, hajia khaltum tace aminiya nasan dolene k'ungiya tabaki k'arin girma wlhy, dama abin yazo a dai-dai, jibine za'ayi gagarimin taron k'ungiya.
     K'yak'yal suka saka dariya.
      "Amma aminiya wani hanzari ba guduba, shin kinsaka Wanda zai kwashe meat pia d'in idan sunci?".
        "A, Aminiya daguduma kuwa, nasaka yarinyarnan Dije mai aiki, babu Wanda yasan yarinyar tanamin aiki ta k'ark'ashin k'asa aii, barama nakirata naji mike wakana agidan?".
         Kiran Dije momy tayi, babu dad'ewa dije ta d'auka, jikin dije har rawa yakeyi tace, " hajia akwaifa Matsala".
     Zumbur hajia babba tamik'e tsaye, ke banason mummunan labari kinfa sani".
        "Hakane hajia amma dolene nafad'a miki, ................kaf dije ta sanarma hajia abinda yafaru, tad'ora dafad'in amma hajia ki kwantar da hankalinki, yanzu haka naje nakwashe meatpia d'in dakika basu, Na canja dawani mai k'yau, koda d'auka akayi danyin bincike bazasuga komaiba, itakuma matarsa dazasu sami bayanai tasuma, bansan miya sametaba, yanzu haka suntafi asibiti. Kinga sauran aiki nakine, saikiyi azamar samun Wanda zai ida miki ita a asibitin".
      Ajiyar zuciya Momy tasaki, tace, " shikenan dije, ki kula da komai, yanzunnan zanzo gidan nima".
         A gaggauce Momy tayima hajia khaltum bayani, dukda a rud'e suke hakan baihanasu Neman yanda zasu salwantar da rayuwar Ayshaba, sungama shirya hajia khaltum zataje asibiti, Momy kuma tanufo gida.

***********
          Suna tafiya asibiti ya khaleel yanufi 6angarensu, meatpia d'in nanan inda suka barsa, tattarashi yayi yazuba aleda, yad'auki key d'in mota da sauri yafito. Aharabar gidan sukaci karo da Momy, kallon-kallo aka tsaya yi, amma dayake Momy A ce, saita wayance, tak'araso gun ya khaleel tana fad'in Ibraheem! Lafiyarka Kuwa? Naganka wani iri?".
         Hawayen dasuka mak'ale a idonsa suka ziraro, Momy tak'araso kusadashi sosai tana share masa, 'yan gidan wad'anda basubiba asibitin duk suna tsaye suna kallon ikon ALLAH.
       kad'an ya khaleel yazame jikinsa daga kusada Momy, yabi sauran 'yan gidan da kallo, yace, "duk Wanda yasan yaci meatpia d'in yashiga mota muje asibiti".
       Cikin dukan k'irji da zare ido Momy tace, " meatpia kuma? miyafaru dashi?".
        Bai bata amsartaba, sai cewa yayi "kedai Momy Shiga mota kawai muje asibiti".
      "Wane irin nashiga mota muje asibiti? Waimike faruwane? Ninasan ninayi meatpia agidannan yau, kuma anacewa duk Wanda yaci yashiga mota aje asibiti, Ibraheem banason kwana-kwana fad'amin miya faru!?".
    Tayi maganar ad'an tsawace.
      Rintse idanu ya khaleel yayi, bai cema Momy uffanba yara6a ta gefenta zai wuce, wata razananniyar tsawa ta Dana masa, "kai!!! Ibrahim, banason iskancifa, Dan ubanka inamaka magana amatsayina Na mahaifiyarka shine kake shareni?".
       Ransa amatuk'ar 6ace yake, amma cikin sanyin murya yace, " Momy mikeso nace mikine, kefa kika bada meatpia d'innan, kuma kinfi kowa sanin mikika zuba acik........
           Baikai k'arsheba ta tari numfashinsa, " minazuba Dan ubanka?".  
        "Momy A'eesha tace kinzuba guba aciki, kuma dabata ganiba bazata fad'aba, dukda zuciyata bawai ta amince baneba, amma inason Sanin mike tsakaninki da matar d'anki? tabbas akwai wani Abu 6oyayye tsakaninki da A'eesha, yazamemin dolene naje abincika duk Wanda yaci meatpia d'in agidannan".
             " yanzu nan Ibrahim harni kake zargi akwai wani Abu tsakanina da matarka??, harma zargina kakeyi nazuba wani Abu aciki nabaku kuci Ku mutu ko? To aii Alhmdllh tunda Baku kad'aine kukaciba, su Ammah ma sunci. shikenan naji, muje asibitin abincikasu".
       Babu Wanda yace komai duk suka Shiga mota, harda ita momyn.

CIKI DA GASKIYA......!!Where stories live. Discover now