42

3.7K 310 3
                                    

   42

     Falon yayi shiru, kowa ya maida hankalinsa ga baffah, dukda ba wannan ne karon farko da aka ta6a irin wannan taronba agidan kuwa.
     Amma a wannan karon sai taron yafirgita zuciyar wasu daga cikin al'ummar gidan, musamman ma hajia babba da gwaggo bintu, Dan taron harda su Aysha aciki, da ita kanta gwaggo bintun.
         Bayan an bud'e taro da addu'oi Ammah tafara magana.
       Nasan zakuyi mamakin wannan taro, to kudaina mamaki, nice nasaka babanku yayishi, maganar gsky taron yashafi wasunku, kuma ina fata yazama alkairi agaremu baki d'aya.
    Ta maida kallonta ga baffah, tareda jinjina masa kai, alamar tabar wuk'a da nama a hannunsa.
          Baffah yafara da sallama da nasiha, sannan yad'ora da fad'in wannan zama yashafi 6angarorine guda biyu zuwa uku.
    Na farko shine bintu wadda kuke kira Maman yara tanada alak'a ga fad'ima, nasan kuma duk kunsan haka.
    Duk suka amsa da eh.
    To alhmdllh, daga yanzun tafita daga jerin masu aikin gidannan, itama tadawo cikinmu, zata cigaba da zama wajen fad'ima insha ALLAH.
         Kowa ya nuna farincikinsa, Dan bazasu iya manta alkairin gwaggo bintu ba akan d'awauniyar yaran gidan, tundaga kan Amatullah taketa d'awainiya dasu, wannan yasaka taci suna Maman yara.
     Ayanda nakula hajia babba ce kawai batayi na'am da batunba, amma batace uffanba.
    Baffah yaciga da fad'in, akwai yarinyar Hama maisuna bishirah, zatayi aure nanda 2 month's idan ALLAH ya kaimu, to tunda bikinta yataho, itama mun dakatar da ita ta huta, ALLAH ya Sanya alkairi.
    Nanma akace amin.
      6angare na biyu kuma shine, za'a kawo sabbin masu aiki su hud'u insha ALLAH, dansu zama canji gasu bintu d'in.

       Kashi Na uku kuma shine maganar auren Mu'azzam!......
    Kowa Afalon saida yad'ago ya kalli baffah, musamman ya khaleel da k'irjinsa yay tsawar hadarin gabas Na tsakkiyar ogusta🤣.
     Hajia babba ma ta kafe baffah da kallon kid'ima.
      Ammah kam murmushi takeyi.
     Aysha kuwa aii atare k'irjinsu yabuga itada ya khaleel😆.lol
        Baffah yacigaba da maganarsa yana nazarin kowannensu, dariya taso kubce masa lokacin da idonsa ya sauka kan ya khaleel d'in, amma saiya danne ya kauda kai yana murmushi.
    Zaman khaleel ya isheni hakanan, Dan haka Na yanke hukuncin masa aure da mace tagari, wadda Na yarda da ingancin tarbiyyarta, ban hanaka anangaba idan kasami wadda kakesoba ka k'ara.
     Bawata baceba illah Aysha y'ar uwarka, yay maganar yana nuna Ayshar.
         Mutum hud'une suka zabura alokaci d'aya.
    Ya khaleel, Aysha, mama, hajia babba.😂
       Ya khaleel yay k'arfin halin fad'in baffah wannan y'ar yarinyar?.
     Kaci gidanku iro, dan k'aniyarka bakaine kata6a fad'amin kafison auren k'aramar yarinya ba? Shiyyasa ina dawowa jiya naga wannan y'ar albarka Na sanarma babanka matar aurenka tazo, haka kakeso muzuba maka ido muzama sakarkaru irinka?, ta maida kallonta ga sauran yaran, kutashi kujeku angama daku, inma da sauran bayani a nemoku daga baya.
       Kowa mik'ewa yayi yabar wajen, saidai Aysha kuka takeyi Wanda batasan dalilinsaba, Na dad'ine kokuwa Na bak'in cikine?.🤷🏽‍♀
 
Tambayar dayakamata musani kenan masu karatu😂.

Daga Baffah sai matansa da ya khaleel da Ammah aka bari awajen.
     Hajia babba tafara magana cikin 6acin rai.
    Gaskiya Alhaji wannan had'in bazai yuwuba, kuma shima aisai atsaya aji za6insa, yanada wadda yakeso aiiko.
        Baffah ya dubeta rai 6ace, to aii ban hanashi fad'ar za6in nasaba, shekaru nawa na6ata ina magana d'aya akan mu'azzam? Kinta6a tayani masa magana? Idan namiki maganar bacakike aure lokaci gareshiba?, to aii yanzu lokacin yazo.
    Kai mu'azzam wacece za6in taka? Kata6a sanar dani kanada wadda kakesone nahanaka?.
    Kan ya khaleel a k'asa yana sauke numfashi da k'yar, saboda damuwar dayake ciki, gawani Abu dayazo ya tokare masa mak'oshi saboda tashin hankalin had'ashi aure da waccan yarinyar da'ake shirinyi.
    Ya girgiza kansa ahankali saboda tambayoyin da baffah yay masa.
    Shiru yayi baice komaiba.
       Wannan ya k'ara hasala hajia babba, tace Ibraheem kabud'e baki kayi magana Dan ubanka, Dan bazan ta6a amincewa jinina yara6uda jinin Fad'ima ba, bazai yuwuba kuwa.
    Ya d'ago idanunsa jajur yazubasu kan hajia babba, please momy kiyi hak'uri, banida hujjar bijirema mahaifina, Dan yabani dama tuni, amma nayi sakaki da'ita.........
    Rufemin baki mara kunyar banza, ka isa kafad'amin mahaifinka? Nima aii mahaifiyarkace, wahalar ma danaci akanka ko Quarter d'inta baiciba, Dan Ubanka bakai kacemin kanason *_Aleeya d'iyar Alhaji Mudansir Na goma ba?._*
     Shine yanzu zaka canja magana anan? Kai sarkin biyayya? To magana d'aya nakeyi banyarda ka auri jinin fad'ima ba, inhar nice *Uwarka!.*
       Da Sauri mama ta nuna hajia babba zatayi magana baffah ya girgiza mata kansa, alamar kartace komai.
    Shiru tayi ta had'iye maganar ranta Na k'una.
      Anty Mamie da umme amarya dai basuce komaiba, amma k'asan ran Anty Mamie tanata farinciki da wannan had'in, Dan tana tausayama khaleel sosai, fatanta a kullum ALLAH yabasa mace tagari, to tana ganin ALLAH ya kar6i addu'arta kuwa.
         Ammah tace lallai Laure kin Isa, to bara kiji Na sanar miki, inhar ni d'innan Na haifi Abdullahi, shikuma ya haifi Ibrahim, to tabbas aurensa da d'iyar Fad'ima babu fashi, dagake har fad'ima babu Wanda ya Isa hanawa.
    Wlhy koda Ibrahim da Ai'shane kuwa, kingadai su za'ama auren ko? To koda zasu kashe kansune saina saka an d'aura auren, sannan arufesu aka bari d'aya, idan ana amarci alahira suje can suyi, Ibrahim kafara shiri, danna gama magana da k'anin mahaifin yarinyar, gobe idan ALLAH ya kaimu babanka Ma'aruff zasuje a tsaida magana, Aleya kuma take ko wacece? Idan kana buk'ata za'a iya had'a maka, babu ruwana dashiga hurumin ubangiji, wannan yarage ruwanka .
     Ammah tayi ficewarta.
     Baffah ma tashi yayi yafita, aikam hajia babba tafara zabga masifa, kowa na gidan yanajinta, ya khaleel yamik'e yabar musu falon, Dan shikad'ai yasan cikin masifar tashin hankalin dayake.
     Baita6a zaton baffah zai d'auki mataki akan rashin auren nasaba haka.
    d'akinsa yashige ya kulle kansa, yafad'a saman gado yana dafeda kansa dake masifar sara masa🤦‍♀, jiyake tamkar zai rabe biyu Dan ciwo.

Aysha ma nacan tana 6arzar kuka a d'akin mama, ahaka mama tashigo ta isketa.
    Da sauri tak'arasa gareta tajawota jikinta ta rungume, tana mai lallashinta.
    Kiyi hak'uri Aysha, nima bazan yarda a cutarmin dakeba, amma miyasa kawu bilya zaimin hakane? Miyasa bai fara sanarminba kafin ya yanke wannan hukuncin?, shin ya mance wacece Laurah?.
     Indan ta Ibrahim ne bazan ta6a damuwa da aurennanba, Dan yanada nagartattun halayen dadukkan macen kwarai zata sosu, amma mahaifiyarsa bazata kasance surukar arzikiba, bakuma zata ta6a barinku kuyi farincikiba.
    Gaskiya bazan amince a cutar da marainiyar ALLAH ba, Ammah kada kimin haka, ki sassauta Dan ALLAH, wlhy nice zan cutu Ammah, Dan ayshace zata shiga k'angin wahala.
    Kalaman mama sunkuma narkar da zuciyar Aysha, takuma rushewa da kuka tareda k'ank'ame mamar.

Har washe gari gidan tsit, kowa yashigo saiya San babu lafiya ga mutanen gidan, Dan raunin farincikin gidan yayi matuk'ar saukar farashin mizani, haka sukayi break fast sukuku, wanda babu Aysha aciki babu ya khaleel, hakama hajia babba da zuri'arta.
     Babu Wanda yatakura akirasu, Dan kowa yasan halin dasuke aciki.

______________________________

    Komai yinsa yakeyi cikin wani yanayi, kokad'an babu alamar d'igon walwala tattare dashi, ga d'unbin kasala daya tashi da ita ayau, hakan tafarune saboda k'arancin barci dabai samuba a daren jiya, saboda maganar auren nasa, yaja siririn tsaki tareda yaye towel d'in dake kugunsa bayan yasaka boxer, yad'an Mirza mai kad'an ajikinsa tareda feshe ko ina Na jikinsa da body spry d'insa mai dad'in k'amshi, yasaka farar vest sannan yasaka Uniform d'in aikinsa, yayi k'yau sosai, musamman dayagama tsuke kugunsa da belt.
    Wani turaren yakuma d'an fesawa kad'an, sannan yajawo takalmansa da safa yazauna kan sofa yana k'ok'arin sakawa.
    Knocking d'in k'ofarsa da akeyi yasakashi jan tsaki, da k'yar yabud'e baki yace ashigo.
     Shahuda ce d'aukeda tire Wanda aka shirya masa break d'insa.
    Cigaba yayi da saka takalmansa batareda yad'ago ya kalletaba.
    Taja table ta ajiye sannan tace ya khaleel ina kwana?.
      Yanzunma bai d'agoba ya amsa da lfy.
        Duk atsorace take da yanayinsa, dukda baya sakar musu fuska sukan gane yanayin farin cikinsa Dana damuwarsa.
     jin alamar tana tsaye akansa yasakashi d'ago jajayen idanunsa yazuba mata, cikin daburcewa tace dama um..um....Anty Mamie ce tace akawo maka break fast naka, ta..tace kaci please.
         Baice komaiba yamaida kansa yana k'ara gyara igiyar takalminsa.
    Da sauri Shahudah tabar d'akin, tanamai godiya ga ALLAH data fito lfy.
    Koda yagama bai kalli abincinba, yak'arasa gaban madubi yad'auki agogonsa yasaka, ya d'auki gun nasa yasaka a gefen k'ugu, sannan yad'auki jakkar lap-top nasa yanufi k'ofa.
        Harya kama handle d'in k'ofar saikuma yatsaya cak, tamkar Wanda aka kirawoshi.
    Gani yayi baidace yawatsama wadda tadamu dashi k'asa a idoba, yadawo baya tareda jawo table d'in da Shahuda ta ajiye break fast d'in gaban sofa.
    Tea kawai yahad'a kad'an yasha, Dan bayajin cin komai ayanzun.
      Yana gamawa yamik'e yafice.
     Babu kowa afalon, wannan yasakashi shiga 6angaren umme Amarya dake kusadashi, a ahanya sukaci karo zata fita aiki, ya risina ya gaidata kamar yanda yasaba.
    Daganan 6angaren Anty Mamie yashiga, itama sun gaisa a tsaitsaye saboda yana sauri kada ya makara.
    Anty Mamie tace aff babana naga kana sauri yanzu, amma idan kadawo inason magana dakai kaji.
    Kansa ya jinjina mata, yana had'iye wani mugun yawu yafice da sauri.
     Itama binsa da kallo tayi, zuciyarta cikeda tausayinsa.
     Daga nan 6angaren mama yashiga, bata a falo.
      Jiyo hayaniyar 'yan uku a bedroom d'insu yasakashi nufar can, saida yay sallama tabashi izinin shiga sannan yashigo.
       Cikin girmamawa ya gaisheta kamar yanda ya saba.
     Yasaci kallon mutuniyar tasa Aysha dake zaune a gado, mama ta tasata gaba, da alama ansakata cin abincin dolene.
    Dan turawa takeyi tana hawaye, dagani kasan Dan dole takecinsa.
      Sai da yamik'e sannan yace mama lfy takene? Ita wannan?, tanacin abinci tana kuka.
      Lafiyarta k'alau babana, iskancintane kawai, tunjiya darana tak'incin abinci, tazauna tanama mutane kukan isakanci, saikace wata yarinyar goye, tak'are maganar da Harar Aysha.
     Shima Harar Aysha yayi, batareda yace komaiba yajuya zai fita, mama saina dawo.
    To babana ALLAH ya tsare.
   Ameen mama yafita zuciyarsa Na k'una, Dan kukan Aysha da ranshincin abincinta yanada nasaba da aurensa da aka sakatayi dole.
   Ya cije le6ensa yayinda yake kutsa kansa 6angaren momynsa.
      Su Hasnah kawai ya Tatar afalo, suka gaidashi.
    Batareda ya amsa ba yace ina momy?.
    Husnah tace tafita tun d'azun.
       Fita kuma? Wajen aiki?.
     A'a gaskiya, koma wanka batayiba, kuma ita ta tuk'a kanta.
    Shiru yayi yana nazarin inataje da sassafen nan?.
    Yajuya yafita dad'an hanzarinsa..............✍






💋💋💋💋💋💋💋💋😍

CIKI DA GASKIYA......!!Where stories live. Discover now