3⃣9⃣

2.2K 260 53
                                    

Tea Party shi ne event na farko da muka farayi, shi ne ya kasance ranar Wednesday. Tun safe aka aiko min da outfit dina, Wata Kimolly gown ce ta wani rantsatsan Silver material, kasanshi black sequence ne. Ga komai accessories dina black. Ajewa nayi bayan na gama yabawa, a ranar akai min kunshina Yayi kyau Dan dawowata kenan na samu sakonshi. Karfen biyar na yamma muka tafi wajen make up wanda Yayi booking seda aka gama Allah Ya taimakeni period dina da safe yazo, Dama na dade ina wannan adduar yadda Bazan Je Ina missing sallah ba Har a kwashe albarkar auren ba.

Misalin Karfe Takwas yazo daukata, friends dina Wanda rabinsu duk Yan ABU ne sunsha English gown dinsu, Sunyi kyau sosae abinsu. Sun fitar Dani kunya. Yana tsaye a jingine jikin wata black Benz, yana sanye da Grey tuxedo suit, yayi kyau naji tamkar na rungumeshi na nunawa duniya yadda nake jinshi a zuciyata. Tunda muka hada ido yake min Murmushi, haka na samu Kaina da Murmushi Wanda nakejin tamkar bakina zai yage saboda Murna. Shi ya bude min kofar na shiga, anan idanuna ya sauka akan Mupheeyda wadda ta hakimce ta baje. Tayi kyau babu karya kuma outfit dinta sak irin nawa, just that nata Baki ne sequence din ash. Sau daya ta kalleni ta maida kanta Kan wayar da take dannawa, seda na zauna sannan ya rufe ni ya koma gaba ya zauna, Umar ke driving. A ka'ida Wanda ya shiga guri shike sallama, nayi bata amsa min ba balle mu gaisa hakan yasa kowacce ta ja mutuncinta har mukaje wani Chinese restaurant anan akai Tea Party din saboda reserving gurin akai gaba daya. Mun sha hotuna, duk Wanda yazo daukar mu se nayi dariya because I was so and super excited, inajin Kamar wannan auren shi ne mabudin dukkan Wasu alkhairin rayuwata, dukda idan na Kalli Mupheeyda zuciyata bugawa take amma Ban Bari hakan Yayi clouding zuciyata ba, abinda ya zama dole Meye naka na fighting dinshi tamkar kana fighting da will din Allah kenan.

Ana kammalawa muka fito, I had lots of fun, abokansa are entertainers, sun bamu dariya sun sani farin ciki sosae. A cikin mota yace

"Hik zanyi dropping Mupheeyda ta kwana gurinki kafin zuwa gobe mu wuce kaduna"

Kafin na bashi amsa tace

"No, na rigada nayi booking hotel room, I'm spending the night there "

Baice komai ba muka cigaba da tafiya, seda muka ajeta a hotel din sannan muka tafi, shike driving ina gefenshi yana nuna min yadda wannan satin yakeda muhimmanci cikin rayuwa, a wannan lokacin Yayi min alkawari Wanda inhar da komai ya tabbata bana tunanin zanyi kunci a rayuwata, but Allah is the best and the most perfect planner. A Wasu lokutan idan ya hukunta abu a kanmu mukanji tamkar inama ba haka abin yake ba, kanajin dama Haka akai, amma later on se ka fahimci there's reason and wisdom behind every will of Allah. Hakace ta faru dani.

Muna shiga gida naje na cire kayana nayi wanka sannan Nazo gaban window na tsaya, a hankali inajin yadda iska ke daddaga curtains din, Garin Yayi dadi ga damuna da bata gama sauka ba, inajin yan mata nata hayaniya kowa yana neman gurin da zai kwanta amma Ni tunani daya ke min yawo a raina, Friday Zaa daura min aure, ranar lahadi zan cika shekaru ashirin da uku a duniya, daidai shekaru ashirin da daya Dana aka sace ni kamar yadda Hamma Aiman yayi min bayani. I so long to see them, inason naji Yaya 'Ya'ya sukeji gameda iyayensu, ban rasa komai ba amma duk lokacinda nayi sujadda Se nayi adduar reunion dinmu dasu.

Nayi zurfi sosae cikin tunani naji hannu ya tabani lokacin ruwan Sama me karfi ya Fara sauka, feshin shi ya bata min fuska da kayan dake jikina. Mama ce hakan yasa na kirkiro Murmushi nace

"Mama"

Kallona Tayi tareda rungumeni tace

"Zanyi kewar ki diyata, Allah Yayi miki albarka"

"Amin "

Na amsa inajin idanuna suna cikowa da kwalla. Dakin Hamma Mus'ab mukaje babu kowa a ciki, gefenta ta zaunar dani ta Fara min karatun aure

HIKMAH Where stories live. Discover now