1⃣6⃣

2K 246 9
                                    


Kwanaki a hankali suke tafiya har Allah ya kawo ranar daurin auren Anty Fadila da Hamma Mussadiq, gaba daya gidan a cike yake Tun ranar alhamis har yau asabar abin yafi tsamari, ko ina ka gifta Yan Uwa ne da abokan Arziki kowa ka gani cikeda farin ciki yake.

Dama baa raba bikin ba dukkan dangi from both sides dukkansu gidanmu sukazo aka hade gaba daya dan Baffa yace hakan zaifi sauki. Kayana da aka kawo dazun daga gurin dinki saboda Yayi min yawa dole se an rage, wani lace ne me bala'in kyau, Yayi kyau har ya gaji ni da Mama ne tayi mana anko. Ina gamawa na fito bayan na bobbeye abinda ya dace. Ina fitowa Angwaye suna shigowa, tunda nake ban taba ganin Hamma Mussadiq Yayi irin wannan kyau din ba, Yayi kyau har ya gaji ga wata haiba da cikar zati da ta kara kamashi. Idanunshi a Kaina Inata Murmushi Kamar bakina zai yage. Alama yayi min akan nazo, kafada ta na make Ina girgiza Kai, turo baki yayi tareda nuna kanshi irin ni ko? Kaina na gyada alamar Eh, wata cousin dita Amira dake gefena taga Inata dariya tace

"Wai dariyar me kikeyi ne? "

Juyowa nayi nace

"Hmm! "

Matsawa nayi na nufi gurinsu dan tuntuni an fito da Anty Fadila se hotuna take, dukkansu Murmushi kawai suke me tsayawa a rai, Ina zuwa aka matsa min na shiga tsakaninsu tareda riko hannayensu akai mana hotuna, karkatowa Yayi saitin kunnena ya rada min

"Kinyi kyau Mashaaa Allah!"

Da sauri na saki hannunshi na kalla Anty Fadila wadda kwatakwata hankalinta baya kanmu Tana magana da kawarta ne. A Haka photo session ya Kare aka cigaba da biki.

Da yamma akaje Luncheon nanma munyi kyau sosae abinka da Fulani kusan dukkansu kowa fari ne, se kadan ne daga cikinmu Wanda skin dinmu Yayi duhu, munyi ankon Silver material mu sisters, friends dinta sun saka cream lace, iyaye kuma golden, ita dashi gaba dayansu fari suka saka all through. Luncheon yayi kyau babu karya, I enjoyed every minute of it.

Da wuri aka tashi saboda Kai Amerya dakinta, tunda aka tashi take kuka ta kama hannuna ta kankame Kamar ni zan hana a kaita, ni Kaina wani irin yanayi nakeji na fargabar rabuwa dukda bawai tayi nisa bane still a anguwan take, tazarar ba mai yawa bace sosae.

A dakin Mama muka shiga, kanwar Mama Anty Hadiza ta kalleni tace

"Hikma jeki ta shirya to"

Kokarin tafiya nake amma Anty Fadila ta damke hannuna haka babu yadda zaayi se hakura akai na zauna, kuma duk nasihar da ake mata da fada a gabana akai aka gama, hannunta cikin nawa aka kaita gurin Mamanta, Ummiey, Tana zaune cikin yan uwanta aka kaita tayi mata nasiha sosae sannan ta dubeni tareda yimin Murmushi tace

"To ko ke Zaa basu yar zaman daki? "

Dariya nayi nida mutanen gurin Wasu na fadin

"Wayaga shirme!"

Da haka muka Je gurin Mama wadda rungumeta kawai Tayi tace

"Allah Ya baki hakuri, Allah Ya Baku zaman lafiya"

Daga nan se Mota lokacin anata kiran Sallar ishai, a Haka mukaje, ina zaune a gefenta mutane se sambatun haduwar gidan suke, Dan babu karya gida yayi kyau an kuma Kawata shi da furniture masu kyau kana kallonsu kaga gidan yar gata. Haka mutane suka Fara bajewa seda ya rage Yan kadan Wanda zasu kara tsaftace gidan, suma suna gamawa na mike dan na bisu mu tafi amma fir Anty Fadila ta Hana, seda aka Kira Ango saboda wani irin kuka da take har seda ya karya min zuciya na Fara, yana daukar wayar yace a barni idan ya shigo zaisa a maidani, Haka suka tafi ya rage daga ni se ita, lullubinta ta yaye fuskarta ta bayyana wadda seda gabana ya fadi saboda yadda tayi wani irin pink tsabar kuka, gashi kwaliyya da akai mata ta luncheon bata wanke ba. Ai kwanciya nayi gefenta na dinga dariya ina nuna ta da yatsa, ai se ta kuma bata rai ba tareda tace min komai ba, seda nayi me isata kafin na janyo hannunta na kaita gaban rantsatsan dressing mirror dinta, Wanda ya kawatu da cosmetics iri iri, itama Tana ganin fuskarta se ta fashe da dariya Tana zaro ido.

"I'm sure idan Hamma ya ganki a Haka, koraki gurin Mama Zaiyi. "

Harara ta sakar min, sannan ta wuce toilet don wanko fuskar ta, Tana fitowa muka cigaba da zama muna taba hira nake ce mata

"Anty Fadila, Dan Allah kada Ki Bari ki zama koma baya wajen Hammana"

Harara ta tayi tareda hura hanci tace

"Auren Hadin? Shi da ba sona yake ba"

Tsaki na dan yi kadan nace

"Lallai ma, zaman da zakiyi kenan?"

Bata Kai ga bani amsa ba mukaji sallama a parlor, da sauri na dakko veil dinta na yafa mata har Kai sannan na gyara zaman nawa na fita parlon daidai shigowar Hamma Har seda mukai gware, nayi baya da sauri ina shafa goshi na tareda turo bakina nace

"Ka buge ni"

Murmushi yayi yana zare glasses din idanunshi Murmushi fal fuskarshi, Yayi kyau me sanyi Har ya gaji a cikin manyan kayanshi na farar dayyar shadda se sheki take Tana daukar ido.

"Hamma is apologizingl"

Ya fada yana hade hannayesnshi guri guda alamun ban hakuri yace

"Ina Addar taki? Kuzo"

Matsa mishi nayi don ya shiga ciki, ya gane manufata hakan yasa ya shige ciki, parlour na wuce muna gaisawa da friends dinsa harda cousins dinmu Wanda suke saani da Hamma, se tsokanata suke Wai kanwar Ango ta gaban goshi. Nidai sae Murmushi kawai nakeyi. Daki na koma seda suka gama barkwancin su da nasihohinsu sannan ya shigo yace

"Fito Zaa kaiki gida"

Immediately na mike na bi bayanshi, inajin sheshekar kukan Anty Fadila Hakanan naji zuciyata ta karye nasan ba karamar kewa zanyi ba.

Karfe Tara da Arbain tamkar rana haka gidan Yayi saboda Wasu irin guda dake tashi from every angle na gidan, Aminu ne dalilin gudar don tunda aka daura aure bai shigo ba se wannan lokacin. Banda Murmushi babu abinda ke tashi daga kyakywar farar fuskarshi, yanata gaisawa da mutane ana tayi mishi Allah Ya sanya alkhairi, straight parlon Alhajin shi ya nufa, yana zaune shi daya yana kallon tashar CNN, yana jin sallamar Aminu Ya dago within a blink of an eye Ya kare mishi kallo, Sanye yake da Wagambari yar ciki da wando coffee se babbar rigar milk, hular kanshi Zanna Bukar ce wadda mafi yawan zaren da akai amfani dashi milk ne, agogon hannunshi na kamfanin Invicta yayi masa das se kyallin angonci yake. Zama yayi fuskarshi da wannan kayataccen Murmushi na tunda akai zancen kome yake yi.

"Yaushe zaku tafi kaida hafsa?"

Kanshi Ya Sosa yace

"Eleven pm ne flight time din namu"

Kai Alhaji Ya gyada yace

"Allah Ya bada zaman lafiya se a kara kula a kuma kiyaye"

"Inshaaa Allah Alhaji"

Addua doguwa Alhaji yaja sannan ya sallami Aminu daga nan Straight dakin Dada ya nufa yasan nan kadai zai iske Hafsa, ile kuwa tana can kurya ta gama cakarewa cikin wata tattausar Lafaya me kyau Tasha sequence a jiki matsayin adon lafayar, tamkar an mata barin turare saboda yadda take kamshi. Yana shigowa aka soma sowa, bai bi takan kowa ba don lokacin tashinsu ya kusa, don Haka hannunta kawai ya kamo hakan yasa ta dago fuskarta pleadingly, yana jin Dada na gyara murya ammma haka ya janye Hafsa Salima se iskanci take mishi.

Karfe goma da ashirin suka isa airport ana gama screening suka shiga jirgi kuma har lokacin daidai da single word bai fita a bakinsu ba sede kana kallonsu kaga Wanda feelings da soyayya me azabtarwa ke dawainiya da junansu, amma yatsa sun kasa kaiwa junansu, kowanne zuciyarshi banda bugawa babu abinda takeyi. A Abuja wani friend dinshi yazo Ya daukesu yana ta tsokanarsu se Aminu ke mayarwa Haka Har suka isa Gwarimfa inda anan sabon gidan Aminu yake. Tundaga gate zakasan gidan ba karamin Haduwa Yayi ba, ko ina bulbs sun haska tamkar gidan rawa, suna parking Aminu Ya riko hannun Hafsa wadda yasa dukkansu jin wani effect na radiating jikinsu.............

_Tired_

_Jakadiyar kainuwa_

HIKMAH Where stories live. Discover now