6⃣

2.5K 295 11
                                    

_I've seen all your comments and votes on wattpad... It's always thank you. Nasan Hikma Ya tado tsohon ciwo, as I can see comments na mutane that went through the pain of infertility. I'm sorry Allah Yana tare daku, he'll ease all of your pains_

*The first six chapters of HIKMAH are dedicated to every infertile family... You will have your baby sooner or later Inshaaa Allah*

"Zamui referring dinku Teaching hospital na gwagwalada"

Doctor Ya fada lokacinda yazo duba babyn Hafsa, kallonshi Hafsa tayi tareda kallon babyn sannan tace

"Amma babanta yace kace zaayi discharging dinmu ne, Naga ta samu sauki referral na Meye Kuma?"

Kanshi Ya girgiza sannan yace

"Eh sallamarku Zamui amma Kinsan zaku dinga zuwa follow up ko? babanta yace dani a Abuja kuke, so is better Ku cigaba acan than ace zaku dawo nan"

Ajiyar zuciya Hafsa ta saki tayi Murmushi tana kallon halittar dake hannunta, da gaske bata taba kawo yarinyar zata murmure har Haka ba, kullum gani take yarinyar zata mutu kafin Washegari amma rai hannun Allah yake.

"Mun gode sosae, kuma Inshaaa Allah Zaa dinga zuwa follow up din"

Kanshi Ya gyada sannan yace

"Kinsan yarinyar preterm ce, akwai organs dinta da are not well developed, to akwai abu da ake kira kangaroo mother care KMC, shi Zaa dinga mata"

Cikin rashin fahimta Hafsa tace

" Bangane ba"

Tsayuwar shi ya gyara yace

"Kinsan kangaroo nada pouch jikinta Wanda take zura danta ko? "

Kai Hafsa ta kada, ya cigaba

"zaki cire rigarki, ki daura babyn bayan kin cire kayanta a kirjinki, ki daure da zani, dumin jikinki zai dinga regulating nata body temperature, sannan breastfeeding is also essential "

Kai ta gyada cikin fahimta, tayi mishi godiya sannan ya fita, yana fita Miss A'isha ta shigo Don hada kayan, Hafsa na zaune ita kuma Miss A'isha ta kammalla ganin Hafsa batada niyyar tashi yasa tace

"Tashi mu tafi mana, kina bata min lokaci yau nake son tafiya"

Dagowa Hafsa tayi tace

"Haba Mom, tafiya zakiyi ki Kara barina? "

Sakaka Miss A'isha ta kalleta sannan Tayi tsaki tareda karbar babyn ta rufeta cikin Farin shawl me baza red a jiki, ganin zata fita yasa Hafsa riko hannunta tace

"Mom me yasa kuke Haka keda Alhaji? Idanunku na nuna abinda kukeso amma kunki, Haba Mom rekindle your love mana.... "

Zancenta ya katse saboda shigowar Alhajin, kallon hafsan kawai yake Se kuma ya Kalli Miss A'isha kafin yace

"Hafsa haka kikeso? "

Da sauri ta gyada kanta batareda ta furta komai ba saboda wani irin excitement da ya lullube ta, kallonshi Miss A'isha tayi tace

"Ina fatan ba fada mata Kake zaka maida ni ba, Abbas ka manta nace Bazan kara komawa gidanka ba? "

Murmushi Alhaji Yayi yayinda jikin Hafsa ya Fara rawa yace

"Eh kin fada A'isha, amma inasan kisan ni dake we're match made in heaven, har yau shekaru ashirin da biyar kin kasa aure, kinga you're telling Abbas is only you I want. Badan ke zanyi ba sedan farin cikin Hafsa. "

Daga Haka ya fice, Miss A'isha ilahirin gabobinta Sunyi sanyi, Hakanan tayi Shiru Ta rasa me takeji, Hafsa ce ta dafa ta Murmushi saman fuskarta tace

HIKMAH Where stories live. Discover now