"Kinsan gidan Hajiya Talatu? "

Kaina na gyada, matar kawar Mama ce anan bayan layinmu suke, ledar ta bani tace

"Ki kai mata"

Amsa nayi cikeda jin dadi zan fita in samu kai sakon Mama, seda nasa hijab ta rakoni har bakin parlor Tana min kashedi akan kada na tsaya Ko ina, tasan da gagan take don matar nada sa'ata Indai naje bana dawowa da wuri, shiyasa bata son aikena se su Hamma.

Gidan na Fara zuwa, bayan na gaisheta na bata sakon sannan na taho tunda Fannah  din basu nan, straight gidansu Abdallah naje ,Kamar kullum nayi knocking maimakon Baba buzu se wani matashin saurayi fari, kyakyawa kyau me sunan kyau, babu tantama shidin ya hada iri da buzaye Don lebenshi pink ne, gashin kanshi a kannanade yake, kina kallon fatarshi kinga ajebutter Dan gayu dashi.

Bansan Inata kallonshi ba seda ya saka hannunshi Yayi waving akan fuskata sannan na dauke idona da sauri inajin yadda jikina ke kyarma, ba wani Babba bane Dan bazai wuce saan Mus'ab ba ko ya girmeshi da shekara daya, tsayuwarshi ya gyara yace

"Se kallona kike ,kin sanni ne?"

Da sauri na girgiza mishi Kaina, cikeda in Ina nace

"Da...da.. ma gurin... Ab....dallah aka aiko ni"

Girarshi ya dage min yace

"Kece Zainab? "

Da sauri na gyada Kaina, Se Naga yayi Murmushi Harda tafa hannunshi sannan yace

"Kece kike kawo letters kina sona Ko? Kece Ko?"

Ya fada yana nufo inda nake, da sauri na shiga ja da baya idanuna a warwaje nace

"wallahi aiko ni akeyi"

Ya wani bata rai yace

"Ina wadda ta aiko ki din?"

Kaina na girgiza amma bai barni nayi magana ba yace

"Se na kaiki Har gida na fadawa Mamanki abinda kike"

Jin Haka yasa na fara kuka ina rokonshi amma mutuminnan Kamar zuga shi nake haka ya tiso keyata har kofar gidanmu, zuciyata Kamar zata fito tsabar yadda take bugawa, hawaye kuwa dama wannan ai a kusa yake, Se fita yake Kamar lalataccen famfo, muna isa na jiyo Ina kuka sosae nace

"wallahi bani nake turo maka ba, Nima aikoni kawai takeyi, kayi hakuri Mama dukana zatayi"

Kanshi Ya gyada tareda nuna ni da yatsan shi yace

"Next time kika kara Se na zaneki sannan na kawo ki har gida kinji?"

Da sauri na gyada Kaina sannan na shige gida da sauri ina goge hawayen fuskata sannan na karasa, straight fridge naje na sha ruwa sannan na wanke fuskata a sink kafin na sanar da Mama na dawo. Dakina na wuce na dakko letter na buda Ina karantawa, gaba daya content din Ya girmi kwakwalwar Kaina, ninke wa nayi Inata yiwa Kaina Murnar Mama bata samu labari ba, sannan ina tunanin yadda zamu kwashe da Anty Fadila idan ta dawo.

Se da aka idar da Sallar Maghrib sannan suka dawo, lokacin muna tareda Mama Ina bata labari mukaji sallamarsu, da murna na Mike amma ganin mood dinsu yasa na koma na zauna babu shiri, suna cewa Mama sun dawo Duka sukai daki nasan sallah zasui, Nima assignment dina Na islamiyya na dakko ina fitarda Tajwid din dake suratul Anfal. Har akai Sallar ishai mukai sallah Anty Fadila bata fito ba, duk babu dadi hakan yasa nace

"Mama Bari naje Naga me Anty Fadila takeyi"

Kanta ta gyada min saboda lazumi da takeyi, dakin na wuce na tura kofar na shiga bakina dauke da sallama, gaba daya dakin a hargitse yake, duk ta fito da kayan ta daga wardrobe Tana zubawa cikin trolleys dinta, dake tayi kusan wata uku a gidanmu, da sauri na karasa Ina fadin

"Anty Fadila Meye kike hada kaya"

Sautin kukanta kawai naji hakan yasa na karasa jikina a sanyaye na riko hannunta ina fadin

"Menene Wai? "

Hannunta ta karbe daga nawa batareda ta kulani ba ta cigaba da abinda take kuma Se kuka take, na dade a tsaye har ta gama sannan tayi zipping dukkansu kuma bata daina kukan ba

"Bari naje na fadawa Mama tunda bazaki daina kukan ba"

Na fada Ina nufar kofa, ji nayi ta ture ni sannan tayi locking kofar tana harara ta, hawaye na zuba, abin se ya bani dariya har nayi Murmushi, hannuna taja muka zauna Kan gado tace

"Hikmah Wai Hamma Mussadiq zan aura kuma nan da wata daya"

Ai mikewa nayi na buga tsalle ina fadin

"Shi ne kike kuka? Yeeeee ni ta koina, Ango Hammana, Amarya Addata. "

Duka ta sakar min a bayana tace

"Bakida hankali, Yanzun da muka fita cewa Yayi Wai Baya sona fa Hikmah"

Se naji Banji dadi ba hakan yasa nace

"Ki rabu dashi, wasa yake miki Gaki kyakyawa waye zaice baya son ki"

Tana son a koda ta Aikuwa taji dadi, da wasa da dariya nasa ta maida dukkan kayan wardrobe, muka bude ledar da suka shigo da ita, Burger ce guda uku, Se kaza gasashiya guda biyu, yoghurt da juice masu sanyi. Abin nema Ya samu zama na gyara na dauki burger daya na kai bakina, lumshe ido nayi saboda dadi daya dakeni, Duka Anty Fadila ta kaimin Tana fadin

"Dadina dake baki ganin Abinci kiyi wasa dashi"

Dariya nayi nace

"Food is life ai!"

Karkashin pillow ta daga ta dakko Tawa ta sameni Wanda take karanta mana nida ita, a zuwanta novels din Hausa da muka karanta bazasu kirgu ba, ita a gidansu ita kadai ce shiyasa take abinda take so, ni kuwa nasan duk ranar da Mama ta ganni to kashi na ya bushe.

Munata Karatu ina buga tsalle idan akai wani show din dake a part 3 muke, ga kaza Inata ci Ina korawa da juice Ashe mun manta bamu rufe kofa ba, Mama taji Shiru Ta biyo mu, tsabar yadda muka zama engrossed Ko sallamar da tayi bamu jiba se jinta kawai mukai tana fadin

"Me kuke karantawa? "

AI tsabar tsoratar da nayi se na Fara tari, Mama tayo Kaina anan Anty Fadila ta boye littafin, A'a abu Kamar wasa se na Fara numfashi samasama, ina janshi da kyar, Mama a rude tace da Anty Fadila

"Jeki dakko ruwa"

A guje ta fita se Gata ta dawo da ruwan roba, da kyar nasha ruwan amma bai lafa ba, hakan yasa Mama tace

"Jeki ki kira min Musaddiq muje asibiti"

Hijab ta dauka tayi waje, Haka ta saka min Hijab Nima ta kamo hannuna hankalinta duk a tashe, Hatta Hamma da yazo seda ya tsorata, a gaggauce muka shiga Mota, zamu fita gate motar Baffa zata shigo, lekowa Yayi yana fadin

"Lafiya? "

Kafin a bashi amsa yace

"Subhanallah! Me ya samu Uwata?"

Mama ce tayi briefing dinshi, Mota ya koma Se asibiti, A emergency aka karbe ni,  allurai akamin a hankali se numfashi Ya fara daidaita Nima na dawo daidai.

File aka bude min sannan doctor Ya karbi history daga wajen Mama anan take fada mishi yadda nake mura kullum kullum, daga baya ya gama rubuce rubucenshi yace da Baffa ai Asthma ce dani, amma zamu dawo ayi gwajegwaje Don a tabbatar da komai.

Haka muka dawo gida da tulin magunguna da dokoki, Tundaga ranar Mama ta Kara kaffakaffa Dani, Munje Munyi test aka tabbatar ita ce kuwa.

Jakadiyar kainuwa

HIKMAH Where stories live. Discover now