2⃣

3.2K 320 7
                                    

                      💕HIKMAH💕
                               2⃣

✍️SHATUUU♥️

🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION

💖Shatuuu095@wattpad

Kwanan su Aminu da Hafsa biyu cikin Garin na Germany, babu inda suke zuwa banda daki, shi ne ma Ya fita Nemo musu sabon SIM saboda suyi communicating da gida, yana siyowa ya dawo inda suka cigaba da kashe junansu da soyayya, they're very romantic couples Wanda da ace hakan shi ke kawo haihuwa bana tunanin zasui shekara bakwai da aure ba tareda sun haihu ba, amma Allah shi ne Allah! Shi yake tsara mana yadda rayuwarmu zata kasance shiyasa ya jarabce su da hakan.

Alarm din dake gefen gadon nasu ne ya Fara bugawa saboda setting dinshi da akai Ya buga a kowacce sallah don idan zasu biyewa timing lallai bazasu yi sallah ba. Hafsa ce ta Fara yunkurawa ta mike tareda fadawa toilet Don daura alwala, seda ta kammalla sannan Aminu Ya shiga yana fitowa Ya jasu sukai sallah sannan suka koma.

Karfe takwas suka kammalla duk wani shirinsu don wannan ce ranar appointment dinsu da Doctor da zai musu aiki. Seda sukaci Abinci kafin suka biyo lift suka sauka kasa, Asibitin baifi 10 meters bane daga hotel din, hakan yasa suka wuce da kafarsu suna ta hira wadda duk yawanci Aminu keyi akan Babynsu ita kuma tana dariya don duk yadda take zumudin babyn Aminu yace bani guri don kullum zancen yake.

Cikin nutsuwa Baturen doctor Ya gama duba file dinsu, lokacin ya dago idanunshi Ya sauke Kan Hafsa da Aminu da suka tsira mishi ido, cikin turanci dinsu Ya Fara musu bayanin yadda procedure yake

"It's my pleasure having you here, na duba file dinku bayan test da kukai running Ya nuna mana male partner yanada low sperm count, while female partner lafiya take, gashi Kunyi signing Kun yadda da aikin Ko? "

Aminu Ya dubi Hafsa sannan yace

"Yes! Mun yadda amma baayi briefing dinmu yadda procedure din take ba, chances na nasara, failure da adverse effects dinta"

Kai Doctor din Ya gyada tareda sake gyara zama yace

"Intrauterine Artificial Insemination, procedure ce da ake yi don addressing Infertility, Yanzun Zaa duba lokacinda ya dace ayi aikin, lokacinda mahaifar ki zata fi karbar ciki, zaka bamu Sperm sample dinka Wanda Zaa saka a mahaifar ta, akwai chances me karfi na nasara, side effects very few ne, kuma ido biyu akeyi"

Wata sassanyan Ajiyar zuciya Hafsa ta saki Don duk tunaninta yanka ta zaayi ayi aikin, hannun Aminu ta sake damkewa cikin nata hakan yasa ya gyada mata Kai alamun karfin gwiwa, basu fito daga office din Doctor ba seda sukai clearing dukkan doubts dinsu kafin akaje inda Hafsa ta kara running Wasu test, kwanaki goma Ya basu da magunguna na Fertility suka koma masaukinsu.

Bayan Sallar ishai suka fita waje Don shan coffee Dan dukkansu biyu addict ne, da wuya kaga daya na son Abu daya baya so, perfect couples ne Wanda suka fahimci kansu sosae, a zamansu Hafsa zata iya irga sau nawa sukai fada, dukkansu free minds ne dasu shiyasa ko sun samu matsala there and then kowa zai fadi abinda ke ranshi. Matsalarsu daya wannan rashin haihuwar itama sune suka damu don kuwa kullum suka shiga dangi kasamcewarsu dangi daya yasa duk inda suka shiga Baki ake basu kada su damu haihuwa lokaci ne. Shekarar da ta gabata Baban Aminu Yayi suggesting suje Germany tunda anan an rasa daga Ina matsalar take, suna zuwa akai komai anan aka gano daga Aminu take, nan hankalinshi Yayi masifar tashi dukda Hafsa na nuna mishi itafa matsawar zata zauna dashi to haihuwa ba komai bace, bayan sun dawo Baban Aminu yace lallai Se an raba auren Dan kada a cuci Hafsa, Anga Tashin hankali marar misaltuwa kada ma Hafsa taji labari. Wannan yasa Baban Hafsa matsayinshi na Babba yace a kyalesu tunda sunji sun gani sun amince. Haka rayuwar ta cigaba har Aminu yace suje suyi Insemination dinnan, babu Wanda suka shawarta Haka suka taho abinsu saboda sunsan family dinsu babu Wanda zai yadda da hakan. Hakan yasa sukai yin kansu saboda suna ganin shi ne kadai mafita a tare dasu.

HIKMAH Where stories live. Discover now