||||||||

852 36 6
                                    

Assalamu alaikum fatan na same ku lafiya. Ina me bawa mabiya littafin nan haquri sakamakon dadewan da nayi banyi posting ba. Ayi mun afuwa abubuwa ne suka dan min yawa. Amma yanzu na dawo in sha Allah.



"Wai Bashir me kake nufi dani ne?" Ta tambaye shi hade da shan kunu kamar ba ita tayi maganar ba. Tayi tayi ta danne zuciyar ta amma sam ta kasa.

"Me kika ce?" Ya dago ya kalle ta gami da rufe laptop dinsa.

"Ba magana nake ba." Ta fada tana gatsina fuska. Tsabar ya raina mata hankali sai bayan ta gama magana sannan zai ce wani me tace.

Tasowa yayi a hankali ya qaraso inda take zaune.

"Haba wifey, me yayi zafi? Umm?" Ya fada a cikin yaudararriya muryar sa. Nan take bata san sanda murmushi ya kwace mata ba.

"A dena fushi dani dan Allah." Ya kafe ta da idonshi masu chanja mata lissafi.

"To ba kaine ba?" Ta turo baki wai ita a lallai fushi take dashi.

"Ai na bayar da haquri koh?" Ya jawota jikinsa. Sun danyi shiru kenan sai wayarsa ta fara qara yace ta miqo masa. Tashi tayi ta ciro ta daga charge. Kamar kar ta kalli screen din sai kuma wata zuciyar ta zuga ta. Tana kalla kuwa gaba daya ta rasa nutsuwarta.

My love??

Yana da wata ne bayan ita? Ita kam tana bala'in kishinsa. Kwanakin baya da kanshi yace mata ya dena kula yan mata. Toh wannan kuma fa?

Numfashi taja kadan ta miqa masa wayar da kyar. Kallon screen din yayi sannan ya kalli fuskarta kafin ya dan yi tsaki.

"Dare yayi koh? Yanzu lokacin matata ne ba aiki ba. Uhm?" Gaba daya a zaton shi bata ga wa ya kira bane shiyasa yake neman ya mata wayo.

"Hmm" kawai tace tare da barin wajen. Dan text ya tura ya kashe wayar ya biyo ta.

Ko da ya taho hanya yaga ta tsaya suna magana da yaran sai kawai shima ya shiga cikinsu ake hirar dashi.

"Abbu," Maryam ta kira sunan shi.

"Mero ta."

"Wai a islamiyya naji ance..." Tun kafin ta qarasa Sa'adatu jikinta ya bata abunda Maryam ke shirin fada ba abu ne mai dadin ji ba.

"Maryam, ku tashi ku tafi dakin ku." Ta basu umarni. Babu musu duk suka miqe suka basu waje. Maida kallonta tayi zuwa Bashir kafin ita ma ta bar wajen.

Tana zuwa daki, ta shirya ta kwanta. Bayan mintuna kadan sai gashi yashigo jiki babu qarfi. Da alama ya fahimci cewa ta ga wadda take kiransa.

"Wallahi ba auren ta zanyi ba." Ya zauna a bakin gado. Luf tayi kamar barci takeyi.

"Kawai dai..."

"Bana son ji." Ta gaya masa muryarta a daqile.

Nima haka kayi mun. Ta fada a cikin ranta.

"Ki tashi muyi magana saboda ba zan so in tashi babu rai ba gobe kar ki sake..." Sosa qeya yayi ba tare da ya qarasa maganar tashi ba.

"Me yasa baka kwa..." Sai kuma tayi shiru. Ji take kamar tayi shiririta idan ta tambaye shi.

"Datuu, akwai kunya tsakanina dake ne?" Ta girgiza kai.

"Inajin akwai matsala fa. A duk sanda na shigo dakin nan sai naji gaba daya na tsani komai kawai ina daurewa ne na miki magana." Zaro idanunta tayi tana mamaki.

Kar de ace...?

Ba haka bane ba ma. Ta fada a ranta ashe a fili ta fada.

"Ba haka bane me?" Ya gyara zaman sa.

"Bakomai." Ta jawo bargo ta rufe fuskarta.

"Sai da safe. Gobe zan koma." Dage kafadarsa yayi cikin halin ke kika sani gami da fucewa. Yana fita ta zauna zumbur tana riqe qirjinta.

Kar dai ace sakamakon abunda ta aikata a dare daya ne yake bibiyar ta.

Wayyo Allah dole taje ta samu Naja'atu qawarta gobe suyi magana.

****

Ko da safiya tayi ta tashi da niyyar kimtsa yara domin su tafi makaranta sai ta tarar har sun shirya.

Murmushin jindadi tayi tana qara jin son yaranta.

"Ina Ummi?" Ta tambaya da yake ita kadai ce bata gani ba.

"Ta tafi wai Abbu ne zai shirya ta. Mummy yau fa kin makara kuma idon ki yayi ja." Bata ce komai ba ta nufi sashen Bashir din. Ta tarar yana bawa Ummi shayi a baki.

"Sai a zo a tafi ko?" Ta jawo Ummin.

"I will like to talk to you in kin dawo." Ta gyada masa kai gami da ficewa.

Sanda ta dawo ta tarar dashi still a kwance yana hutawa.

"Gani." Ta fada tana neman wajen zama. Kamo hannun ta yayi yana shafawa a hankali kafin yayi magana.

"Wannan karan ba zan tafi haka kawai na sai kin gaya mun me yake faruwa." Numfashi taja hade da lumshe idonta. Haushin ta daya. Wai sai ya dinga yi kamar shi baiyi komai ba.

Sake janyota yayi ya dora habarshi akan kafadarta. "Ina jinki." Ya rada mata a kunne.

Hawaye ne ya taru a idonta sanin cewa da zarar ta furta komai toh yau ce ranar zaman ta na qarshe a gidan Bashir.

"Bashir don Allah kar ka guje ni. Kuma dan Allah kayi mun alqawarin zaka yafe mun." Yanzun kam hawaye ne yake zubowa ba qaqqautawa. Gara kawai ta gaya mishi duk abunda zai faru ya faru.

A yi ta ta qare.

"Bashir kafin muyi aure..."

"Mummy!" Ummi ta banko kofa. Nan da nan yayi saurin matsawa daga jikin Sa'adatu. Suka mayar da hanakalinsu kan yarinyar. Duk a tunanin su sun tafi school.

Ficewar da tayi yasa Bashir bugan kujera. Yasan cewa ya rasa wannan damar ta yau.

*****

Zan fara sabon littafi me suna ALQARYARMU sai kui adding dinshi. Na saka introduction din. Ku duba profile dina. Nagode

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Nov 12, 2019 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

Dare daya.Where stories live. Discover now