|||

615 38 3
                                    

"Idan an tashi daga makaranta, tudun Yola zaka kai su duk." Sa'adatu ta fadawa direban yara kafin itama ta bude motar ta ta shige. Yaran ne suka daga mata hannu, murmushi ta yi musu yayin da Kawu direba ya ja motar suka fice makaranta.

A shekarun baya babu ahunda yake birge Sa'adatu illa ta ganta a cikin hadadden gida masu ayki suna mata hidima sannan kuma duk sanda tazo fita ya zama sai kalar motar da take so zata hau. Yau gashi an wayi gari duk burinka ta sun zama gaskiya amma babu kwanciyar hankali a tattare da ita. Ashe kenan kudi ba ya siyan farin ciki da kwanciyar hankali amma ba kowa ne zai gane hakan ba.

Idan anyi sa'a da dace, sai kudin da dukiyar su zama ababen qarawa rayuwa jindadi amma idan hankalin ba'a kwance yake ba duk sai su tashi a banza. Numfashi ta ja kafin ita ma ta fara tuqi zuwa boutique din ta inda take dan zama saboda ta rage zaman kadaici.

Tuqi take yi duk ranta a jagule da tunani a haka dai har ta isa shagon ta tarar har Veronica ta bude shagon tana dan kade kade. Murmushi tayi ta qarasa ciki.

"Ina kwana Madam." Veronica ta russuna ta gayshe ta.

"Lafiya lau. Nica, kin tashi lafiya?" Neman wajen zama tayi ta zauna.

"Dama kullum kullum Dior watches ne ace akwai." Veronica ta fada tana murmushi wai ita tayi qoqarin yin Hausa. Ba a Kano aka haifeta ba amma dai ta kwashe kusan shekara goma sha a Kano duk da haka bata iya Hausa ba. Ko me kace mata zata ji amma ita fa baza ka gane nata ba sai dai idan irin kun saba hira sosai.

"Malama idan zakiyi Hausa daidai kiyi ni ban fahimci abunda kike fada ba." Sa'adatun ta fada tana zagaya shagon. Sarai ta gane abun da Veronica tace amma sai ta wayance.

"Ah I mean people dey ask for Dior watches everyday kuma e don finish long time." Ta sosa keya. Dariya Sa'adatun tayi kafin tace

"Ni ba cewa nayi ki min broken English ba, Hausa zakiyi hajiyata." Sa'adatun ta fada cikin sigar tsokana. A haka dai suka zauna suna hira sama sama har rana ta fito.

"Madam, zan iya fada miki wani sirrina? Ki taimaka mun?" Veronica ta fada cikin broken English. Gyara zama Sa'adatu tayi ta gyada mata kai alamun tana sauraron ta.

*Labarin Veronica*

Wata mata ce wadda baza ta wuce shekara arba'in ba zaune akan kujerar katako. Wata yar T-shirt ce a jikin ta wacce ta sha rana ta dafe. Zanin jikinta ne a daure har kan kirjinta said kuma wata yar hula a kanta. Hannun ta sanye yake da irin abun hannun nan da akeyi na jera duwatsu. Dayan kuma mirjanin roba ne. Sai sharbar gumi takeyi kasancewar ranar ana zafi sosai ga kuma hawaqin da yake fita saga murhu duk ya shige mata hanci har tari take yi. Ganin zafin baya raguwa ne ya saka ta rufe qatuwar lemar ta ta ajiye a gefe.

Masara take gasawa, a gefe kuma qatuwar tukunya ce wacce take dafa masarar sai kuma wani bokiti da yake a gefen ta an qulla gasarar koko a ciki.

Gefenta wani mai dankali da doya ne shima ya kasa su kashi kashi yana jira Allah Ya kawo me siya. Dayan bangeren kuma wata 'yan mata ce take saida abinci. Wajen ta baya rasa mutane to ta hakane idan Madam tayi sa'a sai ita ma a siya masarar ta.

Madam Adesuwa mace mai zuciyar nema. Tunda mijin ta Abdulwali ya rasu ya bar ta da yara hudu, tana iya qoqarin ta taga ba'a kwana da yunwa ba a gidan ta. Mijin ta bayerabe ne amma musulmi. Kasancewar musulunci ya ba wa maza damar auren kirista yasa Abdulwali ya auri Adesuwa wacce aka fi sani da Blessing. Sunan yarabancin ta ne Adesuwa.

Mahaifanta yan asalin Kwara ne, zama ya kawo su Kaduna inda Adesuwa ta hadu da Abdulwali. Basu sha wata wahala ba saboda yaren su daya aka daura musu aure. Bayan shekara goma sha biyu da aure Abdulwali yayi hatsari a hanyar zuwa Lagos yace ga garin ku nan.

Dare daya.Tahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon