Chapter 39

4.1K 199 3
                                    

🕯🕯🕯
    *MATATACE*
          🕯🕯🕯
  

🇳🇬®
*_ABORIGINAL WRITER'S ASSOCIATION📚✍️._*
[❄Dance above the surface of the world,let your thoughts lift you into creativity that is not hampered by opinion.]

story&written by
Haleematu💕meemartjj💕
wattpad@Meemartjj 

*Dedicated to swt sisters*
_Aunty Jamee, aunty ummeetah, and my fa'ixation._

   *_wanga pages kyauta ne ga dukkan masoyan littafim matatace, a duk inda suke ina musi fatan alkhairi._*

wadanga writers kuna raina

_my janaf_
_Hafnan_
_sis Nerja'art_
_lashminzy_
_miss xerks_
_mhizzphydo_

  *_kai da sauran suma baki daya, musamman writters na kungiyar aboriginal writers, ina muku addu'a Allah ya taimake ku, ya kara basira, fikra da fasaha, much fatan alkhairi, yours meemartjj._*

page 77~78

__________Gaba daya wajen sai da kowa ya juyo da kallonshi kan Suhymah dake zaune zufa na faman kyato mata, dai dai sanda Irfan ya tsaya cak da scissors din dake hannunshi kan dogon pink ribbon din da aka daura tsakanin classrooms din.

  Ummeetah dake bayanshi tayi saurin janye hannun nashi daga jikin al-makashin, wanda yayi sanadiyar faduwan scissors din bisa ribbon din.

  wal, wani hasken shocking ya haska tare da bada sauti bisa igiyan, har zuwa jikin wani electric connection da akayi, a firgice duk wanda ke wajen ya fiddo ido, ummeetah ta kuma jan Irfan baya tana kankameshi a jikinta cike da firgici.

  Suhymah dake zaunen can tana kallon komai ta sauke wani ajiyar zuciya, yayin da aka shiga kallon kallon abin mamaki, da mamaki Abba ya kalleshi yana fadin,,

  "Sadeeq meke faruwa ne?" da sauri yabar wajen shida wasu mutanenshi yana fadin,,

  "Abba bari na duba", dai dai sanda su mummy suka kariso wajen harda suhyma, haj. falmata ta fisgeshi daga jikin ummeetah tana tattabashi, kafun ta dago kai a matukar firgice take kallon Ummeetah da fadin,,

  "me kika mishi ne, nace me kika shirya ma jika nane, duk abubbuwan da kika gama kwace mata bai ishe kiba, sai kin hada da kashe mata yaro kwaya daya tall, me kika nufi dashi neeeeeee?" a firgice Ummeetah ta fiddo idanu tana girgixa kanta da hawaye, tama kasa magana, Abba zai magana aunty mashkura ta riga da fadin,,

  "ban fahimta ba hajiya, ta yaya zaki rika mata wadannan tambayoyin, me Ummeetah ta sani?", haj. falmata dake rungume da Irfan a rude take da abin daya faru take fadin,,

  "dom me baxan tambayeta ba, na farko tace sai dashi zata yanka ribbon din nan, na biyu an tasashi a gaba, gaba daya wannan maci amanar yarinyan ta gama wargaxa mata farin cikin gidanta", kowa ya gama tukewa da mamaki, cike da daurewan kai aunty mashkura ke nuna Suhymah dake tsaye gefe tana risgar kuka da fadin,,

  "a'ah, waishin donme ba zaki tuhume yarinyan kiba, ita da tace karya yanka ribbon din?", zatai magana Abba yace,,

  "kunga ku dakata don Allah, komai zai warware, abi komai a sannu", buden bakin haj. falmata sai cewa tayi,,

  "babu abin da za abi a sannu Alh. Ameenu", sai kuma ta sanya kukanta da gaskenta tana matsar kwalla da gefen gyalle, tare da nuna Ummeetah da hannu take fadin,, 

  "wlhy ke wannan diya Allah baxai barki ba, kin aure mata miji sannan kin mallakeshi, yanxun kuma bansan me kike nufi da danta kwaya daya tal daya rage mata a duniya ba", sai lokaci Suhymah ta dago kanta da fadin,,

  "a'ah mummy kar kice haka", a tsawace take fadin,,

  "toh in bance haka ba mezan ce, itace sillar faruwan komai, kina zaune da mijin kie lafiya, bansan me taxo dashi ba, harta da dukiyar ya mallaka mata gabda daya, komai ya lalace, Allah ya isa tsakininki da kishiy……..."

MATATACEWhere stories live. Discover now