Chapter 02

5.3K 251 2
                                    

🕯🕯🕯
            _*MATATACE*_
     🕯🕯🕯

     

story&written by Haleematu💕meemartjj💕
wattpad@meemartjj

🦚🦚🦚 *UNIQUE ONLINE WRITER'S FORUM*🦚🦚🦚

   *Dedicated to lovely sisters*
_Jameela ja'afar yakubu_
_Fateema ja'afar yakubu_
_Fa'iza ja'afar yakubu_

*_page 3&4_*

――――Da sauri ta sakko daga kan gadon, ta nufi downstairs, kitchen tayi, motsin data jine, ya bata tabbacin Ruma ta cika umurnin data bata, na taxo da wuri, don akwai a'ikin da zata mata, ta shiga kitchen din tana karisawa wajen Ruma dake tsaye wajan gas cooker, da fadin,

  Ruma har ashe kinxo, ta juyo tana fadin,,,

  yes madam, na dan juma da zuwa, ummeetah ta fada mun baki riga kin tashi ba, ta yamutsa fuska da yer hamma take fadin,,,

  ummm, today i have a deep sleep, sai yanxun na tashi, hope kin taho mun da cake din, Ruma na murmushi ta nufi wajan wani dan corridor, tare da dauko wani katon white leda, da sauri suhymah ta kariso suna bude cake din, dake cikin kwali har biyu, fondat da butter icing, ta rika blushing ganin yanda cake din su kayi kyau, tana fadin,,,

  ouk plss ki ije mun a wajanki, in kika tashi tafiya sai in amsa, yanxun inaso zan futa ne, Ruma tace,,,

  ouk shikenan, tana maida cake din cikin ledan, lokacin da suhymah tayi hanyar futo so busy, harta kai bakin kofa ta tsaya tana jiyowa da fadin,,,

   kin dai san gaba daya snacks, da girke girken dana ce miki ina so?ta daga kai tana fadin,,,

  yes, already na fara ma, suhymah tace,,,

  good, karki bar yer a'ikin can haka, idan akwai abin da zata miki, ki tabbatar kin sata, tace,,,

  to madam, karki damu, komai za ayi dai dai, daga nan suhymah tasa kai ta fuce, ko wanka ba tayi ba, ta sanja kaya cikin bakar doguwar abaya, tare da yafa yer gyalensa, ta zuri kudade ta zube cikin yer  jakarta data makale, tare da daukan key din mota, tana barin gidan.

  

    sanye yake brown din hulan saki yer maiduguri, mai tsadar gaske, wanda akai mix da coffee fin zare, hulan daidai kanshi, ta gefe kake gani tattausar bakin gashin kansa, sai dan fine sajen nan daya gangaro, kyararran namiji ne, bata inda be yiba, fatansa wankan tarwada ne, yana da dan fuska mai dan tsawo, idanunsa masu kyau, wanda kullum suke kaman yana jin bacci, hancinsa bakinsa, komai barakallah, yana da cikar kwarjini, tare da farin jini na musamman,,,

  jikinsa na sanye cikin wani danyar brown din shadda wanda ta amsa sunanta, hannun yaji links,  sai babban rigan dake saman kayan, daya jie a'iki na alfarma, da coffee din zare, wanda ya gyatta shi bisa kafadunsa, yai cas cas, kaman wanda akasa pins aka danne, yayi mishi kyau sosai, ya futo kaman wani babban mutum, sai kace ba dan 32years da haihuwa ba, kafansa na sanye da costly and classy swet toms coffee colour,tare da zuba kamshin turaren Deen, mai sanyi da dadin shaka,,,

    young Alh. ABUBAKAR SADEEQ AL-AMEEN kenan, attajirin wanda ya amsa sunansa na dan kasuwa, WAYE SHIE?.

                     *****
   Asalinsu yen garin zazzaune, cikin wata anguwa da ake kira da kwarbai, wanda take kusa da fadan sarki, gidan kakanninsa babban gidane, ba laifi kuma akwai masu danshi a familyn, tunda har sarauta akwai,,,

  gidane wanda ya tara manya manya sasoshi masu yawa, mal. Dahiru kusan shine babba, kuma mahaifi ga Alh.Aminu wanda yake kuma mahaifi ga Abubakar sadeeq din, banda mal.Dahiru, akwai kanninsa da da sauran yen uwa da suka yada zur'iarsu, Alh.Aminu da yarsa haj.Nuratu, wanda suke kira da goggon cikin gida, su kadai iyayansu suka haifa, wanda suka jima da komawa ga Allah, sai yen uwa da sauransu, da ake tare,,,

MATATACEWhere stories live. Discover now