Chapter 11

3.5K 228 3
                                    

🕯🕯🕯
            *MATATACE*
     🕯🕯🕯

     

story&written by
Haleematu💕meemartjj💕
wattpad@Meemartjj

   
*Dedicated to swt sisters*
_Aunty Jamee, aunty Ummeetah and my Fa'ixation._

page 21&22

__________A hankali driver ke shiga da motar cikin gidan man, tare da samun waje yayi packing, jama'ane sosai, ga motocin na matafiya da suma suke barbaje a wajan, driver ya bude motar ya futa, yana kallan sadeeq da fadin,,

   yallabai akwai cikuwan mutane a wajan, bari naje na samu wasu daga cikin ma'ikatan wajen, kai kawai ya daga mishi alamar gamsuwa, daga haka driver ya maida kofan ya rufe,,
 
   ya rage daga shi sai ummeetah da suke zaune a baya, fuskanta na facing waje, ta glass take kallan jama'an dake kaiwa suna dawowa, ta juyo a hankali tana kallonsa, kanshi na kasa yana danna wayarsa, cikin wani sanyin murya take fadin,,

   Baffah plsss zanje waje insha isaka, gaba daya maganar sai daya amsa mishi cikin jikinsa, ya dago yana zuba mata ido, fuska ba annuri yake fadin,,

  duk AC dake cikin motar nan be isheki ba, ya karisa maganan yana dan kasa da idanunsa, turo baki ta danyi, da dan bata rai tana zuba mishi ido, a hankali ya dago idanunsa, shima yayi mata kuri, ta koki kauda nata idanun, dan tsaki yayi kafun yace,,

   don Allah jeki, karki cinyeni, murmushin tasa tana bude kofan ta futa, shima zafin ya jie yana jie, don haka ya bude kofan site din da yake kadan, yana kishingida tare da cigaba da danna wayarsa,,

   can wani dan tudu inda taga wasu classy enmmata, da yen uwansu haka, sun futo daga nasu motar suma suna hutawa, itama ta samu gefe daya ta zauna, tana jie suna yer hiransu ana dariya, ita dai ta cigaba da kallon jama'an dake kaiwa da dawowa a wajan,,

    masu tallace tallace kala kala, mutane daban daban, wata yer matashiyar yarinya ce, da bata fie shekarunta ba, siririya yer doguwa, kallo daya zaka mata ka gane bafullatana ne, kodan zanen dake fuskanta, sanye da hijjabi mai roba, sai yer zani data daura ya dingile can sama, katon tray din silver ne bisa kanta, mai dauke da bread, an tsitsirasu, tana tafe tana talla da fadin,,

   anse biredi, in taje wajan wannan motar taje nan, wani wajan a siya, wani wajan kuma ba'a siya ba, haka harta kariso inda su ummeetah ke zaune, tana kallon yen gayun mutan nan da fadin,,

   hajiya kuse biredi, cikin hausarta na fulani, shiru suka mata suna cigaba da hiransu, ta maimaita yafi so uku, ba wanda ya tanka mata, ummeetah na kallon komai, ko sun jita ko basu jita ba, oho, sudai hiransu suke, wata yer yauki dake gefe, tana zaune cute bag dinta ije a gefe, da suka hada ido da yarinyan, sai daukar jakarta tayi tana rungumewa, ganin haka yasa yarinyan barin wajen da sauri,,
   
    sai dai shigowan wani mai motane da gudu ta kan hanyar, yasa yarinyan yin baya, wanda yayi sanadiyar xubewan bread din nata, kadan ya rage bata fadi ba, wasu kuma daga wajan suka fara mata fadan laifin tane, na tsayawa a hanya da tayi, tuni idanunta suka kawo kwalla,,

   ummeetah ta mike da sauri, tan tayata kwashe bread din, kasancewan kan hanya ne, tare suka mike tana daura mata tray din da fadin,,
 
   yer uwa kiyi hakuri, yarinyan ta sauke ajiyar zuciya, da sharan kwalla tana fadin,,

   kawai don mutum an daura mishi talla, ya zama abin wulakantawa, nima a'i bason raina bane zaka rika yawo a titi, cikin rana kana wahala, komai munayi saboda mu samu abin da zamu cie, amman sai wulakanci za ayita ma mutum, cike da tausayawa ummeetah ke fadin,,

   Allah sarki, kiyie hakuri, wata rana sai labari, sorry kinji, share hawayenta tayi da murmushin, tana fadin,,

   bakomai, nagode da taimako, cikin harshen fillanci ummeetah ta amsa mata, harta juya ta juyo da zare ido, itama da fillanci take fadin,,

MATATACEWhere stories live. Discover now