🕯🕯🕯
*MATATACE*
🕯🕯🕯
story&written by
Haleematu💕meemartjj💕
wattpad@Meemartjj*Dedicated to swt sisters*
_Aunty Jamee, aunty Ummeetah any my Fa'ixation._page 53~54
_____________Kwance tayi abinta kan gado, kirjinta ta kifa bisa pillow sai english novel din dake hannunta tana karantawa, wani baccin ne barawo ke neman tafiya da ita, sai wani lumshe ido takeyi.
iskan dake hurowa cikin dakin ne, ta window dake facing waje, yake dada san yata cikin yanayin bacci mai cike da ni'ima, kadan kadan kuma take jin karar bude windown, yayin da design white cottons din dake windown suka shiga yawo suna hurowa ciki.
abin sai ya zame mata kaman a mafarki, kamshin turarenshi ne ya sanyata bude idanunta tarr, tare da dagowa a hankali tana juyawa site din da windown yake, sosai ta zaro ido tana dan murmushi, shima murmushin yakeyi tare da kashe mata ido daya.
zaune yake bisa windown daya hauro ta ciki, ya juya ma waje baya, hannunsa daya rike da wani milk din leda, yayin da dayan yake mata alamar taxo gareshi, mikewa tayi cikin natsuwa shikam saiya zuba mata ido, tana dan gyara pink straight skirt din dake jikinta, sai wata bakin rigar sanyin data sanya a sama mai zip ta gaba, saboda sanyin da ake tsalawa.
yen labbanta sai faman spakling sukeyi, gashinta a fake yake cikin wani bakin hulan sanyi, saita futo da sauran ta kasan hulan, tayi kyau cass da ita, ga hasken da fatarta ya kara ya amsheta, kusa da dan shi ta matso tana fadin,,
Baffah sannu da zuwa, yama kasa magana sai cewa da yayi,,
come on give me a hug, kaman jira take ta fada jikinshi, tana sakalo hannayenta duka biyun ta wuyanshi, tare da hardesu cross, fuskanshi take dan kallo dake kasan nata, sai lokacin tasan da kuma jin kunya, tana boye fuskanta a gefen wuyanshi, hakan ya taimaka wajen kara hada jikinsu waje daya, murmushi sosai yakeyi, yasa dayan hannun yana runguman bayanta, a hankali kuma ta dago, dai dai sanda yake fadin,,
baby yhu too much happy, idanun kasa kasa tana wani kalan murmushi tace,,
saboda ina tare da Baffah nah, sosai kalaman suka ratsa can kuryan zuciyarsa, ya kuma tallafo fuskanta da fadin,,
da gaske kike, kai ta daga alaman eh, idanunta rufe wai ita nan kunya, har lokacin da murmushinta mai bayyanar da dimple dinta, kallonta kawai ya tsaya yie, jin shirun yayi yawa ne ya sanyata dan bude idanunta, kakkaurar white sweater din dake jikinshi take kallo da kuma white p~cap din daya sanya bisa kanshi.
hannayenta ta sanya ta bayanshi tana jawo hulan dake hade da sweatern, ta daura mishi bisa p~cap din, sai kuma ta jawo tafukan hannunsa da suke a kankakare, saboda snow din dake sauka.
drower ta wuce tana dauko wasu kauraran handgloves tazo ta sanya mishi, da fadin,,
Baffah plss ka daina futa ba gloves, kasan snow yayi yawa, bana son kayi mura fa, shidai komai takeyi binta kawai yake da kallon burgewa, itakam duk wannan abin taki yarda su hada ido, can kuma saita dan wayance da kallon ledan daya shigo dashi tana fadin,,
lah ka siyo mun popcorn dinne?, ajiyar zuciya ya sauke yana dago ledan da fadin,,
ba dole ba uwar gidan Baffanta sadeeq, zoki zauna in baki a baki, murmushi tayi tana kokarin barin wajen ya jawo hannunta da fadin,,
ina zaki, dan war tayi tana fadin,,
zan dauko abin zama ne, hannunta ya jawo sosai yana daurata bisa kafafunshi da fadin,,
come on, a'i baki da wani abin zaman daya wuce wannan, duk sai taji kunya ya kamata, kafun kuma ta gyare, a baki yake bata popcorn din ana cie ana yer dariya.