Chapter 33

3.8K 196 0
                                    

🕯🕯🕯
    *MATATACE*
          🕯🕯🕯
  

story&written by
Haleematu💕meemartjj💕
wattpad@Meemartjj 

*Dedicated to swt sisters*
_Aunty Jamee, aunty Ummeetah any my Fa'ixation._

page 65~66

__________A hankali take sauke ajiyar zuciya, tare da share Hwayenta, sanda mummy ke dialing number haj. biswa da video call, sosai suka natsu lokacin da kiran ya fara shiga.

  hoton hamshakiyar macace ya bayyana, tana zaune bisa wasu tsadaddun dinning chairs, taji gwala gwalai a hannu, wanda ya futo ta cikin hannun zumbulelen hijjabin dake jikinta har kasa, cikin salama mummy ta fara kai gaisuwa da fadin,,

  ina gaisuwa shugabar kungiya, da fatan an tashi lafia?, cikin kasaitaccan murmushi ta amsa,,

  barka dai haj. yagana, inace me jiki dai taji sauki?, ajiyar zuciya mummy ta sauke tana fadin,,

  to sauki da dama, dama dai kan lamarin nan ne da mukai magana, uwar kungiya a duba mana, a'ikifa ya lallace, komai ya sukurkuce, plsa ki duba…………, da sauri ta dakatar da ita ta hanyar daga mata hannu da fadin,,

   dakata, ban fahimce kiba, mun riga da mun gama wannan maganar tuni dake, haj. yagana ko kun manta ranar da kuka zo, a gaban idonki yerki ta shiga kungiyar mu akan biyar bukatanta da yarjejeniyar da mukayi akan kar wata mace ta rabi mijinta, an jaddada mata tace ta yarda, baxan manta ba ana gobe daurin auranta, to sai yanxun zata dawo mana da hannun agogo baya, ko dan taga yanxun ta haifeshi ne harya girma, shine tak……,,

   da sauri suhymah ta fisge wayar, da wasu hawaye da suka wanke mata fuska tana fadin,,

   wlhy ban yarda ba, munyi yarjejeniya akan zan samu biyan bukata nah, kun zalunce nie kunce zan samu yanda nake so, a karshe kuma ina zaune saiga mijina da mata harda cikinta, ta tsananta kukanta da fadin,,

   haba haba, wannan zalunci yayi, yawa, wacce irin kungiya ce wannan mara adalci, to nie gaskiya yanxun bana bukatar komai daya wuce d'ana, bani da burin daya wuce inga na haifi yara da yawa, suna kaiwa da dawowa, amma yanxun mafarki na ya zama ba gaskiya ba, Irfan ne kawai wanda ya rage mun inna kalla zanji dadi, plsss na rokeku kubar mun d'ana, baxan iya rayuwa ba Irfan ba, wani dan murmushi tayi kafun tace,,

  baxai yuyuba suhymah, kin riga da kinyi sakaci, kin riga da kin bama kungiya d'anki, yanxun shi kai d'aine ya rage akan hanya, kuma kungiya nada babban buri akan d'anki, sai dai kiyi hakuri……,,

  karya ne, suhymah ta kara katseta da kuka tana fadin,,

  wlhy baxan baku Irfan ba, sai dai kuyi duk abin da za kuyi, ga mari ga tsinka jaka, da wanne zanji, to wlhy Irfan yafi karfin ku, in kuna amai kuna lashewa sai dai kunci kanku, azzalumai marasa mutun……,,

   da sauri mummy ta fisge wayar tana datse kiran, saboda ganin yanda suhymah ke neman juya lamarin ya koma na tashin hankali, jikin mummy ta fada tana sanya wani kuka maicin zuciya da fadin,,

   wayyo Allah na aunty na shiga tara, na bani ban lalace ba, da sauri aunty ta zungureta tana dagowa, da sallama ya shigo rike da hannun Irfan, ta koma da baya tana kuma rushewa da kuka, gaba d'aya sai yaji zuciyarsa ta karaya.

  ya rasa me yasa ta kasa daukan kaddarar daya shigo rayuwansu, tsam mummy ta mike sum sum sum ta fice, kusa da ita ya zauna yana fadin,,

   suhymah wai har yanxun ba zaki daina wannan kukan ba, kinga yanda kika dawo?, harara ta zabga mai cikin kuka tace,,

  kace haka mana, a'i kaima sadeeq harda kai, ban taba tunanin zaka iya tarayya da wata y'e mace ba bayan nie, ban taba tunanin haka daga gareka ba, sadeeq duk irin son da nake maka, ko da baka da laifi, nawa yafi yawa dana dauka yardana na mika maka, ta karisa maganar da matsanancin kuka tana fadawa saman kirjinshi.

MATATACEWhere stories live. Discover now