Babi na talatin da biyar

9.5K 970 234
                                    

*Bismillahir rahmanir rahim*

*huwallazi yuhyi wa yu miit*

*sannan shi (Allah) shi yake rayawa yake kuma kashewa*

______________________________

       A tsakar gida zainab ta sake shimfida musu wata tabarmar suka koma ciki.

       Hira sosai suka dinga yi har da mama,abdur rahman na basu labarin garin ma'aiki madinatul munawwara har aka kirayi sallar magariba,tare suka fita sallar shi da malam da yaya abubakar,koda suka dawo ma bai tafi ba tare suka ci abincin dare sannan ya musu sallama.

         Hannunsa dauke da abdallah ya fito daga gudan,bahijja da sumayya na bayansa wadda ta fito don ta dan taka musu,a bakin motarsa sabuwa da ya sauya qirar range rover yaja burki yana duban sumayya
"Tsarabar abdallah bata qaraso ba,ko zaki dan rakamu waccan titin dake gabanku naga akwai wami super market na dan masa siyayya kafin su iso?". Kai ta kada tana dubansa
" haba sabida dorawa kai wahala,mun yafe duk sanda suka iso ma amsa".kunu ya dan sha yana dubanta
"Dorawa kai wahala kuma?,niba babansa bane?,ko kina so kice ba yarona bane?" Baki ta bude tana dariya tare da dubansa tace
"Ni na isa in fadi haka,kai matsala ta da kai son girma fa"
"Ban kai naso girma ba ko sumayya?" Ya fada cikin wani irin salo da ya sauya yanayin muryarsa idanunsa cikin nata,wanda ya haifarwa da sumayyan rage farashin dariyarta,karon farko da taji duban qwayar idonsa ya mata nauyi,sai ta janye idonta tana cewa
"A'ah,ai ko da sakan daya mutum ya girmeka ya girmemaka har abada" dan shiru yayi sannan ya gyara tsaiwarsa yana miqa mata abdallah
"Karbeshi yau mun wunar muku,sai kuma gobe idan Allah ya kaimu" ta amsheshi tana cewa
"Allah ya nuna mana goben" cikim zuciyarta ta dauka da wasa yake,hannun abdallahn ya bude ya sanya masa 'yan dubu dai dai guda uku yana cewa
"Kasha sweet my son"
"Habba abdur rahman...."
Katseta yayi ta hanyar cewa
"Shshshshsh!,ai bake na bawa ba ko?,kuma wai bakijin kunyar fadar suna na haka gatsal?" Galala ta saki idanu ta bishi da kallo
"Kunyar kamar yaya?" Ta fada tana dubansa,murmushu kawai yayi ya bude gaban motarsa ya zauna sannan yace
"Sai goben ko 'yamma ta?" Murmushi ta saka mamakin abdur rahman din na kuma kasheta
"Nice kuma yau 'yammata abdur rahman ga yaro na a hannu?"
"Oh,kuma fadar sunan nawa dai kika yi?" Ya tambayeta yana kada kai,shuru ta masa tana zagayawa wajen bahijja ta dubeta
"Bahijja ki gaida mama kinji,naga alama wannan yayan naki bayan karatu sa ya tafi qarowa ya qaro yadda ake canjin hali" dariya bahijjan tayi tana amaa mata da zata ji,shima dariyar yayi sannan ya tada motar tasa yayin da sumayya ta shige gida.

        Tunda ya shigo da motarsa layin su sumayyan ya hagi tsaiwar wata motar a qofar gidansu,har zuwa yanzu da motar tazo ta wuce ta gefan tashi yana binta da kallo tare da qoqarin tantance waye a ciki,saidai duk qwaqqwafinsa ya kasa gane waye a ciki saboda glasa din motar mai duhu ne,hakanan sai yaji wani abu mai tauri ya riqe masa wuya,rabin 'yar walwalar da ya samu wunin yau ta kau baki daya,a sannu yaci gaba da tuqa motar tasa har ya qaraso qofar gidan ya tsaya ya fito ya samu yaro ya aikashi ciki,ba jimawa yaron ya fito dama sun riga da sun saba duk sanda aka aika akace ana gaida mama to mukhtar din ne kuma sun san me yazo yi,sai halima ko zainab ta kawo masa abdallahnsa,nan cikin mota yake zama da shi su qaraci wasan su sannan yayi horn su fito su karbeshi da abinda ya kawo masa sannan ya wuce,sau tari yakanji sha'awar ganin sumayyan saidai babu wannan damar,rabon da ya ganta ma bazai iya tantance adadin kwanakin ba,tilas yaje danne komai don ya sani a yanzu ta fita a huruminsa.

        Yau din ma kamar kullum hakan ce ta kasance,abdallahn nata masa gwalanto saidai bai gane me yake cewa ba biye masa kawai yake,bai wani jima ba ya maida shi ya tafi zuciyarsa na sakutarsa kan motar da ya gani,ya mance cewa a yanzun sumayyan rabon mai rabo ce ba mallakinsa bace

  ****    *****   ******  ****

          *BAYAN KWANA BIYU*

      Tun daga ranar abdur rahman ya maida gidan gurin hirarsa,wani lokaci yazo shi kafai wami lokaci ya taho da bahijja,da yake su biyu Allah ya bawa mamansu,sukan dauki lokaci da sumayya suna hirarsu,yayin da wani lokaci idan ya furta wata maganar sai ta sanya ta a duhu,wani sa'in takan yi murmushi ta alaqanta hakan da girma da abdur rahman din ya sake yi,ya fara zama babban mutum shi yasa yanayin hirarrakinsa suke sauyawa,bata taba kawo komai cikin zuciyarta ba saboda ita din rainon mutum daya ce da mutum daya ta taba gina duniyarta wato mukhtar,ba komai take iya ganewa ba ko fahimta game da wasu baqin al'amura a gun d'a namiji ba.

KUNDIN QADDARATAWhere stories live. Discover now