Babi na saba'in da shida

14.8K 1.2K 315
                                    

*Bismillahir rahmanir rahim*

*la haula wala quwwata illa billahil aliyyul azim*
_____________________________________

        Cikin babbar haraban asibitin motar ta ajjiyeta a muhallin da aka tanada saboda ajiyar motoci,cikin rashin qwarin jiki ta bude murfin motar ta fita sanda drivan ke kashe motar yana sake daidaita tsayuwarta,kai tsaye reception ta isa,aka bude mata file kasancewar komai kyauta ne,tayi mamakin kyau da tsaruwar asibitin,wanda ta tabbatar da cewa inda mamallakin asibitin yayi shine saboda kudi ba shakka ba qananun kudi zaya samu da asibitin ba,tsarin ya burgeta,ba qaramar dabara yayi ba,saboda tasan ladan da zaya samu ba kadan bane,d'aya daga cikin abubuwan da masu kudinmu basa ganewa kenan,sun gwammace suyi saboda kasuwanci,ba don ya zame musu sadaka mai gudana ba wadda zata yita bibiyarsu har bayan rayuwarsu ba,abune wanda koda sunyi ba komai bane cikin dukiyar da Allah ya basu ba,Allah madaukakin sarki yana cewa
"Yaku wadanda kuka bada gaskiya da Allah ku ciyar daga abinda muka azurtaku tun kafin ranar da babu fansa a cikinta(da zata yi maka amfani),ba abokantaka (a cikinta da zata yi maka amfani),ba ceto(sai da izinin ubangiji)tazo muku(wato ranar qiyama",bayan mai bada katin ya gama cike mata ya miqa mata yana nuna mata inda zata kai a saka ta a layi yana fadin
" kinyi sa'a kuwa malama,yau oga ne da kansa ya zauna,ba kowa ke samun sa'a irin haka ba ranar garkonshi"ya fada yana washe baki,don tunda ta shigo tayi masa,duk da kasancewarta cikin zabgegen hijabi har qasa amma hakan bai gaza bayyana kyawunta ba
"Na gode" kawai ta fadi ta amshi folder din ta kai inda yace mata,akwai mutane kusan goma sha biyar a gabanta,saboda haka dole ne tayi zaman jira,bata jima da zaman ba kiran nafisa ya shigo wayarta,wanda shine ya sake dauke mata hankali da radadin da take ji,don a qalla sun bata kusan minti talatin suna waya kafin su rabu.

       Sannu sannu suka soma raguwa,duk wanda ya fito fuskanshi qunshe take da fara'a saboda an duba shi yadda ya kamata,uwa uba zai samu magunguna masu kyau fiye da kullum,wanda kusan yawancinsu masu ciki ne,duk na gabanta suka qare layi yazo kanta,wanda bayan fitowar matar qarashe ta miqe ta isa qogar office din ta tura ta shiga.

      Lafiyayyen office ne wanda yake a tsaftace sannan a tsare kamar yadda ilahirin asibitin yake,office ne mai girma wanda daga hannun hagu ke dauke da rukunin wasu irin kujeru kusan guda hudu da table dinsu a tsakiya,kana shigowa kuma table din likitan ne wanda ke dauke da tashi kujerar da kuma kujeru guda biyu a gaban table din suna fuskantar juna wanda anan patient ke zama yayi bayani,daga bayan tashi kujerar wami dan katako ne a tsaye wanda yake rataye 'yar saman suit dinshiba jiki,sannan gaban table din kadan dan gado ne wanda ke hade da na'urar sacanning ta musamman da sauran tarkacen likitoci,daga hannun dama kuwa qofofi biyu ne kulle,daura da su freezer ce girke a kanta akwai set na warmers da cups na tea da na ruwa,sai coffe maker daga gefe.

      Tsaye yake gaban gadon scanning din inda ya baiwa qofa baya,hannunshi dauke da takardar da ya gama yiwa wata mata scanning yana dubawa,ranshi a bace yake sosai har hakan ya nuna saman fuskarshi,yana mamakin yanda a yanzu maza ke wasa sa haqqunanau kan matayensu,kana da mata tana dauke da cikinka,wanda rayuwarta na cikin qila wa qaala ne,ko ta mutu ko dan ya mutu ko a rasa su baki daya idan kuma ta kasance daga cikin masu sa'a su rayu baki daya,amma ka kasa tsayawa ka bata kyakkyawar kulawa?,abincin da zata ci mai kyau ya gagareta?,kullum tana cikin tashin hankali da masifa,tayi wahalarka tayi ta yaranka?,akan me?,saboda me?,duka cikik zuciyarsa yake wannan maganan.

       Turo qofan tayi sallama a bakinta,ya amsa ba tare da qwaqwalwarsa ta bashi wace ba,dan tsayawa tayi saboda batasan inda zata zauna ba,ga faduwar gaban sata rusketa lokaci daya sai daga bisani ganin ba'a ce mata komai ba sannan ta taka ta isa gun kujerun ta zauna.

        Takardar ya nade ya ajjiyeta gefe yana sakin tsaki sannan ya juyo a hankali ta tako zuwa nashi muhallim ya ja kujerar ya zauna ba tare da ya dubi wadda ke zaune din ba,duk da yana shaqar wani qamshi da kamar yaso ya sanshi,ya jawo file dinta ya bude,ganin sabo ne alamun zuwanta na farko ne ya sanya shi fadin
"Uhm,meke damunki?",ita din ma bata dubeshi ba har sai da sautin muryarshi ya daki kunnenta,da sauri ta daga kanta idanunta suka sauka kanshi,tsabar ciwon dake murda mata ya hadu da firgitar da tayi ya so riqe numfashinta,qoqarin miqewa take amma ta kasa,har ya kammala rubuta date din da zaiyi baiji an amsa ba,hakan ya sanyashi daga kansa yana tsammanin ko kurma ce,idanunshi ya dan ware a kanta,kafin yq maidasu yadda suke,wanda hakan ya taimaka wajen sanyata miqewa da hanzari dom barin ofishin,ta gwammace ta haqura da ganin likitan baki daya,cak ta tsaya jin sautin muryarsa kuma muryar mukhtar yana bata umarnin dawowa inda ta tashi din,har cikin zuciyarta tana jin ba zata iya tsayawa ba,a inda daga shi sai ita?", sai ta sake daga qafarta don cikin yunqurin cimma ficewa daga office din ba.

KUNDIN QADDARATAWhere stories live. Discover now