Babi na tamanin da biyu

20.3K 1.4K 432
                                    

*Bismillahir rahmanir rahim*

Allah S W T yana cewa

*ALLAH BAI SANYAWA WANI MUTUM ZUCIYA BIYU A CIKINSA BA*
______________________________________

Gyara kwanciyarta tayi haka fuskarta dauke da murmushi,hakanan take jin dadin kallon hotunan,tunda ya shigo hotel din har ya kai ga qarasowa dakin ya jima kanta tsaye bata sani ba
"Wannan mutum" ta fada a fili qasa qasa
"Fuska kaman an maka mutuwa,smile sunnah ne fa" ta kuma fada tana wucewa zuwa hoton gaba,kowanne hotu da irin yanayin da aka yishi,ta yadda ta kuma sake tabbatarwa yanayinsa daga Allah ne kurum
"Ya salam" ta furta a hankali sanda tazo kan wani hoto nashi da yayi cikin kayan sarauta baki daya harda alkyabba,wani dan banzan kyau yayi ba na kadan ba,wannan ne karo na farko data ganshi bata suit ba,tashi tayi zaune tana gyara zamanta,sai ta hangi kamar inuwar mutum,wani tsoro ya shigeta zuciyarta ta fara gudu,wani yunquri tayi ta miqe zatayi bayan gado da gudu taji an cafketa,sai ta bude baki zata saka ihu,cikin hanzari ya dora bakinsa kan nata ya rufe nata bakin,idanu ta qwalalo tana son fahimtar meke faruwa da ita tare da daga idanunta sama don son ganin waye,da sajen gefan fuskarshi ta gane,sai yanayinta ya sauya daga firgici zuwa tsoro,bugun zuciyarta ya sake qaruwa ta dinga yunqurin janye bakinta amma batasan me ya hana hakan tasiri ba.

A hankali ya zare bakinsa yana janye jikinsa baya,yana jin yadda feelings dinsa ke sauyawa,fuska a hade yana tuhumar kanshi,juyawa kawai yayi ya soma cire takalmin qafarshi da safarsa sannan ya shige toilet kai tsaye,ragwab ta fadi saman kujera tana dafe da kanta,ta rasa me zata iya tunawa cikin abu biyu,ruqon da yayi mata da tsoron da ya bata,ga wani mutuwar jiki sakamakon tsoratar da tayi tun da fari,tana naj zaune dafe da kanta har taji bude qofar toilet din,idanunshi ya sake sauka kanta,hargitsatsen gashinta da rigarta data cukuikuye ya kalla,hakan ya tuna mata kayan dake jikinta,sai tayi hanzarin saka hannu ta janyo hijabinta ta zura,idanunta a qasa ra furta
"Sannu da zuwa"yana takawa zuwa gaban madubi ya amsa
"yauwa..." Shuru ya sake dan ratsawa kadan,ba wanda ya sake furta komai har sai daya kammala shafa mai sannan yace da ita
"Ki shirya zamu fita" ya fada a taqaice,bata tsaya fahimtar komai ba ta fada toilet,don dama neman mafaka take,ta jima ciki tana sauke numfashi kamin ta soma wanka,batasan me yasa abun ya tsaye mata a rai ba.

Yana tsaye gaban mudubi yana gyara sumarshi tare da duban kanshi,ya kalli labbansa a hankali ya sanya harashensa ya kasheshi,qwaqwalwarsa ke qoqarin bijiro masa taushin da yaji saman lips dinta yana qoqarin fada da hakan,tsaki ya saki bayan ya gama gyara sumar tashi yayi jifa da cumb din sannan ya nufi wajen kayan sawarshi ya fidda shirt da trouser baqi da ja ya shirya,ya sanya takalma high top tare da maqala sun glasses don sakaye idanuwanshi ya bude qofar ya fice.

Sanda ta fito baya nan,tunani take ina zasu haka?,duk da batasan inda zasun ba amma hakan ya mata dadi,koba komai zata fita waje tasha iska,tsaf ta shirya cikin abaya maroon data fito da hasken fatarta wadda samanta ke a tsuke qasan a bude qwarai akwai yalwa,ta gyara sumarta ta daureta da band sannan yi rolling da mayafinta,ta daura agogo kana ta sanya zoben dake mahadin agogon ne tsakiyar yatsanta,takalmin data sanya mai tsini ne duk da bata saba sanya irinsu ba amma ta yiwa kanta alqawarin koyar saka su,wani fitinannen kyau tayi tamkar wadda ta fito daga jinsin larabawa,bakinta yasha jan janbaki radau ya sake fitar da sigar dan qaramin bakinta,dududu bata fi sati uku ba cikin qasar amma fatarta ta sake haske da gogewa kamar wadda ta shekara,tana tsaye gaba mudubi tana shafe jikinta da humra ya turo qofar,tsayawa yayi kadan yana dubanta,ko yaqi ko yaso tayi masa kyau,dalili kenan da ya sanya yake jibgowa amira abaya tun a gidan,shigar tana burgeshi,mutum ne mai son kwalliya matuwa da gaske,hakan ne ya sanya tasu ke zuwa daya da amira kota wajen siyayya,saboda tafi farida da huda ado,ganin tana yunqurin waiwayowa ya sanyashi dauke kai,ya qaraso cikin dakin yana daukan wayarsa
"Bani wayata idan kin gama min kallon qurillar da kuma gulmar" mamaki ya kamata,wato dazun dama tsayawa yayi yana ganinta taba kallon hotunanshi?,kunya ta kamata sai ta zunbura baki cikin harshen larabci da take tsammatar ba zqiji abinda take fada ba qasa qasa tace
"Gulma?wai kallon qurilla,to me zan kalla?" Dagowa yayi yana murmushi qasan ransa ba tare da bayyana saman fuskarshi ba,yasan tayi maganar ne ga tunaninta baiji ko bazaiji me zata ce ba,hannunshi ya harde a qirji yana dubanta har ta dauko wayar ta sake nufowa wajensa ta miqa masa,ya kafeta da mayun idanunshi yana mata kallon qurilla,baiko bi ta kan wayar da take miqo masa ba,ya motsa bakinsa kamar wanda baison yin magana
"Qarya nayi kenan?,na gaya miki me kike kallon ko zaki iya tunawa da kanki?" Cikin mamaki ta daga kai ta dubeshi,saidai nauyin da idanunsa suka yi mata ya sanyata sadda kai ba shiri,ashe yana ji?,ta shiga uku ita kam,me ya kita kallonsa koda a waya ne bare tayi masa qunquni?,sake matsowa yayi gab da ita yana son hade tazarar datayi saura tsakaninsu yana duban lips dinta,haka kawai yaji ya bashi sha'awa yadda jambakin ya kwanta saman farar fatarta
"Uhummm,ki bani amsa ko ni na amsa miki,na lura kamar baki da kunya fa sosai" gabanta ya fadi,jikinta yayi sanyi,ba'a taba mata shaidar rashin kunya ba sai yau,yanzu idan da malam ko ma zasuji ya fadi hakan Allah ne kadai yasan fadan da zata sha,sai idanuwanta suka tara qwalla,bata so yayi mata wannan shaidar ba,muryarta na rawa alamun fara kuka ko da yaushe tace
"Kayi haquri,bada niyya bane?"
"Kika yi me?," ya fada yana sake takowa saura kadan ya hade jikkunansu,tsoro ya hajata daga qafafunta bare taja baya,gani take yau Allah ne yasan me zaya yi mata
"Komai ma" ta fada tana dauke qwallar data ziraro mata ta ido daya ta daya idon tana shirin fitowa itama,hakan yaji tausayinta ya kamashi,a yau din nan fa ita ta fiddashi daga matsalar daya kusa sati biyu ciki,bata cancanci tayi bacin rai a yau din ta sanadinsa ba,bata da kowa a qasar saishi,kwananta kusan ashirin da wani abu tana wuni cikin kewa ita daya qulle a dakin,zaya so a yiwa amiransa haka?,bai manta ba hamza yace ya dauketa tamkar qanwarshi sai a yanzun yaji zai iya hakan.

KUNDIN QADDARATAWhere stories live. Discover now