zakisan koni waye 15 and 16

10.7K 401 126
                                    

[5/8, 8:47 PM] ‪+234 813 737 1414‬: 💜💛💚💙❤
*ZAKISAN KONI WAYE
* 💙💚💛💜💛
®zuwairat(ummu maryam)

1⃣5⃣

Dad ameera sauri yake don ya isa gida, yana shiga gidan ko parking kirki baiyiba ya shiga ciki.

Direct dakin mom ya shiga, mom juyowa tayi ta kalleshi kafin tace
"Alh lafia? Ko yauma baka samu ganin shi ba?" Hulan kanshi ya cire yana cewa
"Hajiya.. Ameera ta tayi goshi..." Mom na jin ya kira sunan ameera ta dan bata fuska kaman ba ita ta haifetaba.
"Me akayi kuma?" Dad cire babban riganshi yayi yana cewa
" ameera ta tayi goshi wallahi... Saidai yan bakincik su mutu" dan tabe baki mom tayi
"Wai me yafaru?"
"Ai naga kin bata fuska daga kiran sunan ameera.. To albishirinki"
"Ni ka gayamin abinda ke faruwa" zama dad yayi kusa da mom tare da dora hannunshi kan kafadan mom sannan ya fara cewa
" sir Salem yace yanason ameera da aure kuma na bashi..." Zumbur ta mike
"Haba alh..yace yanasonta ko ka kaimashi tallanta...kuma yarinyan da ba ganin kowa da gashin arziki zaka bawa shugabanku gaba daya ta jawo mana zagi?" Ta danyi shuru ta hadiyi wani abu sannan ta cigaba dacewa
"Gaskiya alh ka sake shawara.." Shima mikewa yayi
"Daman nasan haka zakice...wallahi da ba gabana kika haifeta ba da sai ince bake kika haifetaba...to aure anyi angama...cewa  yayi zai kirani..yana kirana yau zansa a daura masu aure a tafi da ita gidan Hutu...ban taba ganin inda uwa take bakin ciki da karuwan yarta ba sai a kanki...rubbish" mom baki ta tabe  kafin tace
"Ni ina ruwana...daman tsutsun daya ja ruwa kanshi yake karewa....ayi lafiya" dad baice mata komai ba ya fice, direct dakin ameera ya tafi ,nan ya zaiyana mata yanda sukayi da Salem, dad bata gamaba tayi daka tsalle ta fada jikin dad dinta, shima rungumeta yayi.

Bayan dad yafita, kwantawa ameera tayi kan gado tana cewa
"Daman haka Allah yake biyawa bawanshi bukata? Daman duk abinda mutum ke in har kasa abun cikin ranka zaka samu?.. Imagine me as Salem wife , imagine me as surukin former President... Woowww" tafada da karfi tana tsalle kan gado, wayanta ta dauka tafara dailing number zeenat.

❤💜💙💚💛

Bangaren Salem kam hankalishi kwance don yanzu kwana uku da maganan shi da dad ameera, gini kam ana chan anayinta abinka da mai naira har an gama fence din kuma da aka turowa Salem hoton cewa yayi yayi kadan akara tsawon fence din, wani irin dogon fence mai kama da tower akayi sannan aka fara ginin ciki, shima har sunkai tsakiya aka turawa Salem hoton,  shima cewa yayi dakunan sunyi girma a ragesu.

Yau yana kwance murmushi ne kwance a fuskanshi.. Kona meye oho, wayan shi ya dauka yasa Abdul ya kira Makeup artist dinshi.

Around 5pm suka bar gidan, suna zuwa daidai inda ameera ta mareshi ya fara kallon wurin kawai sai ya hangi kaman yarinyan data siya mashi cotton wool lokacin da yake nasal bleeding, kallon Abdul yayi kafin yace
"Alh wancan kaman yarinyan data siyamin auduga ko..." Shima Abdul kallon wurin yayi
"Yes sir..itace kuma kaman abun hawa take jira...kilan ta tashi daga wurin aiki" Salem rage gudun abun hwanshi yayi yana cewa
"Wane aiki take?" Abdul murmushi yayi
"Sir bakaji sanda madam din datakewa aiki tana zaginta wai ta kashe mata kudi har  da cewa saita biyata..." Shuru Salem yayi kaman mai tunanin wani abu  sannan yace
"Sam banjiba ai yarinyan nan tana marina wuta ya daike min Amman naga sanda ta sayi auduga ta baka...Amman baka gayamin aikn datake ba" suna zuwa daidai inda take Abdul nacewa
"Inajin abinci suke saidawa don naji matan nacewa tawuce ta bawa mutane abinci" Salem tsaida taxi yayi inda take, tawa na ganin taxi ya tsaya sai tadanyi baya kadan, Salem dan fiddo kanshi yayi ita kuma ta kura mashi ido tana tunanin ina nasan wannan mutum, Salem zai bude baki yayi magana ta fara cewa
"Lah...Ashe kaine..ina wuni"
"Lafia lau...kinyi tunanin na mutune?" Dan murmushi tayi Wanda ya bayyana one side dimple dinta
"Aa..kawai banyi tunanin kai bane"
"To naji..zo in baki lift"
"Aa nagode..." Kura mata ido yayi for a moment kafin yace
"I insist.. Ko kina tsoron kar..." Dan daria tayi ya dan saci kallon hakoranta
"Meye na tsoro.. Kawai dai nagode.." Shima Salem Dan daria yayi itama tawa tadan kalleshi tayi saurin kauda kanta
"Please ki shigo in ajiyeki" kallon Abdul tayi kafin tace
"wannan passenger da ka dauko fa..kar mu shiga hakkinshi..." Abdul murmushi yayi
"Kar ki damu ni abokinshi ne..." Tawa Dan tsayawa ta yi kaman batason shiga kuma da ka ganta da akwai Dan alaman tsoro tare daita, kara daga kai tayi ta kallesu suka hada ido da Salem, cikin ranshi cewa yayi
"Wannan yarinyan da akwai manyan idanuwa kaman na mage" ahankali ta bude bayan motan tashiga , tana shiga ta dan kwantar da kanta bayan seat da alaman gajiye take, Salem juyawa yayi ya kalleta
"Hajiya ina zaa kaiki?" 
"Oh sorry...tukuntawa zaa kaini"
"Babu nisa ma" inji Abdul, Salem fara tuki yayi, yana cikin tafiya yadan saci kallon ta ta mirror yaga sai lumshe  ido take ahankali,  cigaba da kallonta yayi har ya mance da tuki yake,  saida ya kusa bige wani sannan yadawo hankalinshi, bai dade ba yakara kallon ta wannan karin itama ta daga kanta sukayi ido hudu dashi, murmushi yasakar mata kafin yace
"Nagode da taimakonki fa..."
"Haba ba komai...Amman kabani mamaki..." Daga kanshi yayi ya kalleta
"Da nayi me?" Cikin irin jin haushin nan tace
"Da baka rama marin datayi makaba...mazan hausawa da akwai hakuri wallahi da mazan yarenmune da yarinyan nan bata kara marin mace yaruwanta balle namiji" Salem Dan murmushi yayi yana tunanin
"Bakisan abinda ke faruwa don ina tabbatar maki when am done with her ko dabba bazata iya tabawaba balle mutum" dan murmushi yayi
"To ya zanyi tunda ni talaka ne...wai ke wace yaraece?" Ya tambayeta, Ahankali tace
"Yoruba" ido Salem ya kwalo don sam bata kama da yare
"Kambu " yace cikin ranshi sannan yace
"Yoruba? Amman meyasa kike Hausa kaman bahaushiya?"
"Nan aka haifeni"
"Wow..ya ake cewa kina da kyau da yarenku?" Dan daria tayi shima Abdul yayi
"Ni ban iyaba Amman inaji"
"Baki iyaba kwata2? " Dan girgiza kanta tayi sannan tace
"Naiya few words" Dan daria yayi sanda Abdul ya nuna mashi hanyan dazasu bi, saida yabi hanyan sannan yacigaba dacewa
"To ya ake cewa  my friend da yarenku?" Ahankali tace
"Ore mi" dan daria yayi kafin yace.
" zaki zama oro mi?" Cikin daria tace
"Ba oro mi naceba...I said ore mi" dukkansu daria sukayi kaman sun wani dade na sanin nuna
"To naji..zaki zama ore mi?" Shuru tayi kaman bada ita yakeba.
Saida ya kara cewa
"Baki bani amsaba?" Kallon shi tayi ta mirror suka hada ido tayi murmushi tare da kauda kanta
"Cewa nayi will you be my ore mi" ahankali tace
"You are funny.. Ka taba ganin inda mace da namiji sukayi abota?"
"Eh mana in kuma babu sai mu zama na farko" tawa shuru tayi bAtace komaiba ba salem ya sake cewa
"So zaki zama ore mi?" Batace komaiba har suka zo gidansu,
"Nan zan sauka" tace mashi, tsayawa yayi ta bude ta sauka sannan tace
"Sakallahu akhaairan..." Murmushi yayi
"Ameen nagode" juyawa tayi ta fara tafiya, Salem yabi bayan ta da kall, cikin ranshi yana
"See hips" Salem da akwai san hips, binta yayi da kallo har saida ta kusa shiga gida sannan yace
"Ore mi..baki gayamin sunan kina?"  Ahankali tawa tace
"Tawakaltu"
"Lovely name for a beautiful owner" tawa daria tayi  tare da dan  girgiza kanta sannan ta shiga gida.
Tun waje Salem kejinmuryan yara suna anty tawa oyoyo. Salem kallon yanayin unguwan yayi sannan yace
"Alhamdulillah" kallon Abdul yayi sanda yake juyawa da motan yace
"Alh yau nasamu mace ta farko da tayi min daria" shima Abdul cewa
"Gaskiya kam..ko mun samu amarya?" Hararan Abdul yayi
"Kanason first love taci ubana kenan" Abdul murmushi yayi
"Sir ai bakasan ikon Allah ba" Dan daga kai Salem yayi kafin yace
"Gaskiya kam Amman kada Allah yabamu abinda yafi karfinmu"
"Ameen" Abdul ya amsa mashi,  wuri ya samu yayi parking
"Alh kadawo nan ni nagaji da wannan driving din" ba musu Abdul yafita ya barwa Salem wurin bude Salem ya koma driver seat suka bar wajen, dan yawo suka danyi duk wacce ta tsaida su sai Salem yace kar su tsaya yana cewa
"Alh mu wuce kawai banason shan zagi da yamman nan.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: May 09, 2018 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

zakisan koni wayeWhere stories live. Discover now