zakisan koni waye 13 and 14

4.1K 125 5
                                    

[5/8, 8:46 PM] ‪+234 813 737 1414‬: ❤💚💙💜💛
ZAKISAN KONI WAYE
❤💙💜💛💚
®zuwairat(ummu maryam)

1⃣3⃣

Yarinyan da aka kira da Tawa ta kalli Salem taga kaman da jini hancinshi, bata ce komai ba ta nufi wani chemist dake kusa da wurin, Salem na kallonta ta cire kudi cikin apron din dake jikin ta don da alaman abinci suke saidawa awajen, ba da dadewaba ta dawo rike  da cotton wool, tana zuwa ta mikewa Abdul, ahankali Abdul yace
"Me zanyi dashi?" Yarinyan nuna Salem tayi da yatsa kafin tace
"Habo yake.." Sai lokacin Abdul ya lura da jinin dake hancin Salem, da sauri Abdul ya amshi cotton wool din yafara goge mashi hanci, har lokacin Salem bai dawo daidai ba, don tunda uwar da ta haifeshi baa taba taba mashi lafiyan jikiba, sannan daga nursery school zuwa secondary school Turkish international school yayi kuma ko kadan baa dukan yara, amman shine yau Mace ta mareshi yau, duk da yasan yana da saukin zuciya yasan he can't let this go.
Itakam ameera tana ganin yafara habo ta dauki motanta ta bar wurin Amman fa har lokacin bata bar zaginshi ba.

Abdul yafara Goge mashi hanci, shima sai lokacin Salem yasan yana nasal bleeding, cikin ran Abdul kam ji yake in shi aka mara zai fi mashi sauki sau dubu, don zuciyanshi tafasa yake kuma abinda yafi bashi haushi shine yanda Salem ya hanashi ya Koya mata hankali, Salem ya ji wata babban mace nacewa
"Tawa..na my money you use buy cotton wool?" Ahankali tajuya wurin matan sannan tace
"Zan biya ki cikin kudin da zaki bani anjuma " Mata da ganintaba mutunci kuma da alama ita Tawa takewa aiki
"Ai dole ki biyani..makulmaciya...ko wa ya kiraki oho..oya wuce ki bawa mutane abinci" nafa wayanda suke aiki tare suka fara yi mata dariya, itakam juyawa tayi wurin Salem sannan tace
"Oga sorry..Allah zai sak maka...kuma insha Allah kaima watarana Allah zai baka motan daya fi nata..." Salem tsaya kallonta yayi sannan yace
"Thank you"
"Bakomai..." Ta juya ta tafi tana cewa
"Daman masu kudi basu ganin talaka as anything... Allah zai saka mana".

Salem kallon Abdul dake ta goge  mashi hanci yayi yace
" take me to the hospital " kai kawai ya daga mashi don kunyan hada ido da Salem yake,
Cikin mota suka koma Abdul yafara tuki shi kuma Salem har lokacin hannunshi rike da cotton wool a hancinshi cos jinin ba  bar zuba ba, Abdul dan kallonshi yayi
"Sir ka kwantar da kanka baya kadan" babu musu ya kwantar da kanshi baya.

Free hand dinshi yasaka cikin aljihunshi ya dauko wayanshi, wata number da aka rubuta Nigeria head of NGO yayi dialling, cikin kankanin lokaci akayi picking tare dacewa
"Sir..good afternoon.. How is your holidays"
"Fine" kawai Salem ya amsa atakaice sannan yacigaba dacewa
"Ka turo min Pictures da details na yan northern NGO"
"Sir yaushe kake bukatanshi?"
"Right now" yana kaiwa nan ya katse wayan shi, tare da lumshe idanuwanshi,
"Allah nasan kanason in koyawa yarinyan nan hankali... Don nasan haduwata da ita ba coincidence bane destiny ne" yafada cikin ranshi.

Suna zuwa hospital aka nubashi doc yace abinda ya sameshi ya zo mashi unexpected ne shiyasa yake bleeding, ice block aka sa agaban goshinshi for a moment jinin ya tsaya sannan suka bashi magunguna.

Suna kan hanyan dawowa emails suka shigo mashi, bai budeba har suka isa gida. Suna zuwa gida ya dauki makeup remover ya goge fuskanshi nan ya kara ganin hannun ameera kwance kan fuskanshi, wayan shi ya dauka ya dauki photon fuskanshi ya turawa Khalid nan take Khalid ya kirashi
"Guy meye wannan?"
"Same yarinyan nan ta mareni..."
"What... Karshen mari kenan... She really have to be taught an unforgettable lessons.. If you are not doing anything kawai ka barni in sa aiyi maganinta.."  Ahankali Salem yace
"I have a plan... Zanbi shawaran ka..." Nan ya kwace abinda yayi niyyan yi ya gayawa Khalid, shewa kawai Khalid yayi yana cewa
"Best ko shaidan zai jinjina maka.."
"Ai friend nasan ba haka nan Allah yake ta hada ni daita ba...yanason in koyamata rayuwa..and am not let him down.." Cikin daria Khalid yace
"Yanzu zaka hakura da taxi driving ko?" Shuru Salem yayi for a moment kafin yace
"No.." Cikin zolaya Khalid ya kara cewa
"Haba ango gashi zakayi aure?" Salem katse wayan shi yayi ya dauki iPad dinshi ya ya bude emails dinshi.

zakisan koni wayeOù les histoires vivent. Découvrez maintenant