18

1.5K 86 20
                                    

1️⃣8️⃣Abinda Aka Gasa Shi Yaga Wuta

               Na

Benaxir Omar

         *NWA



Www.benaxiromar.com


Mamaki ya cikata ya kuma hanata magana lallai ya taki saa suna dakin Allah da sai ta barza masa rashin mutunci  ta mike tare da saka takalminta ta nufi hanyan shiga cikin masallaci don samu tayi dawafi   tana lura yana bayanta, salati takeyi  a zuciyanta kaman tasa hannu akai ta kwala ihu haka takeji, yana shiga hakkinta kuma wallahi da ba Ka'aba bane zata iya hakura da fitowa amma ina yayi kadan ya hanata ibada, za kuma  takara kai karansa tunda shi baya jin magana ta fatar baki, haka sukayi dawafi ras yana biye da ita  lokaci lokaci tana sashi a adduointa burinta ta juya taga ya bace,  tana cikin tunani bata ankara ba taji  an bugeta, tsantsan tsayinshi sai data daga kai tana  kallonshi sai kuka yake yana adduoi, tausayinshi ya kamata shi ko wannan meya aikata haka  yadda yakeyi tarasa hanyan kwantatawa caraf daga sama taji  mutuminta kam na cewa " kedai kam akwai tausayi ko da yake abun tausayinne sune wanda Allah yace zuriansu, yayansu tattaba kunninsu bazasu taba shiga aljanna ba" jikinta a sanyaye tana so ta tambayeshi meyasa?  laifin me sukayi haka amma gani take in tayi haka zata bashi hanyan mata magana don haka ta canja hanya aikuwa tajita cikin rundunan yan  indonesia sun taro iyalansu zasu kaita kasa su danne rikota da yayi yasa bata fadi ba dasauri tace "auzubillah" ta fauce jikinta takara saurin tafiyanta gudu gudu harta karasa, tana idarwa aka kira isha don haka tabar filin gurin tunda baa barin mata suyi sallah agun.  Ganin halin da ta shiga aranan ba shiri tabi shago tasiya liqab dinta tundaga ranan da liqab dinta take yawo, har suka fara aikin hajj suka kammala ta dawo gida don itakam harta manta dashi, haba mutum da naci kaman me, sai dai ita kadanta in ta tuna sai tayi murmushi.

           Dawowanta gida yayi dai dai da satin bikin Abdul, domin kuwa tasamu gidan acike da yan'uwa da abokan arziki kowa sai haba haba yake da ita ana murnan ganinta , Sai tajita  waras bata da damuwa ta manta da wani Jamal da Haliitansa balle su Fahad ko yana ina?,  Ko yaushe tana makale jikin Hajiyanta har aka fara taro daga gidan Amarya sunyi kamu sannan sukayi walima, Ran Asabar aka daura aure a ranan kuma zaayi dinner daredare wanda dangin ango suka hada, dama taje anmata wani gown wanda tasiyo material din daga dubai ko amaryan banjin kayanta yakai na Amrah tsada, ga wani ubansu Gwal da ya shimfida a fadddeden wuyanta, tasha gwagwaro da kwaliyan zamani masha Allah, yadda tafito rigan yayi mata cif cif saida Hajiya tace "Anya auta zaki fita haka? ji fa jikinki gaba daya awaje jeki saka ko gyale akai ko?" tayi murmushi tagane mai mahaifiyarta take nufi  donhaka taje ta nemo wani gyale mai tsada ta yaba shi a kafada, ita taja motarta ita kadanta har filin dinner , yasha Decoration masha Allah tubarkallah,  ga masu hoto ko ta ina mutum ya juya ango Amarya tazo dama ango ake jira tana fitowa DJ ya sanar da zuwan  ango da abokansa , dasauri tamike rike da purse dinta dama tayi mint din dari biyar biyar da ta casko gurin Abba,  ta nufeshi tare da sauran yanuwa tana masa manni suna dariya tace " Yaah Abdul ka ganka kuwa? kayi  kayau sosai wallahi" yayi dariya sannan yace " kema haka Allah sa bakifi amaryan tawa kyau ba"
" habawa na isa na bata mata wannan rana?"
jikinta ya bata ana kallonta daga gefensa kawai ta juya bata san lokacin da ta sake bandir din dari biyar din gaba daya ba akasa hankalinta duk yatashi nutsuwa ya bace mata duk kuma sai taji ranta ya baci, meya kawosa gurin ganin kayan dake jikinsa ya tabbatar mata da cewa  abokin Abdul dinsu ne, tana wannan tunanin DJ yakira suyi rawa yadda tasa aranta zata yi rawan ba haka tayi ba, duk taji wani iri  bata sake ba ,  Aunt Amina kanwar Hajiya ce ta lura da yanayinta ta tambayeta ko lafiya? tace mata bakomi zata je gidane, amma ta hanata acewarta Hajiya tace tabari sai zaa koma gaba daya saboda hanyan ba kyau ga dare yayi, jin haka yasa tanufi motarta kawai tashiga ta zauna ta jinginu jikin kujera Ya Allah meya kawoshi, itakam bata san ya zatayi ba dashi Allah yasa tagama haduwa dashi kenan, kamshin turarensa taji, mai sanyaya zuciya turare daya ne da wanda ta saba ji a saudi sai dai gabanta ne ya fadi, taki motsi don kar yagane tana cikin motan, bude motan yayi tare da sallama,  ya zauna agefe sannan yarufo kofan

"Ka gani, kayiwa Allah na rokeka don Allah ka rabu dani wallahi na tsaneka bana son ganinka banason abunda zai hadani dakai"

"kinyi kyau!"

takara sanya hannu ta rufe fuska cike da takaici ba tasan lokacin da hawaye yafara fito mata a fuska ba, hannunsa tagani ya miko zai riketa "kar ka kuskura ka taba ni" bai kulata ba sai da yakai gurin dankwalinta yacire mata flowern kyalkyalin decoration daya makale agurin sannan yace " kar kiyi tunanin  Matsifanki ko korana dakikeyi zaisa na rabu dake, da zanyi hakan dana dade dayi, amma kisani yayinda kike kai karana gurin Allah don ya rabaki da ni, nikuma ina kai kara gurinshi domin ya hadani dake, tabbas nayi dace, yanzu dai sai kingani  ma'ana sai nazo and don Allah kidaina yawan Fada banason wasu suna jin muryanki" yana gama fada yafita bai jira yaji me zatace ba, takaici yasa ba tasan lokacin data ja motan tabar gurin ahaka ba, gida ta nufa ko rufe kan motan batayi ba ta shige Hajiya na falo tare da sauran yanuwanta wanda basuje dinnern ba ta zube tana kuka tace " nikam  ki kira wannan commissionern police din gaskiya akwai wanda yake takurani Hajiya, tun a saudi fa, yanzi har gun dinner yabini"  Sallamansa taji gabanta yakara faduwa a zatonta tunani ne sai ji da tayi Hajiya tace " Ahhn, Amir! harka dawo ne?"

Abinda Aka Gasa Shi yaga WutaTahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon