3

1K 86 3
                                    

3️⃣Abinda Aka Gasa Shi Yaga Wuta

               Na

Benaxir Omar

         *NWA



Www.benaxiromar.com

  
    Ahaka har ta kammala a lokacin  Jamal yagama service kenan ya fara neman aiki, ganin bai samu aiki ba kuma babu alamun nasara yasa taje ta samu managern daya daga cikin gidajen man babanta ta roki alfarman a daukeshi aiki tunda business Administration ya karanta, kuma ta roki alfarman kar ya sanar da baban nata hakan kuwa akayi bugu daya Jamal yayi kudi, abun mamaki duk da yana da amana da rikon gaskiya sai Allah ya buda masa, alokacin anyi allocating dinta ta dawo kano bayan sun fito daga camp cikin wata hudu ya kera gida lafiyayya, hatta gidan da mahaifyarsa take ya canja mata duk da ciwo da takeyi sosai yau gida gobe asibiti.

           Lokacin Kammala bautan kasanta yayi daidai da lokacin da Jamal ya fara shiga da fitar da motocci na sayarwa zuwa cotono, Allah ya daukaka shi fiye da komi arayuwa yasamu rufin asiri kuma daidai da rana daya bai gaza acikin soyayyar da yake nunawa Amrah ba, asalima wani sabon shafi ya bude ganin ya samu kudade, kyaututuka da yake tura mata har inda take service, ran birthdaynta kuwa yayi kaman bai san ranan bane har ta fara fushi dashi ashe ya hada mata wani gagarumin birthday awani karamin restaurant ya gayyato na kusa dashi haka zalika cousin dinta guda daya nabila, sun ci sun sha aka yanka cake anan  aka gayyaci celebrant ta fito dan karban kyautuka da aka bata, bayan haka har zata koma taji ihun da su nabila sukeyi da sauri ta juya kawai taga Jamal akasa ya durkusa kafanshi daya ya ciro zobe diamond a aljihunshi yana mika mata, wani hawayen farin ciki taji ya zubo mata, da sauri ta mika hannunta yasa mata, suka tafa musu yayinda su mazan suka fara cewa ya rungumeta daure fuska yayi wanda tuni suka bar wannan maganan, an ci an koshi anyi rawa an watse. Da kanshi ya mayar da ita gida a mota suna tafe sai murza zoben takeyi tana murmushi ita kadai yace mata " yanzu zaki min iso gurin Abba ashirye nake na turo magabata na"  ta gyada kai tare da rufe fuskanta
"kunyar me kikeji? a duniya bani da tamkarki, kece zuciyata kece kuma gangar jikina, bani kuma da tamkarki, kin tsaya min alokacin da bani da kowa, kin zauna dani alokacin da ni ba kowa bane, don haka kisa aranki kece a zuciyata babu wata mace da zan gani da zata rinjaye ni, ina rokon Allah yabarmu tare kuma ina rokon kar Allah ya gwada min ranan da zan juya miki baya.

          Nan dai ya cigaba da tausasa mata zuciya har yaga lokaci na kurewa anan ya  juya baya yadauko wani gift bag ya bata sannan yace "Hbd my love" dimple dinsa ta lotsa yayinda fararen hakoransa suka bayyana ta kalleshi ta kanne ido sannan tace "nagode, zan sanar da baba insha Allah, ya jikin Innaji? Ka gaishe min da ita dan Allah"
" da sauki sosai jikin ma ya sauka dai amma yanzu gidan ma zan wuce" nan sukayi sallama kaman kar su rabu har ta shige gida, yana shirin kunna mota yaga wayan Fahad

"Yaya kayi sauri jikin Innaji, muna asibiti"wani wawan burki yaja da gudu yabar anguwan zai nufi asibitin, mintuna kadan suka isa dashi inda a gigice yakira wayan Fahad inda ya masa kwatancen dakin da suke. Da sauri ya bude kofan ayadda yaganta jikinsa yayi sanyi da sauri yaje ya rike hannunta, idonsa ta cika fam da hawaye
"Inna ya jikin?"
ta lumshe ido alamun tana jan jiki domin numfashinta ma dakyar yake fita
" Da sauki Baddo, ina son ka saurareni da kyau, diyar nan Ammi, ka lura da ita, ka riketa amana, karka juya mata baya, tayi mana abunda babu wanda yayi, ka aureta sannan ka dauki kaninka Fahad ya zauna agurinka har yayi aure, ban yarda ya zauna awani guri ba, ka gane? Allah ya maka albarka, ya rayaka, ya azurtaku dukkanku na yafe muku kunji?, inason ruwa dan Allah" ta karasa maganan tana tari, dasauri  yafita don debo mata ruwa Fahad na waya awaje,  kafin ya dawo Innaji ta cika
"Innalilahi wa inna ilaihi rajiun" abunda yaketa maimatawa kenan.

Abinda Aka Gasa Shi yaga WutaWhere stories live. Discover now