7

889 74 8
                                    

7️⃣Abinda Aka Gasa Shi Yaga Wuta

               Na

Benaxir Omar

         *NWA



Www.benaxiromar.com






       Sai bayan sallahn asuba bayar adduointa ta mike ta hau kan gado, karfe shida ya fara tashinta
"kinsan zan tafi office amma kina kwance?"

"kayi hakuri" haka ta mike bacci fal a idonta ta shiga kitchen har zata daura ruwan indomie ya leko yace "tuwo zaki min" haka ta canja tukunya ta daura babba, tayi mishi tuwo miyan kubewa ta jera masa a kan dinning har zata koma daki yace "zobon da kika yi ranan don Allah kimin shi" ta kalli agogo tara da rabi sannan tace "office din fa?" bai kulata ba don haka ta koma kitchen ta daura zobo akan wuta, Fahad ne ya shigo ya dauki tray ya debi dankali tare suka fere yana mata tadi, har ransa baiyi niyyan yaci dankalin ba amma ya rasa dalilin da zaisa ya zauna a kitchen din tare da ita don kar taji kadaicin abunda Jamal yake mata, haka suka fere suka soya kwan ta zuba mishi itama ta zuba alokacin har ta zuba kankara a zobon bayan hadin da tayi, ta juye a jug sannan ta kai mishi kan dinning ta sameshi sai saka loman tuwo yakeyi.

   

Dare dare kuwa karfe sha daya har ta mike ta kwanta ya shigo yace "Ammie don Allah sakwara nake son ci"
"toh barin tashi na maka" bayanta na ciwo haka ta mike ta fere doya zata dora kenan taga Fahad yafito  da jallabiya a jikinsa,
"me kuma kike yi a daren nan?"
"sakwara yayanka yake so" bakinsa a bude  ya ja kujera ya zauna sannan ya fara mata tadi, doyan ya dafu tana zubawa a turmi guda daya ya fadi mata akan hannu, ihu ta saka da sauri Fahad ya mike bai san lokacin da ya riko hannun ba, ya debi gishiri jikinsa na bari ya saka mata, hawaye ya cika idonta fal, hannun ya kumbura sumtum yayi muni, 
"kiyi hakuri ki zauna kawai barin karasa" gyada kai kawai tayi tana kallonsa ya zuba dukka doyan a turmin ya fara dakawa, har sai da
yayi lukwis ta nuna masa coolern da zai dauko haka ta lallaba tare suka kulla tasa leda sannan ta jera, dama stew din ya gama tuntuni, suna gama jerawa zata dauki tray din takai mishi Fahad yakarba tana biye dashi suka kai mishi falon ya cika fam
" meye haka kaman mace? meyasa baka jin magana ne? sau nawa nake hanaka shiga kitchen, yanzu meye na dauko tray? ke kuma na saki aiki shine zaki saka wani ko? wato ban isa ba?" ya taso yana matsifa kaman zai mareta daga ita har Fahad ba wanda yace masa uffan haka suka ajiye masa suka koma kitchen din, nan ta tattare ko ina sukayi sallama da Fahad tazo zata shiga daki taji yana kwala mata kira " Amrah meyasa bakida imani ne? kinsan bana son Ajino kin sa min a miya" ta zaro ido domin kuwa bata dashi a kitchen ma balle tasa, ta girgiza kai "sai dai doyan, saboda doyan yana da daci yasa na sa suger saboda yayi zaki amma kayi hakuri don Allah" yadda tayi da fuskanta ga azaban da hannunta ke mata na konewan da tayi, Allah Allah take ta shiga daki ko zata sake hannun  duk da cewa yaji tana ihu a kitchen yaki ya leka balle ya tambayi meya sameta, abunta yafi kuntata mata kenan.

Dakinta ta nufa ta rufe kofan ta fada kan gado, tayi kuka mai isanta, har yakai munzalin da Jamal bai damu da jikinta ba ko abunda ya sameta ba shidai in dai  HQ na nan lafiya toh shi komi ma yafaru, ahaka har bacci ya kwasheta sai kuma jinshi da tayi agefenta daredare "Ammie nah".

Abinda Aka Gasa Shi yaga WutaWhere stories live. Discover now