12

867 71 2
                                    

1️⃣2️⃣Abinda Aka Gasa Shi Yaga Wuta

               Na

Benaxir Omar

         *NWA



Www.benaxiromar.com






       Abin sai ya kasance Fahad ne mai bata abinci, ko ba abinci ba in Fahad na gurin tafi sakewa hatta iyayenta duk sai ta dunkule agefe daya tana kallonsu, yayunta Su abdul da suka dawo  ma su ma abuja suka nufa domin jinyarta alokacin Alhaji ya fara nema mata visa domin su tafi america a can ance masa akwai wani kwararren likitan kwalkwalwa  zai duba Amrah kuma insha Allah za'a dace, Hajiya ta fara koya mata alwala da sallah amma Amrah shiru babu magana balle nuna alamun ta fahimta, wani lokacin sai ta dauki butan sai taga kaman tasan abunda za tayi ko kuma ta taba yin abu kaman haka,  Fahad ne yazo ya fara koya mata alwala, haka Sallah da adduointa, duk kiyayyar da Alhaji yake ji game da Jamal ya kasa yiwa Fahad saboda Fahad yayi mishi abunda ko shi baiyi ba, akwai lokacin daya fita sallah Hajiya taje gida wanka Fahad ne yake bata abinci gwaten dankali ne yayi dadi sosai don yasha fashashen kaza aciki, tana ci tana wasa da yatsunta yana mata labari idonsa kyam akanta domin shi bayaso ya gifta ko nan da nan ne, wani amai ta kwaro shagaf ajikinsa, alokacin Alhaji na tsaye  ta window har zai shigo don a tunaninsa Fahad zaiyi Fada wa Amrah, amma yadda yaga Fahad ya gigice bai damu da jikinsa da amai din ba, tambayanta yakeyi meya sameta? ya takeji? ko yakira likita ne? in banda kallonsa da manyan dara daran idanunta ba abunda take yi , nan ma zuciyarsa ta kara karaya, neman tisue yayi ya goge mata jikinta sannan ya dubo cikin jakanta yaga wata doguwar riga ya dauko sannan ya riko hannunta yace "kije bandaki ki canja kisa wannan ko?" ta gyada kai ya rakata har bandaki sannan yadawo ya canja bedshit din ya gyra kan gadon lokacin da ta fito ya zaunar da ita sannan ya dau wayansa yakira Jamal " don Allah ka taho min da kayana agida mana, na jikina ya baci"  haka ya zauna yana kallonta ita kuma ta fara bashi hakuri ganin yadda ta bata masa jiki da amai,  Alhaji bai shigo ba yana tsaye domin kuwa yasan shigowanshi zai gigita Fahad gwara ya tsaya daga waje yana kallonsu ta glass window din, cikin mintuna kadan sai ga Jamal, ya gaishe da Alhaji amma bai amsa shi ba don haka ya shiga ya bawa Fahad sannan ya zauna agefen Amrah, kallonsa take sosai bata kyafta ido ba, tasan dai ba shine na farko daya tashi ba, amma shima yana da kyau  murmushi tayi sannan tace
"kana da kyau".
  Wani Dimm yaji aransa yaji  tausayinta na neman cika mishi zuciya, da wuri ya kawar da wannan tunanin yana mai gargadi  ransa cewa yanzu ba lokacin da zaiji tausayin Amrah bane ko kuma wani nata,ya tabbata ta fada ne har cikin ranta, ga wani matsanancin bukatarta da yakeji alokacin bai ki kowa ya watse abarshi da matanshi yayi sunnah da ita ba, Fahad ne yafito ta bayansa yana cewa
"inaga abincin ya tsaya mata ne tayi amai"
"kasan me nace?" ta katse Fahad da tambaya, ya kalleta sannan ya girgiza kai alamun a a sannan tace "yamun kyau wannan" ta nuna Jamal, Fahad yaji gabansa ya sake faduwa a karo na biyu kenan da take fadan haka, farko lokacin da Jamal yazo bai ma karaso ba daga nesa ta ganshi tacewa Fahad, Jamal ya mata kyau don haka da sauri yace " kinsan meye kyau kuwa?"
"Ae, abunda mutum yake so, ya kuma bashi sha'awa" ji yayi kaman ta zuba mishi garwashi aransa sai alokacin kuma yayi kori da shaidan daya tuna cewa fa lallai Jamal mijinta ne na sunnah, shi kuwa bai da alaka da ita don haka idan akwai wanda zaiyi kishi toh Jamal ne. Shi kuwa in banda murmushi babu abunda yake yi,  daga shi sai Allah bawanda yasan abunda yake tufkawa aransa,bai ki ta samu lafiya ayau ta koma ba duk da gargadi da mahaifinta ya masa,  yasan ayau ta koma ayau zai daketa,  har sai ya huce takaici ya kuma rama abunda akayi masa. haka zalika sai ya tabbata ya nakasa Alhaji Saed, wannan kadan ya gani akan yarsa, yasan yana sha'awan Amrah amma tsawon shekaru takwas da suka yi tare, shekara biyar soyayya, shekara hudu aure bai taba jin ko da na minti daya So ko kuma wani shakuwa akan Amrah ba, Da fari ma wacece Amrah da zai SO ta, babu wannan ittikafin labarin a tsakanin zuriyansa da zuriyan Amrah, kallon Fahad kawai yake yi, da yake sonta yake kuma kaunarta amma yasan dole ne ya raba su, bazai yiwu ya hada jini da ita ba, wannan haramun ne agareshi,  mikewa yayi yabar musu dakin cike da haushin Amrah yayinda ta fara mika hannu tana son bin Jamal, Fahad ya riko ta sannan yace "kinga! wancan ki rabu dashi, ba ruwanki da kyau dinshi yanzu damuwan ki samu lafiya ne ko? kar ki bari kyau dinshi ya rude ki" sunkuyar da kai tayi tana wasa da yatsunta sai kuma take ganin kaman tasan shi, kaman wani abu ya hada ta dashi, gabanta yayi mummunan fadi da sauri taja bargo ta kwanta.
Alhaji saed kuwa dake kallo a waje Fahad ya karo Daraja a idonsa yayinda kiyayyen Jamal har yanzu ke zuciyansa, yaki gayawa Hajiya ne domin kuwa in ta tashi ita har Fahad zata kora abunta ba abunda ya dameta.

Abinda Aka Gasa Shi yaga WutaWhere stories live. Discover now