episode 23&24

Beginne am Anfang
                                    

    Gyaran murya Nana tayi tace"Muntari maganar nan ce dole na yita, Maganace kuma da ta danganci imamu,matsar kwalla ta fara tace "muntari Nidai nasan ni na haifeka sannan kai yaro ne Mai biyayya,"Bawai ina san haɗa ka da iyalin ka bane amma da kaga abunda Ya faru dani jiya sai kayi kuka,

Wannan karuwar yarinya diyar Bulama jiya Bakaga rashin mutunci da tayi mun ba,kuma habiba na gurun haka zalika imamu, apan wa Apnan ,wallahi baka ji ɗiban Albarka ba har da cewa babu wanda Ya isa Ya hanata Auran imam ta maidashi waina sai yarda ta juyasa,

Shi yasa nikuma tunda na san wadda imam yake so tun jimawa wato Sameera shi yasa na kiraku gaku ga ita nan ayi magana a saka iyayenta a ciki ayi Auren su nan da ƙarshen wata guje ma shaiɗancin ɗiyar bulama .

    Cikin bacin rai Abbu yace"habiba maine ke faruwa."

Affan ne dake gefe yace"haba Abbu kai kasan babu wanda zai zo har gidan,nan Ya zagi Nana bamu ci,masa ba,and Wallahi Abbu ba wai ina karyata Nana bane amma wallahi Adda umaimah bata zagi Nana ba ".

    Cikin harzuƙa Nana tace"uwar Adda ba dai Adda ba,kaga muntari ni ba wannan ba ,muddin imamu yana san nayi shiru da maganar nan sai Ya Auri Sameera dan ba zamu saka ido ba Ya Auri zawarar da tayi Aure uku har da ƴaƴa uku,

Wallahi bazai sab'u ba,idan Ya sab'u kuma mutuwa nayi.

Allah Ya kiyaye,yarinya ƙwara yar shekara talatin bazawara?

Badai a zuri'a paki ba.

    A Karo na farko ummu tace"idan yana santa kuma 'fa Nana?"Mene aibun dan Ya Auri Mai yara uku,bafa zunibi bane,abu ɗaya zamu duba shine suna san juna to mene Ya rage kuma?

Cikin fitina Nana tace "ke dallah rabu dani da tunanin ku na yahudanci,imamu bazai taba Auren ɗiyar Bulama ba,sameerah zai Aura".

    A karo na farko intisar dake fama da kanta tace "amma Nana babu Ya hudanci 'dan hamma imam Ya Auri bazawara indai har yana santa sannan indai har ta ɗebo raban sa sai fa ta saukeshi,idan kika matsawa yin Allah sai kiga kamar yarda kika faɗa sai ki mutu ayi , Haba Nana kefa musulmace ,ko Kin fi san su samu rabansu ta hanyar banza?

    To su samu Mana inti,ke nifa da Ya Auri yarinyar nan gwara Ya je Chan su watse su da Allahn su sannan babu mai kawo mana ɗan zina mu ƙarba,kilan ma sauran ƴaƴan duk a haka aka same su,sannan kiji da kyau Intii tunda na kai yanzu mutuwata ba yanzu ba nayi imani da Allah ,'dan jikina na bani habiba ma sai ta rigani tafiya!

Nana ta Faɗa tana Mai faman hura hanci kafin tace"muntari ,usama ku nake jira kuyi magana 'fa."

    Ƙaramin dariya usama yayi yace"Nana wannan yasa kika kiramu dama"?

Ni dai babu abunda zance illa Abar imam Ya Auri wadda yake so,After all imam ne zai zauna da matar sa ba kowa ba Ko me kace Abbu?

Ni ganina abun nan Ai ba Mai wahala bane.

    Idanun Abbu akan paki yake wanda ke goge kwallarsa gudun kar a gani amma hakan bai hanasa gani ba.

Gyaran murya yayi yace "yanzu Nana Ya kike so ayi,"?

Kaɗa kai tayi tace"yauwa yanzu kayi magana,so nake imamu Ya Auri Sameera nan ba da daɗewa ba.

    Cikin Siririyar murya Abbu yace "shikenan Nana abunda kike so shi za'ayi".

Washe baki tayi ta dafa Sameera dake ji kamar An sata a Aljanna tace "kinji ko sameerah dama na faɗa miki ki kwantar da hankalin ki muntari ya haifu a cikina".

    "Wallahi tallahi bazan Auri Sameera ba,dana Auri Sameera gwara na mutu banyi Aure ba,wallahi bazan Aureta ba ,'dan wallahi kuka ce sai na Aureta zaku rasani, 'dan Zan mutu ne,

AURE UKU(completed)Wo Geschichten leben. Entdecke jetzt