episode 12

469 29 0
                                    

https://chat.whatsapp.com/DgTUlodRcp2AHM4rmfKTqK
AURE UKU

(a hospital romance)

         By

Chuchujay

Episode 1⃣2⃣

        Nana Mai kike faɗa haka ne ?

Kin 'fa san wannan maganar babbar magana ce!

Kallan sa tayi tana Mai gyatso baki tace "yo muntari kace na masa sharri mana kawai!"

Riyal Aini na kalli bidiyan sa da wannan shegiyar guzumar likitar suna Alfasha,

"'dan ma ina tsoran idona kar Ya lalace shi Ya hanani cigaba da kallo amma wallahi imamu ne,"

"Ina faɗa maku neman mata Ya hana yaran  nan Aure ko rashin lapia to ashe kalau mazantakar sa take zina yasa a gaba Ai wallahi imamu yaji haushin rayuwar sa Ya bata wayansa"

"Kallanta ta mayar kan ummu wadda tayi jugun tana Kallan Nana ,cikin haushin ta tace "Ai habiba baki gama tagumi ba sai Yar iskar ta kawo ciki tace nasa ne".

"Dama ni na dade da sanin baki da tarbiyar da zaki bawa yara,yanzu wa gari yawaya?"

Da Ya tashi dai bai bi munanniya ba amma fa akwai raini da taƙama.

"Shi yasa da na kama fatarta sai a na ga jini,"

Cizanta kikayi Nana?

Abbi Ya tambaya da mamaki karara a fuskarsa .

"Yo kar na Cije ta ,Ai wallahi muntari idan ka kasa saka yaran ka sukawa yarinyar nan jagajaga a cikin garin nan baka haifu cikina ba,"

Tunda shi ɗan ka Ya kasa Ya tsaya zoƙoƙo yana kalla tana mun zagi na Inna naha ya kasa cewa komai kai ka yo gaba ka ɗauki mataki.

"Ni ban san ma Mai yarinya irinta take yi a gurin cetan rai ba ,baka ga idanunta ba fiƙi fiƙi kana kallo ansha kwanan gidan maza,"

Ƙishin ɗin ma da naji gurin sameerah yarinyar nan yar Albarka wai tana da ƴara uku kuma ko wannan su a Aure guda ta samu .

"Ni ban ma yarda ba ,kar kaci mamaki Shegu ne".

Kuka kuma ta fashe dashi tana faɗin "wallahi muntari tunda uwata ta haifeni ba'a taba zagina fes kamar yarda ƴar nan ta zageni ba,

Har da kirana karya."

"Cikin damuwa irin ta ɗa idan anyiwa mahaifiyarsa Abu mara kyau Abbi yace"kiyi shiru Nana dole za'a mata hukunci ,Kin manta wanene ɗan ki ?"

Wanene ubanta ?

Idan hukuncin ya kama har shi.

"Matse kwalla tayi tace Ko BULAMA ko menene,naji dai ana faɗin dai babanta na da kuɗi wanda nasan duk kuɗin sa bazai Kai Ka ba"

"Ba dai ɗiyar Alhaji Usman Bulama bace ,ɗiyar sa kwaya daya tilo".

"Jan majina Nana tayi tace "yo idan ma itace menene abun mamaki?"

Amma gaskiya bana tunanin itace wannan daga ita har ubanta yan iskane tunda Ya haifo Yar iska take bi layi layi tana lalata mana yara.

Ummu ce a karo na farko tace "Abbi kar mu faɗa conclusion akan abunda bamu da tabbas".

Cikin balai Nana tace "conculosho,kar ki fara mana ƙaryar turanci anan 'dan Kinganki kinzo daga kasar su,"Nan muntari sai da yaga ƙarshe biro ,

Kar ki fara dani yanzu na sauke miki abinda Ya dameni dama baki san irin haushin ki da nake ji ba.

AURE UKU(completed)Where stories live. Discover now