episode 3

627 30 0
                                    

AURE UKU

   (a hospital romance)

                    By

            CHUCHUJAY.

EPISODE 3⃣

    Kallo ya bita da shi a lokacin da ta rab'a ta gefansa ta wuce baƙinta da Kalmar Sorry wanda bayan nan Kallan Arziƙi daya bai ishe ta ba,

Tab'asa yaji anyi,

Dago wa yayi Ya kalli wanda Ya dafa shi ɗin Kafun yace "guy how far".

    Murmushi guy ɗin yayi yace wa kake kallone Haka PAKI?

Yana mai tambayar nashi yana Kallan direction ɗin da yake kallo.

    Dafe ƙirji PAKI yayi yace "Rayuwata nake kallo Kb,haƙarkarina da Ya bata na tsinta yanzun nan".

Dariya KB yasa sosai kafun yace "baka da lapia gaskiya ,ka bari sameera taji labari kaga wata kana faɗin kaga missing ribs ɗinka".

Tafiya PAKI Ya fara KB na biye dashi kafin yace"tun da nake da Kai tsakanin ka da Allah ka taba ji nace maka ina san sammy?"

Ita kaɗai take haukan ta wanda Ya kamata iyanzu kuma ku sani,

She's not My type of girl,i mean guy she's just not the one.

Kasan irin taste ɗin PAKI da na daɗe ina zayyana maka to yau na ganta cikin asibitin nan and insha Allahu sai ta zama ta IMAM MUKTAR PAKI.

Bai tsaya jin Abunda KB zai ce ba yayi gaba inda kb ɗin Ya bisa a bayan yana faɗin,guy hold on ana kiran mu 'fa Cos za'ayi attaching ɗin mu da snr doctors.

"To kawai yace masa suka nufi inda sauran young doctors ɗin suke".

    Zazzaune suke cikin maɗaiɗaicin hall ɗin dake asibintin a yayin da Ko wannesu ke sanye da Farar lab coat,

    Shigowarta ba karamun sa IMAM PAKI yayi ba cikin wani yanayi na shauki,

Bai taba jin irin Haka akan Ko wacce ƴa mace ba,zungurar sa KB yayi yace abokina kar kace mun itace,

Cikin wani irin yanayin farin ciki yace"Ya kagani ta haɗu Ko?"

Ƴar karamar dariya KB yayi yace baka da lapia,bafa cikin mu take ba mutumina likitace Mai zaman kanta,sannan ka Kalleta da kyau PAKI she's off limit,a fuska ma idan ka Kalleta kasan no nonsense ce,Kai kilan ma wallahi matar Aure ce.

    Ba tare da Paki Ya ɗauke idanun sa akanta ba yace"KB jikina Ya bani ba matar Aure bace 'dan bazan taba jin yarda nake ji yanzu Haka akan matar Aure ba and da kake maganar she's off limit just look At me ,young and handsome ,sannan idan  ita senior doctor ce nima Ai kasan jan Kai ne tunda bana wasa da abunda Ya shafi Aiki ,beside saboda dedication ɗina first class holder ne wanda ba sai na faɗa maka ba,not to brag amma kai ma kasan idan magana ake ta ƴaƴan banki daga su nake,amma mutumina ba ta wannan ake ba batu ake na soyayyar ta da ta caccakar mun zuciya ,"Kai dai kawai idan mun gama abunda zamuyi anan muyi bincike akan ta 'dan Ko sunanta ban sani ba,

Ƙasa KB yayi da murya ganin Babban surgeon na asibitin Ya fara magana,yace"tana cikin hand book ni kam kamar naga hoton ta ,

And "..

Jan hannun sa Paki yayi yace "Kai yi shiru zata fara magana".

"Sunana Dr Umaimah Bulama ,surgeon ce da zaku yi aiki da,and ba sai na faɗa ba ,nasan dukkan wanda yake zaune anan yasan Abunda Ya kawo sa ,ba wai har kace ta Wasa ba saboda we are not some Artist or any sort of entertainers, we are here to save life da taimakon Allah wanda I'm sure shine aim na duk wanda ke zaune anan gurin ,idan kuma kana da wani otherwise aim to i will tell you that nan gun ba gurinka bane, So ba wasa just do abunda Ya kawoka,

AURE UKU(completed)Where stories live. Discover now