episode 4

558 29 2
                                    

AURE UKU
    (a hospital romance)
        By
Chuchujay
Episode 4⃣
BULAMA MANSION.
8:00pm
Da blank tunani Umaimah taje gida,bayan tayi parking motarta ta nufi sashen da zai kaita bangaren Alhaji bulama,
"An dawo daga karuwancin da ake fakewa da aiki kenan a bar mana ƴaƴa ratate a gida da sunan anje aiki alhalin yawan banzan ne kawai ake zuwa,ki daiyyi zuciya kiyi Aure ,Ko da yake Auren fa bai ƙarbeta ba"
Muryar saleema matar yaya Aliyu autan hajiya zuwaira Ya daki kunnenta,
Da hajiyan da sadiya matar Ya Abubakar da  Atika matar usman sai raliya matar Umar sai saleemar mata Aliyu,
Dukkansu suna zaune suna kallo a main palor wanda Hakan Ya tabbatar mata da yaran na tare da Daddynta,
Tun Kafun ta ƙarasa shigowa cikin ɗakin saleema tayi mata wannan raddin,
Takowa tayi bakinta da sallama ta zauna kan stool dake gefe guda ,

"Hajiya Ina wuni,sannu da gida"umaimah ta faɗa ba tare da damuwa ba amma tasa ar ranta yau sai ta mayar wa da saleema raddin da ta mata,

Ba tare da hajiya zuwaira ta ɗauke kanta daga Kallan da take ba tace lapia!.

Likita bokan turai an dawo kennan,
Sadiya ta faɗa wadda da ita kawai suke hirar Arziƙi sai wani lokacin raliya wadda bata cika sakewa da umaimah ɗin ba idan hajiya na nan,
Amma Atika kuwa jirgi ɗaya Ya kwaso su da saleema,

Murmushi umaimah tayi tace"wallahi yaya sadiya nasan su sultan ana chan ana damun Daddy,su Daddy Mai jikoki,"Gashi dai nawa uku,gurin yaya Abubakar Ga sultan ,sultana ga kuma Hameed ,gun yaya Usman ga ibi Ga rumaisah,
Gun yaya umar ma ga sayyid ga na ciki ,gurin yaya Aliyu ne dai ba motsi Ko sai yayi ta biyu kilan juya Ya samo bamu sani ba,tunda har yanzu ta kasa aje yaran ratata.

Ciƙe da balai saleema tace "uban wane Ya faɗa miki ana wa mutum gorin haihuwa,?"Hajiya kina jinta Ko ,gorin haihuwa 'fa take mun kuna jinta.

Tashi tsaye umaimah tayi tace"inji uban da yace kiyi mun gorin zaman Aure".

Bata jira jin mai hajiya take kokarin faɗa ba ta miƙe tayi ciki tana Mai faɗin gobe dan Allah idan kin ganni ki sake sakar bakin ki da bashi da gashi,nonsense.

Koda ta haɗo kan yaranta ta kofar baya suka bi 'dan bama tasan abunda zai sake haɗa su,

Zama tayi kan kujera Abdallah na kan cinyarta yana ta zuba mata surutun sa wanda galibi hirar Adda diya ne, kallan nadiya dake fama tutura baki tayi tace "lapia diya kike ta faman turo baki "

Kuka tasa kamar tana jira tace"wallahi mami ni gidan Dada (kakar umaimah)zani na gaji da zaman gidan nan ,kullum cikin cin zalina hamma NAMEER yake yana kuma Kallan yarda hamma sultan ke ji da Adda sultana da hameed,amma ni ina yin abu zai buge ni ,kowa a gidan nan haka suke mun hamma sultan ne kawai bai mun Faɗa nidai mami nagaji,"Haka jiya hajiya ma cemun tayi wai ni da hamma NAMEER da Abdallah baban mu ba ɗaya ba kuma wai baban Abdallah barawone ɗan shan jini,
Koma mami ba yau ta fara faɗa ba ni bana so .

Wani iri umaimah taji a zuciyarta jin abunda nadiya ta faɗa ,dole zata ma tufkar hanci 'dan bazai taba iyuwa ba ace ana faɗawa yaran ta magana irin wannan.

NAMEER '
Ta kwalawa nameer wanda Ya wuce ɗaki kira tayi dan yasan dama nadiya sai ta kai ƙararsa .

Na'am mami'
Ya faɗa yana Mai fitowa falan,

Zama yayi yana faman zare ido,
Kwantar da muryarta tayi cikin murya wadda uwa ke koƙarin jan ɗanta a jiki tace""Nameer Mai yasa kake dukan nadiya?
Mai yasa ba kasan na zauna lapia When kaine babba amma kaine ka kasa jan kannen ka a jiki ,kana so kace mun idan Abdallah ya Kai duka shima zaka dake shi Ko?

Haba nameer why Are doing this to your mother you're 11 years old for GOD sakes,
Dawowa tayi kasan da yake zaune ta zauna ta jawo hannun sa tace "nameer ka ma mamin ka magana maine yake damuka?"Why Are you always this bitter.

AURE UKU(completed)Where stories live. Discover now