Nima ina Tare da kai Hamma imam ,i will support you and we will beat Nana to it,

Muryan Afnan yayi echoing  cikin ɗakin a yayin da yake shigowa ciki,

    Kallansa imam yayi yace "lab'e ka koma kai kuma?"

Takowa ciki yayi yace"Ba lab'e ba nake bafa ,i Just got to overheard something and yau Brother's night ne shiyasa nima nazo a yi dani,

Sai a lokacin suka kula da pillow ɗin dake hannun sa,dariya suka sa a yayin da Ya shigo cikin yana Mai darawar shima,a haka sukayi ta hirar yaushe gamo har bacci Ya daukesu ".

******

Washe gari kamar yarda Iyalan Paki suke karin kumallo a yau ɗin ma haka ne,sai dai a wannan karan baki ɗayan su ne suka hallarta ciki kuwa har da sameera yar karo wadda ke ta faman shishigin ganin yan uwan Imam sun karb'eta dan yarda Nana ta saka mata Auran imam gani take kamar ta Aure sa an gama,

    Hatta Abbu da bai gari sai da Ya amsa shamacin Nana,

Bayan addua babu abunda kakeji na surutu face karar cin abinci,bayan sun gama  Nana ta miƙe tana Mai faɗin"kowa Ya sameni a babban falo ".

Babu musu kowa Ya hallarta duk da kuwa sun san sarai rigimace,

Zama tayi ta ɗora kafa ɗaya kan ɗaya Kafun ta kalli Afnan tace "ke tashi kije ki kira sameera Ya Ana zama na ahali zata ware kanta?.

    Wani irin kallo Afnan ta mata kafun tace "bana tuna lokacin da kika haifi Daddynta ko mummynta,"

Tsawar da Abbu ya daka mata ne yasata tashi zuwa kiran Sameera tana Mai jin haushi,

    Gyara zama usama yayi yace "Amma Abbu banga inda maganar Afnan tayi rashin dai dai ba,Nana fa taso mu tayi ta katse mana dukkan wani aikin da muke Mai amfani ta kawo mu nan dan yin magana mai muhimmanci,mene na sako wata sameerah?

Wacece wata sameerah ma?"

Cikin fushi Nana tace"uwarka Habiba mara ɗa'a ɗinchan ce Sameera usama,"Nace maka uwarka habiba.

    Duk yaran gidan babu Mai fushin usama dan muddin Nana ta zagi Ummu gabansa baya b'ata lokaci wajen nuna fushinsa,cikin fushi Ya tashi yana Mai faɗin"Nana nazata komai Ya chanza shekara talatin da shida kenan fa!

Yakamata ki gane a yanzu da baya ba ɗaya Bane ,a da muna yara bamu fahimta,yanzu kuwa Ummu na da yaro Mai shekara talatin da shida idan baki ɗaga mata ƙafa dan komai ba kya ɗaga mata dan yaranta,babu yarda za'ayi muji daɗi muna zaune kina aibata mana uwa.

    Baki tab'a kaunar ummu ba kamar ta kashe miki wani,Mai tayi miki?

Babu 'fa abinda ta tab'a miki illa zuri'a da ta bawa yaran ki,menene laifinta?

Gaskiya bana jin daɗin irin abunda kike yiwa Ummu Nana .

    Kallan Abbu wanda yayi shiru yayi yace "kayi mun afuwa Abbu akan abunda na faɗa sannan ni Zan wuce dan na bar aiki sosai a company na dan Kafun nazo nan ma meeting biyu na ɗaga."

Ya juya zai bar falon Ya jiyo muryar Nana tana Mai faɗin"ɗan kundun uba Mai shegiyar baƙar zuciya Ya ta kakan sa,Ai sai kayi hakuri ka dawo muyi abinda ya kawo mu sannan indai Habiba ce Zan yi ƙokari naga ban faɗi abu mara daɗi ba akan ta har ka juya kuntacce."

    Usama ka dawo ba!.

Muryar Ummu wadda taji daɗin tsaya matan da yayi ta Katsesa,

Dawowa yayi Ya zauna yana Mai faɗin "Allah yasa shima zaman ba wani rigimarki bace".

    Yana ƙare maganar Sameera ta biyo Afnan,gefe Nana ta nunawa Sameera tace"zo zauna yarinyar Arziƙi,"

Babu musu kuwa ta dawo ta zauna.

AURE UKU(completed)Where stories live. Discover now