Hurriya - 15

1.4K 30 6
                                    

Salame na turo number Malamin Hajiya Fatee ta kira shi a waya, suka gaisa ta fada masa abubuwan da suka faru ya jajanta mata, ya kara mata da cewar shi ma layinsa aka rufe shiyasa bata ji shi ba. Hajiya Kaltume ya karba suka gaisa sannan ta dora masa da banin abun da ya sami Hajiya Fatee, daga karshe suka yanke ranar da zai shigo garin. Sannan Hajiya Fatee ta iya fita dakinta ta samu ruwan tea ta sha domin bata iya cin komai. Hajiya Katume bata jima a gidan ba Fadeel ya shigo gaishe da mahaifiyar, da zai fita Hajiya Kaltume ta bukaci ya sauke ta gida.

***    ***   ***

Ba kadan ran Momy ya ba ce ba, jin cewar Captain ya zo gidan tana bachi, kuma ya fita da bacin rai saboda Hurriya.

“Oh to wai miye na siya mata gilashin ma?”

Namra ta aje spoon din hannunta.

“To nidai ranar da ya zo last na ganta da shi cirko cirko, gilashinta a kasa tana lalabe to shi ne yau take fada min ai marinta yayi saboda sun yi karo”

“Ai gara da mareta ma, yarinyar nan bata da hankali, sannan yanzu ya zo ta ki ta karbi box din wata kila ba zai sake dawowa gidan nan ba kuma, ta ja min ya fara fushi da ni kenan”

“Shi ma fa Captain din nan ya cika zuciya ga zafin hannu, amman dai bata kyauta ba da bata karba ba”

“Bar yar iska bata san su waye iyayensa ba ne shiyasa, shi ma dai miye na kawo mata glass ko makancewa ta yi iya ruwansa”

“Kila ya ga be kyauta ba, ko kuma...”

Momy ta kalleta da duba kyama.

“Ko kuma me? Allah ya kiyaye ai ko mata sun kare duniya Captain ba zai yi komai da wannan yar tatsitsiyar yarinyar na duka ma nawa take shekaranjiya ta yi 16yrs fa, kuma shi da yake da matar da zai aura”

“Toh ba sai idan anyi auren ba, wannan me bakar zuciyar? Ba kowa ce zata iya zama da shi ba”

“Ai ko fasawa aka yi sai dai ya aureki, daman Hajiya Turai ta so a hada wannan zumunci shi din ne ya ki, kuma kin san basa masa dole ”

“Ni”

Namra ta nuna kanta domin bata taba jin makamacin haka daga bakin Momy ba.

“Ke fa mun sha yin maganar da Hajiya Turai ai, amman shi Jameel din ne be yarda ba, yanzu dai ya samu wadda yake so an huta”

Namra bata ce komai ba ta maida idonta kan abincin da take ci tana motsa shi a hankali kamar mai tunani. Momy kuma ta tashi daga dinning din tana ta masifa saboda Namra bata tasheta daga bacci ba.

“Kiransa zan yi yanzu Allah yasa ya daga, kar wannan yar filfilwar ta jazamin masifa ni Nafisa”

Nan ma Namra bata ce komai b ta cigaba da motsa abinci tana tauna wanda yake bakinta ta kasa hadewa sai tunani take. Kamin ta juyo ta kalli falon da aka bude, Hurriya ce ta shigo kanta ba dankwali rabin kan nata a tsire.

“Yi sauri ki dauki abun da zaki dauka ki fice kamin Momy ta fito, dan na san sai ta miki fadan kin karbar box din da Captain ya baki”

“Abinci zan zuba”

Ta nuna abinci tana kallon stairs gabanta sai tsananta faduwa yake.

“Zo ki zuba”

Ta nufi dinning din da sauri ta dauki plate ta zuba abincin mutum biyu ita da Hamad ta saka naman kaza a sama ta dauki spoon biyu ta saka.

“Ke da Hamad zaku ci?”

“Eh”

“Dazun shi ya hana ki karbar glass din ko?”

Du hast das Ende der veröffentlichten Teile erreicht.

⏰ Letzte Aktualisierung: Oct 20, 2023 ⏰

Füge diese Geschichte zu deiner Bibliothek hinzu, um über neue Kapitel informiert zu werden!

H U R I Y Y AWo Geschichten leben. Entdecke jetzt