Hurriya - 12

470 31 4
                                    

Musib ya aje ma Captain keys din motar Momy da ta bada umarnin a dauko masa. Kallon Keys din yayi sannan ya mika hannu ya dauka ya mike tsaye. Tsabar bacin rai zuciyarsa har zafi take kamar zata fashe, baya jin yana da sauran wata magana a yanzu kuma baya bukatar yi ma Momy sallama bayan an bata masa tayun mota a gidanta. Shi ya fara fita sannan mahaifiyarsa ta bi bayansa Momy da Musib suka biyo shi suna ba shi hakuri kamar su suka masa laifin shi dai be ce uffan ba ya matsa key hannunsa motar ta fita key ya sannan ya nufita har suka bar gidan kalma daya bata sake fitowa daga bakinsa. Ran Momy be yi dadi ba ganin ďan ďan'uwanta da take ji da shi ya fita cikin bacin rai.

“Ni abun nan ya ba ni mamaki, wai waye yayi wannan aika-aikar”

“Zai wuce Kaltume? Ai bata son kowa da alheri a gidan nan kuma ta ga mota mai tsada ina za so haka, ballantana fitowar nan da ta yi dan uwa ko daya be je ya mata barka da fitowa ba”

“Amman Momy Yasir dai ba zai yi haka ba kin san ko da ta saka shi”

“Su matan fa? Kuma shi ma ba munafurci ba ne da nuna soyayyar ido, ai ta ciki na ciki dan'uwa be taba son dan'uba ba har abada”

“Ko kuma ta aiko wani yayi ba”

Ta juyo tare da Musib suka shigo falon, ko zama ba su yi ba motar Appa ta faka a harabar ya bude ya fito ya shigo cikin falon fuska a dauke.

“Ku ba mu guri zan yi magana da mahaifiyarku”

Appa ya fada immediately after ya rufe kofar falon, Musib ya dubi Miwan sannan suka tashi suka haura sama, Momy kuma ta zauna ita ma nata ran a bace tana sauraren da wacce Appa ya zo.

“Nafisa ina son na tambaye ki, akwai laifin da Hurriya ta yi miki ko kuma Hamad?”

“Wani abun aka fada kuma?”

“Akan wani dalili zaki nemi banbanta su da sauran yayanki? Fada min banbanci dake tsakinsu da Namra ko Miwan, dukansu ba Yayana ba ne? Akan wane dalili zaki ce Hurriya sai dai ta share dakinta da kanta kuma idan zata hau stairs ko ta sauka ba ta hau kamar yadda Namra ko Musib suke yi ba?”

Momy ta rike baki.

“Oh Allah na ni Nafisa, yaushe aka yi haka? Kuma shi kenan daga fada maka zance karya da gaskiya sai ka hau ka zauna har da zuwa gurin fada ba tare da ka tsaya ka bincika ba? Shiyasa ka dauko su ka kawo min? Me yasa ba a kaiwa Kaltume ba? Ita da yake tsoronta kake sai Nafisa da aka raina itace mai dadi hawa, gashi sai mulki take mana ciki gidan ita da yaranta”

“Daga ke har ita karkashin kulawata kuke kuma karkashin ikona, dan haka duk gurin da nake ra'ayi a can yarana za su zauna, kuma ina gargadinki wannan ya zama na karshe da zan sake jin wani abu marar dadi akan Hurriya da Hamad, zan iya canja mata ban zanja yaya ba, gaba daya yarana babu na yarwa kuma bana son a batawa kowa”

“Eh amman ai ka ware wadanda kake so kake kauna, na tabbatar da nawa yayan Kaltume ko Iyami take yi ma wani abu ba zaka yi magana ba, amman da yake yayan mowa ne ai gashi nan ka shigo falo cikin bacin rai saboda an taba yan gold, ni da zaka nuna musu kauna ka dawo da uwarsu ai da duk yafi wannan nema musu yanci da kake, idan ya so sai ta rike yayanta na rike nawa”

“Abun da na ga damar aiwatarwa shi zan aiwatar, babu mai fada min gabas, na san Allah, daman ke haka kike banta zuwa da wata magana ba ki musa min ba, ban taba fada kin yi shiru kin saurareni ba sai kin fada, sa'insa da ni ba yau kika fara ba, daga ke har Kaltume babu wadda nake jin sanyinta kowacce ku da lagon da take matsawa ta bata min rai”

Momy ta fashe da kuka domin kalaman Appa sun mata zafi, ta san abun da Appa ya fada akam Iyami gaskiya ne, domin ya saba yi mata fada ko a gabansu kamar yadda su ma zai iya musu a gabanta ko kuma ya tara su gaba daya yayi musu fadan idan wani abu ya faru, su kan tanka shi su kare kansu ko maida martani amman Iyami bata cewa idan yana fada har yayi ya gama, ko daga kai ba zata yi ta kalleshi ba, wannan ta saka suke yawan yi mata kallon munafuka, hawaye shar Momy take yi daman kuma bata gama hucewa daga bacin ran abun da aka yi ma Captain ba.

H U R I Y Y Aحيث تعيش القصص. اكتشف الآن