HURRIYA -03

573 38 2
                                    

☆❁ 𝗛𝗨𝗥𝗜𝗬𝗬𝗔 ❁☆
                 

𝐁𝐲   𝐊𝐡𝐚𝐝𝐞𝐞𝐣𝐚 𝐂𝐚𝐧𝐝𝐲

𝗣𝗮𝗴𝗲 3️⃣

“Amma I'm sorry laifin fa duk na Hamad ne shi ba a masa magana ya ji”

Amma ta dago da idanuwanta da suka kumbura ta kalleta.

“Ke ai kina ji? Kuma ke ce yayarsa ki daina biye masa mana, ki zauna lafiya da dan'uwanki dan Allah, kullum ina fada muku haka amman baku ji, Hurriya ki daina biye masa kina kallon ba sonku ake a gidan nan ba, a madadin ku so kanku kullum sai rigima da junanku”

Amma na magana Hurriya na yawo da idonta akan akwatunan da suke tsaye gefen kofar dakin da bata lura da su ba sai a yanzu.

“Amma kayan miye a akwaitinki?”

“Tafiya zan yi”

Hurriya ta dubeta da sauri tana kallonta da ya kumbura sosai.

“Amma ina zaki je?”

“Gida zan koma gurin Gwaggo”

“Saboda me?”

Amma ta yi murmushi hawaye na sauko mata.

“Hurriya abincina ya kare a gidan mahaifinku”

“Kamar Yaya? Toh ba sai ya kawo wani ba? Amma me ya faru kika yi kuka? Me yasa zaki tafi?”

Amma ta rufe ido ta dantse baki.

“Je ki kira Hamad”

Hurriya da bata gama fahimtar abun da yake faruwa ba idonta ya cika da hawaye har ya zubo ta kasan gilashin da shi ne rayuwarta. Ta mike tsaye ta fice daga dakin kamin ta isa dakin Hamad ta cire hijabin dake jikinta ta rike a hannu tana tafe tana hawaye har ta isa bakin kofar dakin. Murda kofar dakin ta yi ta tura ta shiga, Hamad dake sanye da short yana kokarin cire safar kafarsa ya kalleta.

“What? Amma ta miki fada ko? That's good next time sai ki sake shiga min hanci”

Ya fada azatonsa Amma ta yi mata fada ne sosai, daman haka take sometime idan aka yi mata fada kuka take.

“Ba saboda haka ba ne, Amma ta ce na kira ka kuma kuka take yi, ban san abun da aka yi mata ba”

Be tsaya ya karasa cire safar daya ba ya sauko da kafar ya biyo bayan Hurriya da tuni ta juya bayan ta isar masa da sakon Amma. Hamad na shiga dakin ya karasa inda take zaune ya zauna bakin gadon babu abun da zuciyarsa take nuna masa sai fadan da suka yi da Hurriya.

“Amma saboda Hurriya ne ko?”

Amma ta share hawayenta ta kalleshi, sannan ta kalli Hurriya ta mika mata hannu. Hurriya dake tsaye jikin kofar dakin ta karaso da sauri hawaye na sauko mata ta kasan gilashin dake idonta. Amma ta kama Hamad ta dauki hannu Hurriya ta dora a saman hannun na Hamad.

“Dan Allah ku zauna lafiya, ku so junanku ku kaunaci junanku, kai baka da wata yar'uwa da ta fi Hurriya, Hurriya ke ma baki da wani dan'uwa da ya fi Hamad, wannan yawan fadan da kuke yi ku daina anyi ance da rashin bawa juna girma duk ku aje shi a gafe, musamman ma kai Hamad idan baka canja wannan hallayar ba zaka sha wahala a gidan nan kana kallon yadda kake rayuwa ma yanzu balle kuma idan bana nan”

“Amma ina zaki je?”

Hurriya ta tambaya daman ta kagu ta ji domin hankalinta yayi matukar tashi akan hawayen da ta gani a idon mahaifiyarta ga kuma tufafinta a shirye. Amma ta kalli Hurriya sai ta rasa ta ina zata fara amsa mata tambayarta, at her age it's too early ta fada mata sakinta mahaifinsu ya yi, ita kanta kalmar tana mata nauyin furtawa a yanzu balle kuma yadda ƴaƴanta za su ji idan ya sauka a kunnesu har su fahimta.

H U R I Y Y AWhere stories live. Discover now