Hurriya -09

394 25 0
                                    

Hurriya na shiga falon Hajiya Kaltume ta fara rabon ido ganin yadda kowa yayi jigun, wasu daga yayanta kuma suna amsa waya suna kuka. Gurin da ta tafi wayo ta nufa wato gurin yayanta ta tsaya kusa da shi tana kallonsa har ya gama wayar sannan ta ce.

“Yaya wai garkuwa aka yi da Hajiya?”

Kamin ya bata amsa Khairi ta watsa mata harara.

“Tsohuwar munafuka, hala dadi kika ji?”

“Dadi dai? Me ye abun jindadi a ciki da har zata ji dadin? Wace irin magana ce wannan?”

“Toh Yaya idan ba haka ba, me yasa take tambaya?”

“Bata da hakkin sani ne? Ni kuna bani mamaki a gidan nan Wallahi, miye laifi a ciki idan ta tambaya? Karki bata min rai yanzu na fara dukanki”

Yasir ya karashe maganar yana nunata da yatsa, sai ta dauke kai domin ta sani sarai zai iya, ba wani jutuwa suke da juna ba. Ya dubi Hurriya dake gefensa tsaye.

“Eh sace ta aka yi, mu ma yanzu Appa ya zo mana da maganar sun ce za a ba su miliyan dari”

A take hankalinta ya tashi, tana son ta sake cewa wani abu tana tsoron kar Khairi ko Salma su kwatseta, dan haka ta ja bakinta ta yi shiru tana cigaba da sauran yadda ake ta kiran yan'uwa ana fada musu.

****       ****         ****

A haka sai da Hajiya ta kara sati daya a hannun mutanen nan ita da Hajiya Fatee domin police aka saka a lamarin su kuma suka hana a aika da kudin, suka ce za a gano inda take, sai da Appa ya ga abun na su ba mai yi ba, ga hankalin yaransa da yan'uwan Hajiya Kaltume ya tashi ya nemi sassauci suka rage kadan ga miliyan dari, a sake neman sauki, daker da addu'a da sudin goshi aka samu suka sauko a miliyan goma, bangare Hajiya Fatee ma haka suka karba, Appa ya hada kudinaka rasa wanda zai kai, sai da wani kanen Hajiya Kaltume yayi jihadi yace shi zai tafi kai musu kudin, ranar da zai tafi suka fadi inda zai tsaya a dajin su zo su tafi da shi, haka kuwa aka yi Fadeel ya kawo nasa kudin aka hada da na Appa suka shiga mota aka kaishi har inda suka bukata suka fito suna masa addu'a, su kawo wajen gari suka tsaya. Ba zan wani jima ba suka kira suka ce aje a dauke ta a wata gona dake nan dogon dutse a nan za su aje su. Abun ka da mai nema Yasir da Fadeel da Uncle din Fadeel din suka nufi gurin da moto suna gudu kamar ba za su je su same su a gurin ba. Kamin su isa kowannensu hankalinsa ya tashi kuma zuciyarsa ta cika da zullumi, domin suna tsoron kar su je su tararda gawarta domin sun saba haka wani lokacin sai su ce aje a dauka sai an tafi a tararda mutum a mace.
A bakin titi suka faka motar suka fita suka shiga cikin gonar domin dubawa, Yasir da waya a kunne yana fadawa Appa sun isa gurin Appa kuwa sai gargadi yake masa.

“Yasir ku kula da kyau, zai iya yiyuwa dabara suka muku saboda idan kun shiga gurin su sace ku”

“Aka yi mana Addu'a Appa In Shaa Allah babu abun da zai faru, fatanmu dai a samu Hajiya da rai”

Yana rufe baki ya ji muryar Fadeel yana fadin ya karaso nan gasu a nan, da sauri Yasir ya katse wayar ya nufi gurin, Hajiya Fatee ce da Hajiya Kaltume daure jikin itace, kansu babu ko dankwali sai wani zane atamfa kala daya da suka yafa kamar wasu yan kauye sun yi yaushi kai kace allayahun da yayi sati ne a daure, fuska ta yi burun-burun kana ganin kasan an dade ba a sadu da ruwa ba, baki ya bushe idanuwa sun kode kamar wadanda suka kusa kusantar rame. Hajiya na ganin Yasir ta fashe da kuka, Hajiya Fatee kuma ta fara zubar da hawaye.

“Alhamdulillah Alhamdulillah”

Shi ne abun da sukr ta fada bayan sun kwance su.

“Ku yi sauri muje kar su biyo sawunmu, Sannu Hajiya”

Fadeel ya fada yana kallon mahaifiyarsa cike da tausayawa.

“Bana iya tafiya Fadeel bana iya komai”

H U R I Y Y AWaar verhalen tot leven komen. Ontdek het nu