HURIYYA -04

542 40 1
                                    

“Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un”

Shi ne abun da Hajiya Binta take ta nanatawa idonta a rufe domin danta be zo mata da labari mai dadi ba, a cikin matansa daga wanda ta rasu har wadanda suke a gidansa yanzu babu wanda take so irin Iyami, domin macece wadda ta san kanta take bata girma take rawar jiki da ita tana kyautata mata kamar uwarta.

“Subhanallahi Tsoho baka kyauta ba, ka yi gaggawa kuma daman gaggawa aikin sheidan ne, ina ma baka aikata ba ka dan daga mata kafa ko kuma na turata gidansu har sai ka samu natsuwa”

Cikin wani kalar rauni da rashin sukunin abun da ya aikata ya sake noce kansa kasa ya sauke ajiyar zuciya.

“Hajiya natsuwar ce ta gagare ni samu, ba yau na fara jin bana da sukuni idan bana tare da Iyami ba, ji nake kamar wani abu ne a saman kaina, sai a yanzu da na sauwake mata sannan na ji nauyi ya sauka, ni kaina ina son Iyami amman bana jin natsuwa a zamantakewarmu yanzu, kuma na yi ta addu'a ina fatan samun sauki abun amman hakan ya gagara wata kila sakin shi ne mafi alheri daman aure rai ne da shi”

“Har saki nawa ka yi mata tsoho?”

“Daya na yi mata Hajiya”

“To da sauki idan abubuwa suka daidai wata kila za a iya gyarawa, ko dan yan diyanta Tsoho, dubi Hurriyya da Hamad ga cikin dake jikinta yaran nan ba za su taba jindadin zama a gidan idan bata ciki ba, ko ma kallon iyayen kowa na nan ta su bata nan sai ya saka su jin wani iri”

“In Sha Allahu zan ba su duk wani jindadi da farinciki da yaya suke bukata a gurin uwa da uba, ban taba fadar maganar nan a gaban kowa ba sai yau a gabanki, Hajiya duk cikin yayana na fi kaunar Hurriya, saboda kokarinta ga kuma lalurar da take tare da ita, Allah ya saka min tausayin yarinyar nan, fitowa daga gida zuwa nan Wallahi yaran nan kawai nake ta tunani a raina”

“Tsoho”

Ta kira sunansa sai ya dago ya kalli mahaifiyarsa da fatar jikinta ta fara zazzaga saboda tsufa.

“Dan Allah idan ka samu sukuni ka dawo da Iyami dakinta, ko ba komai ta saba da rayuwar jindadi ga kuma ciki ga tunanin yaranta be kamata ka saka mata da haka a irin wannan lokacin ba, idan ma baka yi hankali ba tana cika idda wani zai dauke ta mace mai kyau da kurciya haka nan, ka kusan haihuwarta fa amman tana zaune gidanka gwanin sha'awa ga girmama mutane yarinya mai hankali da tarbiya”

Ajiyar zuciya ya sauke mai nauyi.

“Hajiya ban sake ta sai da na bata kyauta gidana da yake samaru, kuma na bata kudin da zata iya rike kanta da su naira miliyan ashiri, kuma babu abun da zan karba daga kyautar da na taba mata, kayan dakinta da komai ma gobe zan saka a kwashe a kai mata har gidansu, wata kila dai zaman auren ya kare gaba daya, dan Allah karki cilasta ni aikata abun da zai hana ni samun natsuwa ki yi mana addu'a kawai”

“Toh Tsoho Allah yasa hakan shi ya fi alheri, ya kawo mafita a tsakaninku”

Hajiya ta fada muryarta na rawa hawaye na cika idonta har suna kokarin zubowa, mikewa ta yi tsaye ta shige dakinta ta bar shi a katon falon dake cike da sanyi ac. Hannu ya saka ya dage kansa yana jin wani karin rashin natsuwar da bakinciki na kusanto shi, ada yayi tunanin idan ya rabu da ita zai samu sakewa, sai dai bakinciki rabuwa da ita ba dan zuciyarsa na so ba, da kuma tunanin damuwar da yaransa za su shiga ya hana shi samun natsuwa, arzikinsa daya a yanzu ya daina jin wannan nauyi da yake ji a lokacin da yake tare da ita. Ya dade zaune a cikin falon kamar wanda ya rasa makama sannan ya tashi ya fice yana gyara babbar rigarsa. Yana fitowa direbansa ya fito ya bude masa motar ya shiga ya maida kofar ya rufe sannanya zagaya ya shiga mazaunin tuki ya tashi motar suka fice daga gidan, kamin ya isa gurin da yake gudanar da kasuwanci kiran Bappa ya shigo wayarsa ya fi a kirga amman yaki ya daga saboda ya san maganar Iyami za su yi masa.

H U R I Y Y AWhere stories live. Discover now