HURRIYA -01

1.1K 56 6
                                    

☆❁ 𝗛 𝗨 𝗥 𝗜 𝗬 𝗬 𝗔 ❁☆
                 

𝐁𝐲   𝐊𝐡𝐚𝐝𝐞𝐞𝐣𝐚 𝐂𝐚𝐧𝐝𝐲

*©®Hakkin mallaka nawa ne ni Khadeeja Candy, ban yarda a sarrafamin labari ta kowace siga ba balle har a dorashi a Website ko YouTube ba tare da izinina ba, yin hakan kuskure ne babba domin zai iya janyowa mutum matsala saboda haka a kiyaye ⚠*

Wannan Littafin Sadaukarwa ce ga.

Zainab A Baba Abokiyar Hira.

Asma'u Badamasi Bauchi

And
Hafsat Muhammad Betuwa Maman An-noor

i appreciate your love 🥰❤

H U R I Y Y A -Labari ne mai ban tausayi da taɓa zuciya. Story of the 2nd October 2023

𝐑𝐚𝐧𝐚𝐤𝐮𝐧 𝐏𝐨𝐬𝐭𝐢𝐧𝐠 𝐌𝐨𝐧𝐝𝐚𝐲 𝐓𝐮𝐞𝐝𝐚𝐲 𝐖𝐞𝐝𝐧𝐞𝐬𝐝𝐚𝐲 𝐓𝐡𝐮𝐫𝐬𝐝𝐚𝐲 𝐅𝐫𝐢𝐝𝐚𝐲.

Idan kina da wani abun da kike so a tallata miki you can chat me on 08036126660 or https://wa.me/qr/3D4THFJXLUGTM1

Bismillahi Rahmanin Rahim...

𝗣𝗮𝗴𝗲 1️⃣

Babban gidan sama ne mai dauke da bangare biyar, na farkon da na biyu zuwa na uku da hudu sukansu suna facing din babban gate din gidan. Yayinda dayan wanda shi ne na biyar yake dama da part din hudun, dukannin part din suna da karamin gate da zaka iya hango wanda zai shiga ko ya fita, haka zalika ko wane part yana da gurin aje mota kamar uku sai kuma karamin filin da za a iya wata hidimar idan da bukata. An kawata kowane entrance na parts din da fulawowayin na kasko, a ko wane bangare akwai kujeru da aka tanada domin hutawa ko shan iska.

Babbar harabar gidan wani katon fili ne da za a iya gina kananan gidaje hudu ko biyar, ko wace kusurwa da ginin na jikin gidan an dasa masa dagayen itatuwa, tsakiyar compound din kuma an yi masa round da flowers. Ko masu gadin gidan kadai ka kalla ka san ba kananan kudi suke samu ba, balle kuma ka sauke idonka akan manyan  motoci da aka jere a harabar da aka tanada domin aje motocin Alfarma, bayan mota biyu wasu daya wata uku da suke aje a kowane bangaren uku da suke gidan.
  End of discussion shi ne sunan da mafi akasarin jama'ar unguwar suke kiran gidan da shi, ba a unguwar Millions Quarters ba kawai, kusan duk wanda yake cikin garin Gusau ya san gidan Alhaji Haruna Mai Yadi, saboda yadda jama'a suke yawan labarin gidan da irinsa a rare a garin Gusau. Kasancewar ba kowa yake damuwa ya gina gida mai kyau da fasali kamar yadda shi ya zabi ya bayyana nashi arzikin ba a fili ba.

A cikin part hudu da suke gidan uku ne suke dauke da iyalai yayinda dayan da ya banbanta da saura kuma ya kasance na Alhaji Haruna Mai Yadi, part din farko na Hajiya Kaltume ne uwargida ran gida, wato Uwargidan Alhaji Haruna a yanzu, sai mai bi mata Hajiya Nafisa da ake kira da Momy, sai ta ukunsu wadda ta zama turmin tsakar gida hausawa suka ce sha luguden mahassada wato Hajiya Iyami ake kira da Amma. Dayan part din wanda shi ne cikon na hudu, part ne da ba a taba zamansa ba, kasancewar matansa uku ne a yanzu tsabanin hudun da ya ci burin yi.

A kowane part akwai dakin yara na maza dabam na matan dabam, akwai sitting room har biyu karami da babba, sai bedrooms din ko wace mata dake dauke da mayan furnitures na alfarma, dukannin furniture din parts din iri daya ne sai dai kala ta banbanta. Na dakin Hajiya Kaltume red color ne tun daga kan kayan dakin kujeru har zuwa curtains dinta, sai dai an yi musu ado da ratsin golden hakan ya kara musu kyau gashi yaranta na taya ta gyara bangarenta kasancewarsu yan mata masu wayo da son kwalliya domin yan matanta hudu, Umm Kultoon wadda ta ci sunan mahaifiyarsu ake kiranta da Maama, sai mai bin ta Umm Salma, Umm Khairi, da kuma yar auta Umm Ruman, sai dai dukansu suna bin bayan babban ďanta Yassar ne da ya kasance namiji daya tilo a yayanta.

H U R I Y Y ADove le storie prendono vita. Scoprilo ora