Page 60- Komai Ya Yi Farko...

Börja om från början
                                    

Bayan ta fita ya dawo da hankalinsa gare ni. Sai da ya yi min kyakkyawar sumba, kafin ya kwantar da jaririn a kan katifarsa. Ya ce,
"Ga haihuwar Ummu, ban nemi zabinki ba. Haka Afreen ma duka ni na yi musu suna. A yanzu da muka samu wannan, na yarje miki, ki zabi duk sunan da kike so da shi zan yi masa huduba."

Kwarai na ji dadin zabin da ya ba ni. Na saki sassanyan murmushi ina duban sa. Na ce,
"Na zabar masa Abubakar Saddiq, sunan mahaifina. Ina masa fatan ya kasance da halayen takwaransa na ainahi, Sayyiduna Abubakar."
Ya kalli cikin idona, da murmushi ya ce,
"Madalla da wannan suna mai tarin girma da ma'ana. Allah Ya yi masa albarka, Ya albarkaci rayuwarsa shi da 'yan'uwansa."
Na amsa da amin.

Tun daga nan sai kowa ya shaida sunansa Abubakar amma za mu dinga kisan sa da Sadiq. Da na fada wa Umma sunan da aka samu, har sai da na ji sautin kuka a cikin muryarta. Ta ji dadi da na yi wa mijinta takwara. Amma duk da haka sai ta ce,
"Me ya sa ba ki yi karar sanya Ahmad, sunan mahaifinsa ba?"
Na yi murmushi.
"Ah kun ga Hajiya Umma, ana so ana kaiwa market. Ai shi ya ba ni zabi, ni kuma na ga tunda ga Afreen sunan Mami, wannan karan sai a juya."
Ta ce,
"Shi kenan, kun kyauta sosai. Allah Ya yi muku albarka, Ya raya muku zuri'a."
Ban ce amin ba sai dai na fada a cikin zuciya, saboda kawaici irin na yarinyar Hausawa.

Wannan karan ba a yi taron suna ba, na makale da hujjar CS da aka yi min. Muka ci gaba da kula da Sadiq dinmu, a gefe guda kuma ina zuwa aikina hankali kwance.

Abubakar na da shekara daya da rabi approval dina na zuwa karin karatu ya fito. Ko da na fada wa Haidar ba karamin farinciki ya yi ba. Ya ce sai in yaye Sadiq din tunda da ma ya isa yayen. Bayan kwana biyu, ranar Juma'a na yaye shi.

Ina ta shirye-shiryen tafiya Columbia, can South America, sai ga Haidar ya shigo daki. Ya rungume ni hade da kissing goshina ya ce,
"Albishirinki."
Na dago kaina da annuri na ce,
"Goro, fari kal."
Ya ce,
"Na dauki hutun karshen shekara, tare za mu yi tafiyar nan. Daga can in karasa hutuna na good three months tare da matata. Idan na gama duka sannan zan dawo."

Na kuwa rungume shi ina jin wani irin farinciki yana lullube ni. Da ma tunanin yadda zan tafi in bar mijina har shekara biyu nake yi. Amma idan muka tafi tare, at least zan rage wani haushin.
Ya rungume ni hade da cewa,
"Idan ma na dawo din, zan samu lokaci mu kawo miki ziyara ni da yarana. Sannan ke ma ko nan da shekara ne kya dawo gida ai."

Na daga masa kai.
"Thank you so much my Darling husband. Madalla da samun miji nagari irin Aliyu Haidar. Daya tamkar dubu. Mijin Ummu Baban Ummu."
A bayyane na ci gaba da nuna masa farincikin da kalamansa suka sanya ni.

Daga nan sai muka ci gaba da shirin tafiya tare. A bangare guda kuma zuciyata cike take da zulumin kewar yarana da zan yi, musamman Sadiq da yake karami kuma sabon dan yaye.

Mun yi bankwana da iyaye da dangi, daga nan jirginmu ya lula sai Columbia. Tare muka dinga zuwa makarantar  da Haidar har sai da na gama duk wasu cike-cike, ya rage saura sati biyu mu fara shiga aji. A cikin sati biyun nan ko rana babu wanda ya gani a cikinmu. Kullum muna cikin daki muna kashe junanmu da soyayya. Soyayyar da ko farkon aurenmu ba ta kai ta ba. Duk wani motsi nawa a jikin Haidar ne. Tamkar cingam haka na kasance masa. A tsayin zaman nan mun mori junanmu da kyau. Hatta wayoyinmu a kashe suke, sai bayan kwana biyu ko uku mu kunna mu dan yi waya da gida da kuma yaranmu sannan mu mayar da su a kashe.

Ko da na fara zuwa lecture ma kullum na dawo tare muke. Ga weekend kuma haka za mu karaci yawonmu makale da juna, kuma babu wanda ya damu da hakan ko kadan.
Muna video call da su Ummu a Tab dinsu akai-akai.
A haka har hutun Haidar ya kare. Na sha kuka sosai a lokacin da zai tafi. Saboda wata irin rayuwa ce muka yi a Columbia mai cike da tsaftatacciyar kauna. Sai da ya yi ta yi min kalamai masu dadi sannan na dan hakura. Amma a daren ba mu runtsa ba har gari ya waye. Tare muka je Airport, ban kuma tafi ba har sai da jirginsu ya tashi.

DARE DUBUDär berättelser lever. Upptäck nu