Page 56- Confess 2

Start from the beginning
                                    

Daga haka ta sallame mu ta tafi. Mu kuma muka zauna shawarar ta inda za mu fara. Shi ne a karshe muka tsaya a kan za mu kwashi romo daga jikinta, kafin mu yanka ta da wukar da ke jikin Saminu. Wannan shi ne gaskiyar abin da ya faru."

Ya karasa maganar cike da rauni. Ai kuwa kotu ta kaure da hayaniya. Alhaji Abdulkadir shiru ya yi da alama ya zama speechless. Na mayar da duba na ga Anti Khadija, kuka take wiwi.
Can na tsinto muryar Malama Zainab, cikin hargowa tana fadin,
"Wallahi karya suke yi min...ku jiye mini masharrantan yara. Ni ina ma na taba ganin ku? Wallahi ban san su ba yallabai..."

"Order!"
Alkali ya fada cikin tsawa. Dole ta shiga taitayinta, ta hau mazurai.
Saminu da hawaye suka gama wankewa, ya daga hannunsa. Alkali ya ba shi izinin magana.
"Yallabai, duk abin da Ibro ya fada haka ne. Wallahi da gaskiyarsa. Wannan matar muguwa ce. Ta jima tana sanya mu aikata mummunan abu. Dan ko matar nan da aka kawo dazu, aka ce wai mahaifiyata ce, wallahi ban taba ganin ta ba sai yau. Ni dai lauyanmu ya same mu, ya shaida mana za a kawo wata mata da za ta zama mahaifiyata, wai daga wata asibiti suka je suka samo ta a kan cewa za a biya mata kudin magunguna idan har ta bayar da shaidar ita ce mahaifiyata. Amma Allah na sama Yana gani ban san ta ba."

Sama'ila ya karbe da fadin,
"Da gaske ta jima tana sanya mu aiki. Daga cikin ayyukan da muka yi mata har da kisan 'yar'uwar waccan."
Ya nuna ni da hannu.
"Ni dai ban san mene ne ya hada su ba da farko. Amma dai ta sanya mu mun ci gaba da bibiyar su, daga makaranta zuwa gida. Amma a lokacin sai muka kyale su saboda hanyar cike take da mutane dole idan muka taba su za a iya ganewa.
Daga baya kuma sai muka samu labarin an sace su, masu garkuwa da mutane. Hajiya ta yi ta dariya tana cewa Allah Ya kara. Amma duk da haka ta ce ba za mu kyale su ba, yadda suka ja ta hakura da aikinta duk son da take yi masa, ba za ta taba kyale su ba. Sai ta ce mu kashe musu iyaye, ko mu nakasa su. Ita da kanta ta samo mana bindiga, ta damka mana tare da cewa mu lura sosai, mu yi aiki yadda ya kamata.
A lokacin da muka fara bibiyar Baban nasu, sai kawai muka gan shi yana ta nufan wani daji bayan mun sauka daga motar garin Sassanya da muka hau. Daga nan muka fara tsorata, sai muka jira a bakin wani icce. Can kuma sai ga shi ya taho tare da daya daga cikinsu, shi ne mu kuma muka saita mata bindiga, a take ta fadi wurin, hakan ya ba mu tabbacin ta mutu. Sai muka samu muka gudu ba tare da barin shaidar komai ba.
Samun nasarar kashe ta ya sanya ta ce ita gudar, wato waccan lauyar, mu bar ta kawai, radadin mutuwar 'yar'uwarta ba zai taba barin ta jin dadin duniya ba."

Duk da gudumar da alkali ke bugawa yana fadin
"Order!"
Hakan bai sanya aka yi shiru ba, har sai da aka dauki dogon lokaci kafin aka nutsu.
Na dago kai na dube ta, kai kawai na gyada ina sharce hawayena.
Wannan fa shi ne ana zaton wuta a makera...na yi shiru da tunanin, jin alkali ya fara magana.

"A bisa zantukan da duk muka saurara, masu laifi sun amsa laifinsu. Sannan sun tona wa wacce da sanya su, suke yi mata aiki, asiri. Kotu ta yanke wa Ahmadu, Saminu, Ibrahim (Ibro) da kuma Sama'il, daurin rai da rai a gidan yari, tare da horo mai tsanani. Kotu ta sassauta musu ne bisa ga la'akari da tona wa kansu asiri da suka yi."
Ya yi gajeren rubutu, ya dago fuskarsa ya ce,
"Sannan Mrs Zainab Abdulkadir, kotu ta yanke mata hukuncin kisa ta hanyar rataya, tare da tarar naira miliyan biyu ga Hannatu da aka keta wa haddi."
Ya buga guduma hade da fadin,
"Kooootu!"
Ya mike ya fice.

In ban da gunjin kukansu babu abin da yake tashi. Ni kuwa fuskata fal da annuri. Farinciki biyu a lokaci guda; ga na samun nasarar shari'armu, ga kuma ta tonuwar asirin makasan 'yar'uwata, aminiyata, wacce kullum nake kwana na tashi da takaicin rashin gane wadanda suka kashetan.
A lokaci guda muka kalli juna ni da Barrista Rafiq, ya sakar min murmushi ya ce,
"Congratulations Barrista Khairi. Sai mun hadu next time?"
Na daga masa kai.
"In shaa Allahu an dasa yin nasara kenan a kanka Barrista. Da kai da ire-irenka ma."
Sannan na dubi Fa'iz da ke fadin
"Congratulation Barrister Khairi."
Ni ma na maimaita masa,
"Congratulations Barrista Fa'iz."
Sannan duk muka mike.

Ji na yi an rungume ni, ina dubawa na ga Hannatu ce. Kuka mai hade da dariya take yi. Na hau bubbuga bayanta a hankali ina fadin,
"Barka da arziki Hannatu. A yau Allah Ya nufa an karban miki hakkinki. Duk da babu abin da zai iya maye gurbin babban abin da kika yi rashi, amma at least za ki rage kaso mai yawa na daga cikin kuncinki."
Ta dago daga jikina ta ce,
"Dukkanin kokarin naki ne Aunty Khairi. Ba zan taba mantawa da ke da tarin alkhairinki ba a gare ni. Hakika sunanki ya cancanta a gare ki sosai, uwar alkhairi, domin kuwa na ga alkhairin naki."

Kama ta na yi muka fita, saboda duk idanuwanmu mutane a kanmu suke. Muna tsayuwa sai ji na yi an taba ni. Anti Khadija ce. Kafin fadan komai sai gani na yi ta zube a kasa, guiwoyinta bisa kasa, ba ta damu da dattin da za ta iya kwasa ba. Ta kama bakin gyalena. Cikin kuka ta ce,
"Ban san da wane baki zan iya gode miki ba Khairi. Hakika kin saka sharri da alheri, kin nuna min kin fi ni. Yau ga ranar da Allah Ya nuna min iyakata, ke din da na dinga aibuntawa a baya, kin yi min abin da ba ni da bakin gode miki. Allah'n da Ya halicce ni, Ya san sirrin da ke cikin kalbi, Shi kadai ne zai iya biyan ki. Abu daya da zan iya cewa a yanzu shi ne, ki yafe min komai, idan na ce komai, ina nufin komai da komai. Ki manta da baya, ki kalle ni a matsayin 'yar'uwarki mai kaunarki har cikin zuciya. Wallahi na ga ishara...na ga ishara Khairi."

Kuka take yi sosai, wani irin tausayinta ne ya shige ni, na kama hannunta na mikar tsaye, sai kawai na ji kwallan ni ma sun zo min, muka rungume juna muna sakin kuka a tare.

Amrah A Mashi❤️

DARE DUBUWhere stories live. Discover now