Page 55- Confess 1

Zacznij od początku
                                    

Alkali ya dago kai daga rubutun da yake yi, ya ce,
"Ko lauyoyi masu kara suna da tambayar da za su yi wa Mrs. Zainab Abdulkadir?"

Na kuwa mike, a hankali na tako zuwa gabanta. Na ce,
"Hajiya Zainab, kin ce tamkar 'yarki ta ciki haka kika dauki Hannatu. Amma me ya sa tun da ake zaman kotun ba ki taba zuwa ba sai yau da kika zo kare wadanda ake zargi da haike mata?"
"Objection my Lord! Barrista UmmulKhairi na kokarin titsiye shaidata, bayan kuma ta riga ta fada a baya cewa ba za ta bari a zalunci yaran nan ba ne shi ya sa ta zo kotun."
Alkali ya ce,
"Objection overruled. Barrista UmmulKhairi ci gaba."

Sum sum sum Barrista Rafiq ya koma ya zauna. Ni kuma na ce
"Thank you my Lord."
Sannan na juya ga Malama Zainab na ce
"Uhm hmm...ya aka yi haka ta faru?"
Kai tsaye ta ce,
"Ni ban damu da zaman kotu ba shi ya sa...ban ma dai taba zuwa ba gaskiya."
"To me ya sa kuma yau kika damu da shi?"
"Saboda in wanke wadanda ake zargi don ba su ba ne."
Na yi gajeren murmushi.
"Yanzu idan har 'yar taki ta cikinki ce ma haka za ki zo ki kare wadanda ake zargi?"
"Ko ni na haife ta zan zo, matukar dai ba su din ba ne ba."
"Me ya sa duk a sauran zaman kotun ba ki zo kin wanke su ba sai yau?"
"Saboda ban san su ake zargi ba."
Kai tsaye ta fadi hakan ba tare da tunanin me amsar tata za ta haifar ba.
"Idan har na fahimce ki Hajiya Zainab, ba ki san cewa su Ahmadu ne ake zargi da haike wa 'yarki ba ko?"
Ta daga kai.
"Duk da 'yarki ce kenan ba ki taba neman sanin wadanda suka haike mata ba ballantana har ki tsayu tsayin-daka wurin ganin an bi mata hakkinta?"
"E, to. Ni so na yi a bar wa Allah. Da tun farko ba a bata lokacin zuwa kotun ba, ai komai tsawon dare gari zai waye. Asirinsu zai tonu."
Na gyada kai,
"Haka ne. Mu koma kan batun su Ahmadu da kika yi tafiya da su. Shin maigidanki ya san tare kuka tafi?"
"E, ya sani."
Ta fada a hankali ba kamar sauran amsoshin da take bayarwa kanta tsaye ba.

Jin hakan ya sanya na juya ga alkali na ce,
"My Lord, zan so kotu ta ba ni dama domin yi wa Alhaji Abdulkadir wasu 'yan tambayoyi."
Alkali ya ce
"Kotu ta ba ki dama."

Cikin sanyin jiki ya fito, sai da ya yi rantsuwa a kan zai fadi gaskiya, kafin na dube shi na ce,
"Alhaji, kai ne mahaifin Hannatu, raped victim dinmu. Sannan kai ne mijin Hajiya Zainab da ta zo domin kare wadanda ake tuhuma da haike wa diyarka. Kuma har'ilayau kai ne ubangidan wadanda ake zargin. Na san kana bibiye da komai tun farko har zuwa yanzu. Matarka Hajiya Zainab ta zo tana bayar da shaidar cewa ba su gari a ranar da abun nan ya faru, sannan ta ba da tabbacin ka sani, ka san cewa tare ta tafi da su, ta sauke wani a kauyensu, sannan ta wuce da wani Kano. Me ya sa duk ka san haka amma ka yi shiru, ka bar kotu da tuhumar wadanda ba sa ma gari a sadda abun ya faru?"

Gyada kansa ya yi, fuska babu annuri ya ce,
"Wallahi ni ban sani ba. Abu daya dai da na sani shi ne ta je Kano ranar, don sadda muka je asibitin da aka kai Hannatun, na kira in shaida mata abin da yake faruwa ta ce ba ta dawo ba. Kuma tana dawowar abu na farko da ta fara yi shi ne zuwa asibitin.
Amma ba ta fada min tare da su Ahmadu za ta tafi ba, kamar yadda ita kadai ta zo asibitin, kuma direct daga Kano din take ballantana in yi tunanin ko ta biya ta sauke su ne."

Sosai na ji dadin amsarsa. Na juya ga alkali na ce,
"Na gama yi masa tambayar ya mai shari'a."
Aka ba shi izinin komawa ya zauna.
Na juya gare ta na ce,
"Hajiya, kin dai ji da kunnuwanki mijinki ya karyata batun wai ya san tare kuka tafi."
Ta yi shiru tana rarraba ido tamkar bera a cikin buta.

Na sake duban alkali na ce,
"My Lord, wannan shi yake tabbatar wa kotu da cewa batun da Hajiya Zainab ta yi na cewar yaran nan ba sa nan ranar da abun nan ya faru, labari ne kawai na kanzon kurege. Sun tsara abunsu ne a tunaninsu hakan zai haifar da d'a mai ido. Na gode ya mai shari'a."

Daga haka na koma na zauna. Ita kuma aka ba ta izinin tafiya.

Shiru kotun ta yi, kowa na sauraren abin da alkali zai fada. Can sai ga sautin kuka yana tashi. Kowa ya daga kansa domin neman ta inda sautin yake tashi. Ibro ne, daya daga cikin wadanda ake zargi. Cikin kukan nashi ya daga hannu, alkali ya dube shi, hade da zare gilashin idonsa, ya ce,
"Yaya aka yi? Kotu ta ba ka damar magana."

Cikin kukan ya ce,
"Ya mai shari'a, na gaji. Allah ma Ya sani ina son kawo karshen wannan shari'ar ni dai a yau din nan. Da gaske mu muka haike wa Hannatu. Amma wallahi sanya mu aka yi mu kashe ta, shi ne mu kuma muka ce sai mun samu biyan bukatarmu kafin aika ta lahira."
Cike da al'ajabi nake bin sa da kallo, kamar yadda na lura da kowa mamakin kalaman nashi yake yi, har alkali.
"Uhm hmm...go on. Wa ya saka ku kashe ta?"
Kai tsaye ya amsa da
"Matar mahaifinta, wannan wacce ta tafi yanzun nan bayan ta gama bayar da shaidar karya. Mun jima muna yi mata aiki kuma muna samun nasara."
"Me ya sa ka zabi ka tona asiri a yanzu?"
Alkalin ya tambaye shi cike da al'ajabi.
Ya ce
"Saboda na ga alaman za ta shigar da mu ne, ita ta kubuta ba tare da an zarge ta ba, mu kuma a daure mu bisa ga zunubin aikata fyade. Ta gama lalata mana rayuwa, ita ta tsira."

Alkali ya dan shafi fuskarsa, kafin ya yi gajeren rubutu, ya ce,
"Za a tafi hutun awa daya da rabi. Kafin nan kotu ta bayar da izinin a je a kamo Hajiya Zainab Abdulkadir kafin nan da lokacin dawowar."
Ya buga guduma hade da mikewa.



Amrah A Mashi❤️

DARE DUBUOpowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz