Page 51- Babbar Kotu

Start bij het begin
                                    

Yanayin amsarsa da kuma yadda matar ta so yin magana ya dakatar da ita ne ya ba mu tabbacin akwai abin da suke boyewa. Na yi ta-maza na ce,
"Sunana UmmulKhairi, wannan kuma Hannatu. Tare muka zo da bak'i amma maza ne suna waje. Idan za ku ba mu dama in je in shigo da su. Wata magana ce mai muhimmanci ke tafe da mu."

"Ke ni fa wallahi tsoron zamanin nan nake. Mutane ba gaskiya sam-sam, Allah a baki Fir'auna a zuci."
Na saki gajeren murmushi hade da zaro ID card dina duk da na san ba ganewa za su yi ba.

"Kamar yadda na fada muku, sunana UmmulKhairi. Ni Barrister ce mai aiki a hukumar kare hakkin dan'Adam ta bangaren fyade."
"To sai kuma aka yi yaya? Mene ne alakarmu da ku?
Duk da taso min da fadan da ya yi bai sanya na saduda ba, na ce,
"Ka taimaka ka ba mu damar shigowa da abokanan tafiyar mu. Za su fayyace maka komai."

Bayyanannen tsaki ya yi hade da nuna mana hanya.
"Kun san Allah, idan ba ku bar gidan nan ba yanzun nan zan tara muku mutane in ce kun zo har gida kuna son titsiye mu. Yo wai ina dalili! Ana dole ne?"

Har ya yi ya gama matar ba ta ce uffan ba, sai dai da alama fuskarta akwai rahama, don sai ta bude bakinta za ta yi magana amma ya yi kokarin dakatar da ita.
Ganin da gaske mutanen yake son tara mana ya sanya na kama hannun Hannatu na mikar da ita. Na dubi matar na ce,
"Baiwar Allah, ke ma mace ce 'yar'uwarmu. Idan har kin taba haihuwa na san dole kin san zafinta. Idan ma ba ki taba ba to wani naki ya haihu ba za ki rasa jin labarin yadda zafin haihuwar yake ba.
Ki auna a ce kaddara ce ta afka a kan diyar da kika haifa, wasu kartin banza suka keta haddinta. Shin yaya za ki ji? A wane irin yanayi za ki tsinci kanki?"

Shiru ta yi amma da alama maganganuna sun shige ta. Ganin haka ya sanya na dora da fadin,
"Wannan yarinyar, duka-duka shekarunta goma sha takwas. A kan idanuwanku maza har uku suka keta martabarta, suka shige ta ta karfi da yaji. Me ya sa kuke nuna kamar ba ku san ta ba alhali kuma kun san ta din? Shin ba za ku auna a ce a kan naku abun ya faru ba? Yaya za ku ji idan wadanda abun ya faru a gabansu suka nuna ba su sani ba, kuma su ne kadai kuke da fata a kansu?"

Bakidaya jikin matar ya gama yin sanyi, ta dubi mijinta da ya yi shiru ta yi masa fullanci, can kuma sai ta juyo gare ni ta ce,
"Ki rantse ba cutar da mu kuka zo yi ba."

Dariya na ji ta zo min amma na yi saurin matse ta.
"Ko kadan. Wallahi mu ba azzalumai ba ne, ba za mu taba cutar da mutum ba."
Ta sauke bayyananniyar ajiyar zuciya. Mijin ya ce,
"Kika ce tare kuke da wasu?"
Na daga masa kai.
"To je ki shigo da su. Kuma idan kuka cuce mu Allah na gani ba za mu yafe muku ba."
"Na yarda."
Na ba shi amsa hade da fita waje na bar Hannatu bayan na zaunar da ita.

Ina isa wurinsu duk suka yi saurin zuwa kaina.
"Kai yau Allah Ya hada ni da wasu irin mutane. Ba su fa yarda da mu ba wallahi."
"Ai da ma na san za a sha wuya. Su din ne dai ko?"
"Alamu sun nuna su ne. Na samu dai na shawo kan matar da kyar, mijin ya fi taurin kai. Ya ce in shigo da ku."
Na yi gaba suka bi bayana zuwa cikin gidan.

Su Haidar suka gabatar da kansu, kafin matar nan ta ce,
"Gaskiya ina kallon ta na shaide ta. Yarinyar nan a kan idanuwanmu wasu maza suka keta alfarmarta. Ta ba ni tausayi fa."
Mijinta ya amshe da
"Yanzu me kuke nema a wurinmu?"

Barrista Fa'iz ne ya yi caraf ya ce,
"An shigar da zancen nata a kotu, an yi zaman farko saura na biyu, kuma da ku muka dogara, saboda ta ba mu labarin taimakonta da kuka yi. Muna so ranar shiga kotu ku je ki bayar da shaida."

Tamkar idanuwansu za su fado kasa haka suke bin mu da kallon tsoro hade da mamaki.
"Kai anya kuwa ka san abin da kake fada? Mu? Mu ne za mu je kotu mu bayar da shaida? Aradun Allah ba zan iya ba tsoro nake ji."

Cikin sanyin murya na dubi mijin da ke maganar, na ce,
"Babu abin da za a yi muku Babana. Idan kuka bayar da shaidar nan aka yanke wa azzaluman hukunci lada za ku samu fa, kun ga an rage azzalumai a doron kasa. Amma yin shirunku alhali kun san gaskiya tamkar zalunci ne. Kawai abin da kuka sani ne za ku fada, ba dad'i ba ragi."

Da gani ya dan fara saukowa, Fa'iz ya dora da,
"Ku dubi girman Allah ku yi taimakon musulunci. Yarinyar nan ta sha wuya sosai, da kyar ta rayu."
"Mu za mu ba ka wannan labarin ai tunda mu muka kai ta asibitin cikin halin rai ko mutuwa."
Ya katse Fa'iz din.
"To tun da haka ne, ka ga bai kamata ba ku yi shiru ko? Ku taimaka mana."

Sai da ya ja matarsa suka shiga daki fiye da minti biyar sai ga su sun dawo. Ya dube mu ya ce,
"Yaushe ne shiga kotun kuka ce?"
"Saura kwana biyar yau. Ranar Alhamis ne in shaa Allahu."
Na yi gaggawar ba shi amsa.
Ya ce
"Kun ga an ci sa'a ma ranar muna Katsina. Sai ku fada mana wurin da za a yi. Da izinin Allah za mu zo."

Wani irin dadi ne ya k'ume ni, kafin in ce komai Haidar ya ce
"Ku fada min inda zan same ku, ni da kaina zan je in dauke ku ranar."
"Kenan ba ka yarda ba da na ce za mu je?"
"Na yarda mana. Wai don in saukaka muku ne."
Ya ba shi amsa yana murmushi.
"To ba sai ka zo daukarmu ba. Mu da kanmu za mu same ku ko karfe shidan safiya ake so. Kawai ku fada mana inda za mu je."

Wahalar sha'anin mutumin ya sanya na yi gudun kar ma ya ce ya fasa. Don haka na yi saurin cewa,
"Babbar kotu za ku ce. Duk mai abun hawan da kuka fada wa haka zai gane."
"Babbar kotu ko?"
Ya maimaita. Sannan ya dubi matar tashi ya ce
"Ki taya ni rikewa. Babbar kotu."
Ita ma ta maimaita
"Babbar kotu."
Ni abun ma dariya ya ba ni, kamar sun samu wani karatu.

Bankwana muka yi musu sannan muka tafi, har mota mijin ya raka mu yana maimaita babbar kotu a bakinsa.




Amrah A Mashi❤️

DARE DUBUWaar verhalen tot leven komen. Ontdek het nu