Haidar ya goyi bayan wannan idea, don haka sai muka yi parking a gaban wani gida. Ni da Hannatu ne a karshe su biyu kuma gabanmu.

Wasu yara Haidar ya tambaya gidan mai gari. A tsorace suke, don haka sai ya saki murmushi, ya ce,
"Kun ga ba ku san mu ba ko? Baki ne daga birni muke. Akwai wasu bayin Allah ne da muka zo mu saka musu da alkhairi kwatankwacin yadda suka saka mana mu ma."
Barrista Fa'iz ya dora da
"Watakila ma kun san su. Wasu mata da miji ne, za ku gan su tare suke tafiya ko'ina, har cikin Katsina suke zuwa su biyun."

Gudan yaron har da saurinsa ya ce,
"Wasu wanda matar ba ta da tsayi amma shi namijin dogo ne ko?
Na yi saurin daga musu kai duk da ban san hakan ne ko ba haka ba.
Yaron ya ce,
"Kai Habu ba ka gane su ba? Kawu Sada ne fa shi da Inna Safare. Ka tuna har Baba na yi musu fada a kan yawan tafiyar kafa da suke yi har zuwa Katsina? Ai yanzu ma haka ba su nan suna can Katsinar."
"Ka tabbata?"
Yaron ya jinjina kai.
"Ai duk kauyen nan babu mai tafiya tare da matarsa idan ba Kawu Sada ba. An ce wai aiki suke zuwa a wani gida, shi ya sa sai karshen mako suke zuwa nan."

Na fada kogin tunani. Can kuma na ce,
"A wace rana ce suke tafiya, kuma yaushe suke dawowa?"
Na fadi hakan ne ina tuna ranar da kaddarar can ta afka wa Hannatu.
"Akwai dai ranar da na ga za su tafi, kamar ranar Litinin ne da safe."
Dayan ya yi caraf ya ce,
"E Litinin ne ka ma tuna min. Ba har Ummaru ya ce zai dinga bin su ya je makaranta ba?"
"Haka ne."
Ya ba shi amsa.
"Kamar dai ranar Jumu'a ne suke dawowa nan."

Kawai sai na ji hankalina ya kwanta da bayanin yaran. Ta yiwu su din ne, ta yiwu kuma ba su ba ne. Na dubi Haidar da Fa'iz na ce,
"Ina ji a jikina fa mun dace."
Ashe su ma tunanin da suke yi kenan. Fa'iz ya ce,
"Za mu tabbatar da hakan ne idan muka dawo ranar Asabar."
Ya dubi dayan yaron ya ce,
"Yaya sunanka?"
"Garbati."
Ya ba shi amsa.
"Ina ne gidanku?"
Da hannu ya gwada mana gidan nasu, babu nisa daga nan.
Haidar ya dube shi, ya ce,
"Ka san yadda za a yi? Ranar Asabar idan Allah Ya kai mu, za mu dawo, da yamma kamar haka dai bayan la'asar. Sai ka jira mu a daidai nan, daga nan ka raka mu gidan nasu."
Yaro ya jinjina kai.
"To sai kun zo."
Haidar ya zaro dari biyu ya ba su ya ce su raba. A take fuskarsu ta fadada da annuri, mu kuma muka koma cikin mota tare da fatan wannan hikimar da muka yi mu dace.

Hakan da ya faru sai ni ma na samu wata idea din. Na dubi Hannatu na ce,
"Kin ce za ki gane mai keke napep din nan da ya dauke ki ko?"
Ta daga kai.
"Har keken nashi ma zan iya ganewa. Hatta lambar keken ma..."
Ta dan yi gajeren tunani, kafin ta ce,
"Tabbas na rike ta."
Na saki hamdala a bayyane, domin hakan ba karamin taimaka wa bincikenmu zai yi ba.
Na zaro takarda da biro daga cikin jakata na mika mata na ce,
"Rubuta lambar a nan."
Sannan na daga kaina na ce wa Haidar da Fa'iz,
"Kun san me za mu yi daga wannan step din?"
Dukkansu suka gyada kai. Na ce,
"Kamar yadda masu motocin haya suke da kungiya haka su ma masu keken suke da ita. Tunda ta rike lambar, da ita za mu yi amfani mu je wurin masu keken, mu nemi shugabansu sai ya nemo mana shi, idan har ya yi rijista da kungiyarsu gano shi ba zai mana wahala ba. Sai dai fatan dacewa."

Duk suka hada baki wajen fadin,
"Good idea."
Haidar har da tafa min yake.

Bayan mun iso cikin gari, kai tsaye ofishin masu keke napep muka nema, duk da maghriba ta fara gabatowa amma muka yanke zuwa a yanzun domin kammala komai a kan lokaci. Domin Hausawa sun ce da sanyin safiya ake kamun fara.

Da muka isa wurin, Chairman muka nema wanda shi ne Ogansu duka. Haidar ya mika masa takardar bayan dogon bayanin da Barrista Fa'iz ya yi masa.
Ya duba lambar sosai, kafin ya dago kai ya ce,
"Ban dai gane lambar ba gaskiya, amma zan duba cikin gwanen lambobin da ke jikin littafinmu. Sai dai wani hanzari ba gudu ba, gaskiya mun tashi aikin yau, gobe da safe ku dawo."

Barrista Fa'iz ya zaro kudi daga cikin aljihunsa wanda za su iya kai dubu biyar, ya mika su ga mutumin hade da fadin,
"Sauri muke yi ne ta yadda ba za mu iya jira har sai gobe sannan ka duba mana ba. Ka dai taimaka mana don Allah."

Da fara'arsa ya karbe kudi ya ce mu biyo shi zuwa ofishinsa.
Wani tsohon office ne, kujerun cikin duk sun mutu, ga wani teburi da ke jibge da tulin takardu duk kura.
Zama ya yi a kan kujerar ya hau bincikar wani long book, yana yi yana kara duba takardar da na ba shi.
Ya dan jima yana dubawa sannan ya dago ya ce,
"Kun taki babbar sa'a kuwa, Habibu ne. Yaro mai hankali na tabbata zai yi muku abin da kuke so."

Dukkanmu muka hau godiya ga Allah, na ce,
"Lambar wayarsa fa? Ko za mu iya samun sa a yau?"
"Ga lambarsa nan a gaban lambar keken tashi ai."
Fa'iz ya matsa ya kwafi lambar a wayarsa.
"Idan kun taki sa'a kuna iya samun ganin shi a yau din ma. Idan kuma wayarsa ba ta shiga ba ku yi hakurin gobe."

Godiya muka yi masa tare da tafiya zukatanmu fayau. A raina addu'a nake Allah Ya sa mu same shi.

Fa'iz ya latsa kiran sa sai dai a kashe ya ji wayar. Haidar ya ce,
"Maghiba ta riga ta yi, ni ina ganin a hakura kawai har zuwa gobe sai a neme shi. In shaa Allahu za a dace."

Daga haka muka tsaya. Har gida Haidar ya kai Fa'iz sannan muka biya muka sauke Hannatu ma, a lokacin isha'i ake neman kira. Ko da muka isa gida wanka da sallah kawai na yi, ko abinci ban iya ci ba sai bacci, saboda gajiyar da na yi.



Amrah A Mashi❤️

DARE DUBUWhere stories live. Discover now